Yaki da COVID-19 ya lakume biliyan daya a Gombe
Gwamnan Jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya ya ce kwao yanzu, gwamnatinsa ta kashe Naira biliyan daya wajen yaki da cutar coronavirus a jihar. Yayin kaddamar da wani dakin gwaji a Babban Asibitin Kwararru na Jihar da ke garin Gombe, gwamnan ya ce yanzu jihar ta kammala shirin yaki da cututtuka ciki har da ta coronavirus. […]
Gwamnan Jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya ya ce kwao yanzu, gwamnatinsa ta kashe Naira biliyan daya wajen yaki da cutar coronavirus a jihar.
Yayin kaddamar da wani dakin gwaji a Babban Asibitin Kwararru na Jihar da ke garin Gombe, gwamnan ya ce yanzu jihar ta kammala shirin yaki da cututtuka ciki har da ta coronavirus.
Ya ce bayan sabon dakin gwajin wanda aka kashe kimanin Naira miliyan 120 wajen gina shi, shirye-shirye sun yi nisa na gina wasu dakunan gwaje-gwajen da taimakon Hukumar Bunkasa Ilimin Manyan Makarantu ta Kasa da kuma Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Gabas.
Inuwa ya ce da zarar aikin dakunan ya kammala, harkar lafiya a jihar za ta kara inganta.
Ya kuma yi kira ga Hukumar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa ta Kasa (NCDC) da ta kara tallafa wa jihar, yana mai cewa mota guda daya kirar Hilux da kudi Naira miliyan 100 kawai suka samu daga hukumar.
Shugaban kwamitin yaki da COVID-19 a jihar, Farfesa Idris Mohammed cewa ya kaddamar da dakin gwajin wani babbar nasara ce a yaki da annobar a Jihar Gombe.