Yaki da shan inna: Da sauran rina a kaba(1)

  Shan Inna wata nau’in cuta ce da ke kama kanananan yara ta nakasa su,tana mutukar barazana ga yara ne tun daga lokacin haihuwarsu zuwa shekaru Biyar na yarintarsu.Kafin gano mece ce cutar shan Inna a yankunanmu na kasashen Hausa tun da ana danganta cutar ne da cewa shafar aljannu ce. Ana cewa wata jinnu […]

Yaki da shan inna: Da sauran rina a kaba(1)
Yaki da shan inna: Da sauran rina a kaba(1)

 

Shan Inna wata nau’in cuta ce da ke kama kanananan yara ta nakasa su,tana mutukar barazana ga yara ne tun daga lokacin haihuwarsu zuwa shekaru Biyar na yarintarsu.
Kafin gano mece ce cutar shan Inna a yankunanmu na kasashen Hausa tun da ana danganta cutar ne da cewa shafar aljannu ce. Ana cewa wata jinnu ce da ake kiranta da Inna takan shafi yaro saboda haka sai ya taso jikinsa a shanye, don haka ma da zarar an ga alamunta sai a garzaya wajen ’yan bori don neman magani da a karshe yake gagara sai yaron da abin ya shafa ya tashi cikin nakasa idan aka yi sa’a bai rasa ransa ba..
Iyayemmu da dama sun wahala matuka kafin a gano cewa, shan inna kwayar cuta ce da take kama kananan yara, har takai ga nakasa su. Gano hakan, ya rage larurar da ake yi da ’yan bori da bokaye bisa tsammanin da ake na cewa aljana Inna ce take shafar yara.
Cutar Shan Inna ba kawai a nan kasar ba a wasu kasashen Afirka da kasashen Asiya, irin su Indiya da Pakistan da wasu yankunan Latin Amurka tayi barazana sosai wajen cutarda kananan yara wannan tasa Gwamnatocin kasashe da Majalisar dinkin Duniya,da manyan kungiyoyi masu taimaka wa harka jinkai da rashin lafiya suka tashi haikan wajen ganin bayan wannan muguwar cuta, ta hanyar gudanar da rigakafinta ga kananan yara.
Najeriya na daga cikin kasashe da aka samu cutar ta shan inna tana kaiwa da komowa. Don haka kasashe masu tallafa wa yaki da cutar tare da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) Asusun tallafa wa rayuwar yara ta Duniya (UNICEF) da Gidauniyar Bilgate da Melinda (Billgate & Melinda) da Gidauniyar Dangote da sauran kungiyoyinmu na kasa da gwamnatoci a matakai daban-daban tun daga matakin tarayya da jihohi da kananan hukumomi hade da sarakuna da hakimai dagatai da masu unguwanni, da suka tashi haikan dan ganin an  sami nasarar kawar da barazanar cutar ta dakile yaduwarta ta hanyar tabbatar da cewa an yi wa yara ’yan kasa da shekaru biyar riga-kafin cutar.
Wannan mataki na yakar dakile yaduwar cutar shan inna, ya fuskanci matsaloli sosai a tsakanin al’ummarmu, musamman ma a wasu manyan garuruwa na Arewacin kasar nan da suka hada da Kano da Kaduna da Katsina da Sakkwato da sauran garuruwa da dama, musammam bisa zato da zarge-zarge da aka rika dorawa akan sahihancin yin riga-kafin, musammam ma ganin yadda hukumomi suka tashi tsaye haikan dan tabbatar da sai lallai kowa ya ba da dansa an yi masa riga-kafin alhali akwai wasu dimbin cututtuka da su ma suke bukatar wannan kulawa ta musamman don dakile su musammam ma mutane masu korafi sun fi kafa hujja da yaduwar cutar zazzabin cizon sauro. An yi ta kewayawa da maganganu na tuhumar hukumomi akan dagewarsu na cewa kowane mai yaro da bai wuce wa’adin karbar rigakafin ba sai lallai ya mika dansa an yi masa.
