Yaki da fataucin mutane
A kwanan nan kusan kullum sai an ji an kama wadansu, ko wadansu sun rasa rayukansu wajen shiga Turai. Wannan wani abin takaicin karshen zamani ne, inda mutane ke rufe kofarsu ga ’yan uwansu, duk da yadda ake ruruta ’yanci da tausayin talakawa. Shugabannin manyan kasashen duniya kan rufe kofa ko gina katangar karfe don […]
A kwanan nan kusan kullum sai an ji an kama wadansu, ko wadansu sun rasa rayukansu wajen shiga Turai.
Wannan wani abin takaicin karshen zamani ne, inda mutane ke rufe kofarsu ga ’yan uwansu, duk da yadda ake ruruta ’yanci da tausayin talakawa.
Shugabannin manyan kasashen duniya kan rufe kofa ko gina katangar karfe don kada baki su shiga kasashensu. Duk da yadda ake kallon irin shugabannin da kima, amma abin kunya ne ganin yadda suke taimakon azzalumai masu kama- karya a kasashe masu tasowa har abin ya kai yadda muke gani a yau. Domin da sun tsawata da ba haka ba.
Wannan dabi’ar daya take da halin masu hannu-da-shunin da ke katange gidajensu da yin dogayen rufi, su aje bakaken karnuka da masu gadi. Sukan guji ’yan uwa na jini, kuma ba ruwansu da makwabta balle su samu baki ko a kai musu ziyara don raya zumunci. N aman Layya ma sai da su kadai su ci, su boye sauran a gidan kankara.
A ruhin Jari-Hujja sukan tafi tare da wadanda suke dadada musu ko biyayya ga wasu manufofinsu, don ci gaba da mulki ko tara dukiya tare da zuke tattalin arzikin kasa domin son rai. Ta wannan sigar likitoci da malamai da sauran kwararu kan kwarara zuwa kasashen ketare don taimakawa wajen bunkasa tattalin arzikin kasashen da zufarsu ta hanyar biyan harajoji.
A hanyar barin kasar haihuwa akan yi kundumbala, inda wadansu mutane kan sayar da gidaje da gonakin gado don su yi wannan hijira. Haka akan yi wa mata alkawarin irin daular da za su samu a waje, su gina gidaje, su hau latsatsun motoci, a kwanta kan sitiyari, wuyarta a tsallaka Turai.
Mutanen kan yi tafiyar kasa ko su shiga jirgin ruwa duk da hadarin kishirwa ma ba ma yunwa ba ta ishi mutum. Ga jirkicewar jiragen ruwa da barzanar ’yan fashi a teku, amma sai mutane, musamman matasa su gwammace su yi wannan kasadar da ci gaba da hakurin hallaka a kasashensu na haihuwa, domin ba aikin yi, ba kudin kara karatu ba tsaro.
Mafi yawan wadanda suke wannan kaurar sun hada da Larabawa da ’yan Afirka ko Gabas ta Tsakiya, musamman kasashen da yaki ya daidaita kamar Iraki da Siriya da Libiya da bakake ’yan Afirka masu mafarkin Aljannar duniya tun suna da kuruciya. A dayar nahiyar mutanen Meziko da Kudancin Amurka kan tsallake katangar Amurka da zuwa New York ko Kalifoniya.
Kai dan uwa dubi ’yan uwanmu a Saudiyya, za ka iya irin rayuwar da suke yi! Rayuwa ta rashin ’yanci da tsoro da jahilci. Gara ka dawo gida inda aka san mutuncinka, kuma za ka iya samun nasara da daukaka kamar kowa.
Akan samu fataken da ke karbar daloli da duk wata kadara don mutane su tsallakar da mutum. Wadansu kuma akan yi garkuwa da su daga nan sai a tsallaka da su su koma kamar fursunoni, inda za su zama bayi sai yadda aka yi da rayuwarsu. A haka a hana su duk wata mu’amala da ’yan uwansu, a toshe duk wata kafa da za ta ba su damar mu’amala da duniya sai yadda aka dora su!
Tun bayan haramta cinikin bayi, ba a taba samun lokacin da ake fataucin mutane ba kamar wannan karni musamman mata da kananan yara.
Wannan fitinar ta fi yin tasiri a kauyuka, musamma na jihohin Kudu kamar Edo da Delta da wasu sassan Arewa, inda ake kai ’yan mata Saudiyya su yi aikatau daga nan sai su makale, rayuwarsu ta koma kan sikeli, su yi nan, a yi can da su! Sannan da dama daga cikin matan nan kan tsallaka ko akan rufe musu ido sukan iske babu wata sana’a da za su tsira da ita sai karuwanci, inda kasar Italiya kan karbi manyan baki da alhazai.
Abin tambaya a nan laifin wane ne? tabbas laifi na wuyan shugabanninmu da suka lalata tattalin arziki, suka jefa mu cikin wahala da bakin jahilci. Tare da yadda malamai suke kin amfani da basirar da Allah Ya ba su wajen nuna muhimmancin kishin kasa wajen gina kasar da kishin kai.
Ya kamata talakawa su zama masu hakuri da hangen nesa, domin Turai ba Aljanna ba ce, hasali mutane nawa suka je Turai cikin gata suka dawo a tsiyace! Sukan rasa tarbiyya inda ake gudun ba su ’ya su aura, ko wurin kwana, ko ma a hana yara wasa da ’ya’yan da suka dawo don kada su gurbata tarbiyya.
Sau da yawa idan mutum ya dawo sai ya rasa inda zai fara, wadansu kan nemi jari amma sai su cinye su gaza biyan bashin da ya yi musu katutu. Ga ba ilimi sai dogon buri, kai da ko sana’a ba ka iya ba sai ka rika wasikar jaki tare da kyuatar miliyoyin daloli a duniyarka!
Tabbas ya kamata malamai da gwamnatoci da ’yan wasan kwaikwayo da mawaka su tashi tsaye wajen fadakar da mutane kan fa’idar zama a gida, domin duk wanda ya bar gida, gida ya bar shi.
Girmama baki da tausayin talaka na daya daga cikin abubuwan da suke bambanta mutum da dabba! Sannan idan muka kwatanta ladan da ake samu wajen ciyarwa da kullun sai an ba da sadaka, musamman ta fuskar ciyar da talaka. Amma a yau da sunan wayewar zamani an yi watsi da wannan mutunci, idan ba za a karu da kai ba ko sallama ba a yi maka balle ta yin bisimillah!
Idan da za a koma ga koyarwa da gaskiya kamar yadda addini ya tanada da ba a yi kyashin juna ba, domin da talaka da attajiri duk ’yan Adam ne.
Akwai arziki a Afirka, musamman a Najeriya, kuma mun fara dacewa da shugabanni nagari, tabbas ba mu da inda ya wuce kasarmu, duk inda muka je ba inda za mu yi kewa kamar gida. Duk inda ka je ko kake son zuwa ba inda ya kai gida.
Duk da cewa sukan wulakanta kansu ta hanyar cudanya da maza mabambanta wdaanda wadansu kan kare da kamuwa da wasu cutuutuka ko a dawo da su ta yadda damuwar rayuwa kan addabe su kuma sun mutum ba shiri, wadansu ma mutuwa ta zo musu cikin kuruciyar. Wannan harkar na sa an tasa keyar dubbai dawowa gida daga Arewacin Afirka.
Akwai kungiyoyi da dama da suka shafi fataucin mutane kamawa da wadanda suke taimakawa wajen dakile harkar da wadanda suke tafiyar da harkar, yayin da suke yaki da juna, idan kasa na son tsira da mutuncin kanta dole ta kama fataken mutane da hukunta su.
Wasu kasashe kan kafa dokoki ta yadda ko da dan kasar ya fita kwadago a kasashen ketare dole ya kawo hakkin ilimintarwa da haraji domin ai kasarsa ta ba shi ilimin farko, aka kula da rayuwarsa a matakin farko.
A dawo da wadanda suka yi hijira, tabbas kishin kasa na daga cikin imani ga Ubangiji, kuma kungiyoyi da gwamnatoci a matakai mabambanta su yi hobbasa wajen mayar da bakin haure ’yan kasa nagari.
Buhari Daure
Modoji, Katsina
za a iya samunsa ta imel: [email protected]