Yaki da miyagun kwayoyi a Jihar Kano

A ranar Alhamis din makon jiya ne Gwamnatin Jihar Kano a karkashin jagorancin Ma’aikatar Shari’a ta Jihar da sashen kula da ingancin ayyukan gwamnati (SerbiceCom) ta gudanar da taron yini daya a jihar kan illolin sha da fataucin miyagun kwayoyi. Gwamnatin ta bayyana niyyar za ta kafa hukumar da za ta dora wa alhakin yaki da […]

Yaki da miyagun kwayoyi a Jihar Kano
Yaki da miyagun kwayoyi a Jihar Kano

A ranar Alhamis din makon jiya ne Gwamnatin Jihar Kano a karkashin jagorancin Ma’aikatar Shari’a ta Jihar da sashen kula da ingancin ayyukan gwamnati (SerbiceCom) ta gudanar da taron yini daya a jihar kan illolin sha da fataucin miyagun kwayoyi. Gwamnatin ta bayyana niyyar za ta kafa hukumar da za ta dora wa alhakin yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi, sabanin irin wadanda hukumomin Gwamnatin Tarayya irin su Hukumar Yaki da Tu’ammali da Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) da ta Kwastam da ta Tsaro ta Farin Kaya (NSCDC) da ta Kula da Ingancin Abinci da Abin sha (NAFDAC) da aka dora wa alhakin wannan aiki suke gudanar da nasu.

Yanzu dai Kundin tsarin mulkin kasar nan na 1999, da aka yi wa kwaskwarima ya ware yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi kacokan a cikin batutuwan da Gwamnatin Tarayya kadai ke da ikon yi, kamar yadda take da iko a kan batutuwan da suka shafi kafawa da kula da masu damara, irin ’yan sanda da Kwastam da masu kula da shigi-da-fici. Wadannan tanadi na Kano na iya samun cikas kan wannan niyyar, kamar yadda a shigowar wannan jamhuriyar aka yi ta samun cece-ku ce lokacin da jihohi suka kafa rundunonin Hisbah da na kula da ababen hawa da makamantansu.

Taron na Kano, mai karatu ka iya cewa dori ne a kan kwatankwacinsa na kwana daya da Kamfanin Media Trust mai buga jaridun Daily Trust da Aminiya ya gudanar a Kano a ranar 22 ga watan Nuwamban da ya gabata. Taron da Babban Editan Kamfanin Malam Mannir Dan-Ali ya fadi wajen bude shi cewa suna gudanar da shi ne a zaman fadakarwa da wayar da kan al’umma, a matsyayin gudunmuwar da kamfanin zai iya bayarwa don kyautata zamantakewar al’umma. Sai kuma la’akari da  yadda annobar shan miyagun kwayoyi ta zama ruwan dare a jihohin Arewa da kasa baki daya, annobar da ya ce tana bukatar taimakon kowa da kowa.

A shekarun 2015, da 2016, da 2017, a jere, Hukumar  NDLEA, a cikin rahotanninta ta bayyana Jihar Kano, a matsayin jihar da ke kan gaba a cikin jihohin kasar nan da Birnin Tarayya, Abuja wajen tu’ammali da miyagun kwayoyi. Ko a ’yan watannin da suka gabata sai da hukumar a wani rahotanta ta sake cewa a kullum ana shan kwalbar kodin miliyan 3, (a matsayin daya daga cikin kayan maye da masu shan miyagun kwayoyi suke tu’ammali maimakon magani).

Wadannan rahotanni ko kusa ba su yi wa mahukuntar jihar dadi ba, don haka suka yi ta musanta su, musantawar da ba ta sa hukumar ta janye matsayinta ba.