Mutane da dama zarge-zargen ya yi musu tasiri, musamman ma da suka ga an matsa kan sai lallai sun ba da ’ya’yansu an yi musu. Cikin zargin da ya fi tasiri a baya shi ne na cewa,yin riga-kafin wani tsari ne da aka kudunduno a fakaice,don shigar da tsarin iyali a cikin al’umma da yawanci suke kyamatarta.
Masu wannan zargi a lokacin sun karfafa cewa ana bai wa yara rigakafinne yanzu wanda sai nan gaba in sun girma tsarin kayyade iyalin zai yi aiki a jikinsu. Hakan tasa wasu iyaye fur suka ki yarda da rigakafin ta bijire a yi wa ’ya’yansu.har ta kai a wasu wuraren sai an yi jan ido an matsa wa mutane, har sai an yi amfani da karfin gwamnati an tilasata wa mutum sannan yake yarda a yi wa iyalansu.Wannan mataki ta kai har ga kama wasu magidanta a rufe su saboda bijerewar da suke yi.
Hukomomi sun yi kokari haikan wajen su wayar da kan al’umma,ta nuna musu wadannan zarge-zarge ba haka yake ba ta daukar matakai daban-daban wajen wayar da kan jama’a har ma da yin ihisani ga yara da iyaye da suke amincewa ayi wa ’ya’yansu..
Akwai wani tsohon gwamna da aka taba yi cikin zababbun gwamnonin kasar nan,a lokacinsa yasa an gudanar da bincike, domin yankan shakku a kan maganin da ake anfani da shi, a rigakafin daga karshe aka samu sakamako da tabbacin da ya nuna rigakafin na shan-inan, bai da wata illa da ake zato.
Irin kokarin da hukumomi da kungiyoyi na gida da na waje suka yi wajen wayar da kan al’umma don su amince da karbar rigakafin ya saukaka kaifin kamuwa da cutar ta shan-inna, har ana sanya kasar nan cikin kasashen da aka dau lokaci ba a ji inda aka ga alamun bayyanar cutar ba a halin da ake ciki.
A iya cewa duk da wannan kokari da ake na raba kasar da cutar “Polio,” akwai wasu abubuwa da suke faruwa, idan ba a sanya kula da daukar mataki akai ba a iya cewa ana tufka ne wasu na warwarewa.
Wasu manyan jihohin Arewacin kasar nan domin kuwa a wasu lokutan ana aikin ne a rubuce a takarda, amma ba a aika ce ba. Domin da zarar an fita bakin aiki da ake yawan aiwatarwa na rigakafin lokaci bayan lokaci, yawancin gidaje da ake zana alamar shaidar an yi wa ’ya’yansu riga-kafin, bincike ya nuna sam ba,a yi musu.
Wani bincike na bin diddigi ya nuna cewa, da zarar wasu cikin, ma’aikatan da ake dauka na musamman sun fito bakin aikinsu na bin gidaje, su su rika diga rigakafin sai su hada kai da masu gidan da dama suke turjiya ga yi wa ’ya’yansu rigakafin, a ba su dan “ihisani” kyautar da da aka tanada ake bai wa duk gidan da aka yi wa riga kafin, sannan su cike takardu na shaidar anyi, sai su diga wa yaran alamar tawwada da ake sawa a dan yatsa, na nuna shaidar an yi musu, sai kuma su tsiyayar da ruwan maganin su tafi da kwalbar da ta zame musu shaidar sun gudanar da aikinsu.
Muddin ba a kara sa’ido da kulawa sosai ba, musamman akan ma’aikatan da suke shiga gida-gida, suna rigakafin, to zai zama nasarar da aka ce Najeriya ta samu na dakile yaduwar kwata- kwata zai zamo da sauran rina a kaba. Kada a yi mamaki jin cutar ta bulla a wani waje a lokacin da ba a tsammanin. Allah ya kiyaye bisa yakinin da zaton da ake da shi na game dukkan yaran kasar nan da rigakafinta alhali kuwa ana tufka wasu na warwara.

 

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno