Yaki da cin hanci:Akwai jan aiki a gaban Buhari – Abubakar Alhaji

Aminiya ta samu damar tattaunawa da Sardaunan Sakkwato, tsohon ministan kudi kuma  tsohon jakadan Nijeriya a Ingila, Alhaji Abubakar Alhaji, kan al’amuran da suka shafi kasar nan da jihar Sakkwato. Ga yadda hirar ta kasance: Aminiya: A matsayinka na tsohon ministan Kudi kuma Jakadan Nijeriya a Ingila, yaya za ka kwatanta aikin gwamnati can baya […]

Yaki da cin hanci:Akwai jan aiki a gaban Buhari – Abubakar Alhaji

Aminiya ta samu damar tattaunawa da Sardaunan Sakkwato, tsohon ministan kudi kuma  tsohon jakadan Nijeriya a Ingila, Alhaji Abubakar Alhaji, kan al’amuran da suka shafi kasar nan da jihar Sakkwato. Ga yadda hirar ta kasance:

Aminiya: A matsayinka na tsohon ministan Kudi kuma Jakadan Nijeriya a Ingila, yaya za ka kwatanta aikin gwamnati can baya da yanzu?

Alhaji Alhaji: Babu kwatanci, yanzu abubuwa sun lalace, kafin haka idan ka ki yin aiki ko ka aikata rashin gaskiya za a hukuntaka, amma yanzu ka sani bata-gari sun yawaita a cikinmu. A lokacin ina jakadan Nijeriya a Ingila akwai shugaban kasar da ke ba da labara, wani ya gaya masa cewa da ka zama shugaban kasa gara ka zama minista a Nijeriya, saboda kudaden da suke kashewa. Ka gani a Ingila na san an yi Firaminstan da ke hawa keke ya tafi ofis, a garin nan Sakkwato ko kashi gwamna zai yi sai an yi masa jiniya, wane rashin hankali ne wanan? Sarauniyar Ingila ba a yi mata jiniya, amma a nan Najeriya ko jami’in shige da fice ana yi masa, don ana yi wa ido ne. Ai shugaba Buhari ba karamin aiki ne a gabansa ba. Waton AllahYya kawo mana canji wanda sai godiya, domin Buhari ba zai yarda da kowace almundahana ko rashin gaskiya irin wanda Obasanjo da na tare da shi suka aikata ba. Lalle an samu canji, musamman ta fuskar taka wa barayin gwamnati burki,na goyi bayan kokarin da yake yi na yaki da cin hanci da rashawa. Shirye-shiryen da Buhari ya dauko suna da kyau ba abin da zan ce sai dai in kara masa kwarin guiwa kan lamarinsa, Allah Ya taimake mu Ya ba da ikon cika nufinmu.
Aminiya: Kai jigo ne a jihar Sakkwato kuma tsohon mai ba da shawara kan tattalin arziki a jihohin Sakkwato da Kebbi da Zamfara, me ke faruwa yanzu an daina ganinka cikin harkokin gwamnati?
Alhaji Alhaji: Akwai dalili, mutanen nan ba su karbar shawara ko ka ba su, to ina zan je, babu inda zan je, ina zaune gidana, daga nan nakan je filin jirgi idan dare ya yi in dawo gida, don ban son cudanya da su, saboda ba su son gaskiya, kuma gaskiya ba ta neman ado. Yanzu za ka ga alkali wanda bai kamata yana cikin mutane ba, shi ne yake yawo da sarakuna, yana gina gidaje, haba! A ingila da na yi karatu alkali ba ya iya saye ko mallakar abin da ya fi karfin samunsa, don kada a tayar masu da kayar baya.
Aminiya: Gwamnatin jihar Sakkwato za ta ba da muhimmanci kan fannin ilmi fiye da sauran fannoni don samun ingantaccen ilmi, ya kake kallo lamarin?
Alhaji Alhaji: Wannan abin wasa ne, lalle wasa ce wannan, tun zamanin Alu Wamakko shekara takwas babu wani cigaba da makaratu suka samu, ko Bafarawa ya gudanar da aiki a fannin ilmi fiye da shi. Lokacin Bafarawa malamai ana yi masu kokari, sabanin yanzu, halin da ilmi ya shiga yana bata min rai, don a lokacin da muna kananan ba haka abin yake ba. Mahaifina yana shugaban makaranta, na sani shugaba yakan zauna cikin makarantar da yake karantarwa, haka mahaifina ya yi, yanzu fa haka ake yi, wane abun kunya ne wannan? Ina fatan Idan Buhari ya gama karbar bayanai kan abubuwan kasar nan, ya nada ministocinsa abubuwa za su dawo daidai. Abubuwan akwai matsala, don Jonathan ya kashe kasa, yadda ya cika mata a gwamnatinsa, a ce Diezani ce ministan mai, kai ka san babu gaskiya. Ina karanta jarida na ga an ce ta tsere da biliyoyin Naira. Lamarin kasar nan kamar zuciyarka ta fashe, hakan ya sanya mutane suka cire tsammanin gyaruwar kasar nan, don wadanda ke shugabanci ba aikin suke so ba, su dai kawai su samu kwangila a gwamnati shi ke nan. Ka duba a nan Sakkwato yadda wani tsohon gwamna ke watsi da kudi, ya kira mutane a gidansa ana rabon atamfa da shadda a lokacin azumi, kai ka san babu gaskiya, an sanya wa mutane talauci da mutuwar zuciya karfi da yaji. Fiye da rabin Sakkwato duk in da ka duba sai ka ga gidan da wannan tsohon gwamnan ya gina, idan akwai adalci mutane za su yarda da kai? A lokaacin da gidana na kofar Marke ya kone kamfanin Julius Berger da dan uwana Ali Dasuki ne suka gina min wannan gidan suka ce dole in bar can in dawo nan.
Allah Ya kawo Buhari, muna fata Allah Ya ya ba shi ikon mayar da kasar nan inda ta fito da cigabanta, Obasanjo da Jonathan su ne suka mayar da kasar nan baya, don a lokacinsu ne biyayya ta kau, ka dubi lokacin gwamnatin Babangida, wadansu cewa suke yi waye shugaba, Abubakar ko Babangida? amma aka tura ni jakada a kasar Ingila kuma na tafi, duk da na samu tsaikon tafiya saboda rashin lafiyar mahaifina, na yi aiki can shekara shida. Turawa sun shimfida gaskiya a kasar nan, wadansu ne suka mayar da ita cikin rashin gaskiya, wadda muke fatan Buhari zai tsamo kasar nan daga halin da take ciki.
Duk kokarin da Aminiya ta yi domin Sardauna ya yi magana kan diyarsa da shugaba Buhari ya nada a matsayin minista kuma ake cece-ku-ce a jihar Sakkwato ya ci tura. Domin ya ki yarda ya ce uffan a game da hakan.