Yaki da rashin tsaro ba na gwamnati kadai ba ne – Al-Makura
Gwamnan Jihar Nasarawa Umaru Tanko Al-Makura ya ce yaki da rashin tsaro a jihar bai kamata a bar shi a hannun gwamnati kadai ba, don haka ya yi kira ga kungiyoyin addinan nan biyu da ke jihar wato na Musulmi da na Kirista su zage dantse wajen fuskatar matsalar rashin tsaro da ke addabar jihar […]
Gwamnan Jihar Nasarawa Umaru Tanko Al-Makura ya ce yaki da rashin tsaro a jihar bai kamata a bar shi a hannun gwamnati kadai ba, don haka ya yi kira ga kungiyoyin addinan nan biyu da ke jihar wato na Musulmi da na Kirista su zage dantse wajen fuskatar matsalar rashin tsaro da ke addabar jihar a ’yan kwanakin nan ta hanyar kirkiro shirye-shiryen da za su inganta hadin kai a tsakanin al’ummar jihar. Gwamna Al-Makura ya bayyana haka ne wajen rantsar da shugabannin Hukumar Jin Dadin Kiristoci masu aikin Ziyara ta jihar da aka gudanar a Lafiya fadar jihar.
Gwamna Al-Makura wanda Sakatariyar Gwamnatin Jihar Hajiya Zainab Abdulmumini ta wakilta ya yaba wa hangen nisan Babban Sakataren Hukumar Jin Dadin Kiristoci masu aikin ziyara Barista Clement Ode Magaji kan gudunmawar da yake badawa wajen dorewar zaman lafiya a tsakanin al’ummar Kiristoci da Musulmin jihar.
Shugaban biki Sanata John danboyi wanda ya bayyana shirin a matsayin irinsa na farko da aka taba gudanar a jihar, ya yi kira ga Kiristoci masu ziyara daga jihar da kasa baki daya su rika yin kokari suna daukar nauyin kansu zuwa kasa mai tsarki ba su rika jira gwamnati tana biya musu kudin tafiyar ba.
Ya shawarci babban sakataren hukumar Barista Clement Magaji ya rika tantance wadanda suka kai ziyarar a bara don ba sababbin maniyyata damar zuwa.
A jawabansu shugabannin kungiyar Kiristocin Najeriya reshen Jihar Nasarawa Bishop Mila Maza da Kwamishiniyar Hukumar Masu Ziyara Kiristoci a yankin Arewa ta Tsakiya, Misis Healin Joseph sun shawarci maniyyatan su dauki aikin Ubangiji da za su je kasa mai tsarkin da muhimmanci ta hanyar gudanar da addu’o’i na musamman ga jihar don kawo karshen rigirgimu da take fuskanta a halin yanzu. A jawabi Babban Sakataren Hukumar Barista Clement Magaji ya ce sun yanke shawarar shirya bikin ne inda aka gayyato Musulmi a jihar domin kawo hadin kai da wanzuwar zaman lafiya a jihar baki daya. Aminiya ta gano cewa wannan biki shi ne irinsa na farko da aka gudanar a jihar wanda ya samu halartar sarakunan gargajiya da shugabannin Kiristoci na jihar da na kasa da jami’an gwamnati da al’ummar Musulmi da Kiristoci da sauransu.