Ka iya cewa Kano ta yi wannan mummunar suna ne bisa ga kasancewarta jiha mafi yawan jama’a, kuma babbar cibiyar kasuwanci, uwa uba kuma jihar da ta yi kaurin suna a kan ayyukan ’yan daba da bangar siyasa da husuma ta ba gaira ba dalili. Kazalika yanzu annobar shan miyagun kwayoyin a jihar a kullum tana daukar sabon salo, kasancewar bayan kayayyakin sa maye irin su bula da man fetur da kashin kadangare da zakami da tabar wiwi da giya, kuma a tsakanin matasa maza, yanzu  an samu kari da miyagun kwayoyi irin su Tiramol da kodin da sauransu. Kuma annobar ta yadu har zuwa ’yan mata da matan aure, kuma babu batun gidan mai hali da marar hali, balle kuma a gidan saraki da talaka, ta dai zama ruwan dare game duniya, Allah Kai mana magani.

A jawabin da ya aike wajen bude taron, ta hannun Sakataren Gwamnatin Jihar Alhaji Usman Alhaji, Gwamnan Jihar Dokta Abdullahi Umar Ganduje, kokawa ya yi a kan irin mummunan kamarin  da annobar da shan miyagun kwayoyi ya yi a jihar musamman tsakanin matasa maza da mata, inda yake kara haddasa aikata miyagun laifuffuka da sauran ta’addanci. Abin da ya ce yana bukatar kara yin zurfin tunani a kan hanyoyin da za a tunkari annobar da niyyar dakile ta, ko ma kawar da ita kwata-kwata a jihar.

A fadar Gwamna Ganduje, niyyar gwamnatin jihar ce ta yi wani abu sabo a kan yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyin ta hanyar kafa wata sabuwar hukuma ta farko irinta a kasar nan da ayyukanta za su kunshi rigakafi da tsarin gudanar da bincike don fahimtar musabbabin tushen wannan mummunan alkaba’i, kuma ta shige gaba wajen gyaran zukata da  horarwa tare da samar da ayyukan yi, duk da niyyar sake mayar da masu tu’ammali da miyagun kwayoyin  cikin mutanen kirki. Don haka sai Gwamnan ya jefa babban kalubale ga masu ruwa-da-tsaki da aka gayyato taron, yana mai tunatar da su cewa dama ce gare su, su yi kyakkyawan nazari da tuntubar juna da niyyar fito da mafita.

Mai karatu ya kamata ka sani cewa duk masu ruwa-da-tsaki maza da mata da kake jin a gayyato don ba da kasida a wancan taro an gayyato su, sun kuma hallara tare da gabatar da kasida, tun daga kan malaman jami’a zuwa jami’an tsaro masu daura damara da malaman addinin Musulunci kungiyoyin kare hakkin dan Adam.

Taro ne dai ka iya cewa duk abin da gwamnatin Jihar Kanon take bukata don kafa waccan hukuma ta samu, don kuwa hatta batun rashin damar da take da shi na kundin tsarin mulkin kasar kan bai ba ta damar kafa irin wannan hukuma, lauyoyi da ’yan boko da jami’an tsaro sun ce za ta iya.

Saura da me? Ya rage ga gwamnatin Jihar Kano ta nuna da gaske take kuma tana da karfin nufin da za ta kafa hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyin da magance mata annobar da a kullum yaduwa take tamkar wutar daji, kuma ta tabbatar za ta sakar mata mara ta yi aikinta cikin kamanta gaskiya da adalci.

Ba don komai na fadi haka ba, sai sanin da na yi cewa wadansu ’yan siyasa musamman  masu rike da madafun iko na taka gagarumar rawa wajen shaye-shayen miyagun kwayoyi da matasanmu suke yi yau a kasar nan. Akasarin ’yan siyasar sukan ba matasan kudaden sayen kayan mayen, don kawai su yi musu bangar siyasa, kazalika ko kama matasan aka yi da wata ta’asa, ’yan siyasar dai, kan shige gaba wajen karbo su  daga hannun jami’an tsaro, ko alkalai, daga nan kuma maganar ko shari’ar ta mutu. Na tabbatar da cewa muddin Kano ta kafa wannan hukuma da ta yi niyya, sauran jihohi za su kwaikwaya, don kuwa annobar sha da fataucin miyagun kwayoyi, annoba ce da ta addabi kowa.