Yaki na Ruhaniya (2) Sanin magabcinmu:
Kowace kasa da za ta shiga cikin kai harin yaki zuwa wata kasa; dole ne ta yi kokarin sanin wannan kasa da za ta fuskanta da yakin, ta san kowane irin kayan fada ne a gar esu, su san karfin sojojinsu, su kuma san irin dabarunsu, muddin ba a yi la’akari da wadannan muhimman abubuwa […]
Kowace kasa da za ta shiga cikin kai harin yaki zuwa wata kasa; dole ne ta yi kokarin sanin wannan kasa da za ta fuskanta da yakin, ta san kowane irin kayan fada ne a gar esu, su san karfin sojojinsu, su kuma san irin dabarunsu, muddin ba a yi la’akari da wadannan muhimman abubuwa ba; to babu shakka zai zama da wuya a ci nasara bisa kowane irin magabci.
Ina so mu sake duba inda muka yi karatu daga farkon wannan koyarwar; a cikin Littafin Afisawa:6:12, maganar Allah na koya mana cewa: “Gama kokawarmu ba da nama da jini take ba, amma da mulkoki da ikoki da mahukumntan wannan zamani mai duhu da rundunai masu ruhaniya na mugunta cikin sammai.” Sai mu gane wannan sosai domin yawancin lokaci mukan yi tsammani mutum nama da jini shi ne magabcinmu, amma idan muka duba cikin maganar Allah, sai mu iske ba haka yake ba. Kodayake mutum ne mu ke gani a yau da kullum, amma ainihin gaskiyar shi ne ruhun da yake aiki a cikinsa Iblis ne da kansa. Mu sani cewa, shugaban wannan mulki ko mu ce masarauta, Shaidan ne da kansa, shi ne yake shugabancin wannan runduna ta duhu mai mugunta kuma. Kada mu manta cewa lokacin da Allah Ya halicci Shaidan, ba a matsayin Shaidan ko Iblis ba ne Allah Ya yi shi, shi wannan Shaidan a yau Allah Ya halicce shi ne a matsayin babban Mala’ika wanda ke da suna LUCIFER; bari mu ga labarin faduwarsa, a cikin Littafin Annabi Ishaya, sura 14 daga aya 12. “Daga sama ga faduwarka, ya Lucifer, dan asubahi! Duba fa, aka datse ka har kasa, kai mai kasar da al’ummai! Cikin zuciyarka ka ce, zan daukaka KursiyiNa bisa taurarin Allah, zan zauna bisa dutse na taron jama’a, can kurewar Arewa: in hau can bisa madaukakan hadurra, in mai da kai na kamar Mai Iko Duka. Amma dai har Lahira za a gangarar da kai, har zuwa kurewar ramin. Wadanda suka ganka za su zuba maka ido, su yi binbini a kanka, su ce, Ko shi ne mutumin da ya sa duniya ta yi rawa, mai girgiza mulkoki; wanda ya mayar da duniya kamar jeji, ya kabantar da birane; wanda ba ya kan saki mamammunsa su koma gidansu ba? Dukan sarakunan al’ummai, ai, dukansu, a cikin daraja suke barci, kowa cikin gidansa.” (Ishaya:14:12 – 18). Haka nan kuma cikin Littafin Ezekiel: 28:13 – 17:; Maganar Allah ta sake koya mana kamar haka: “ A cikin Eden kake, gonar Allah: kowane dutse mai daraja ya zama rufinka, su sardius da topaz da lu’u-lu’u da beryl da onyd da jasper da sapphire da emerald da carbuncle da zinariya: aikin kayan kidi da na busa naka a cikinka ne; ranar da aka halice ka aka shirya su, kai ne cerub shafaffe, mai rufewa: na kafa ka a bisa dutse mai tsarki na Allah: tafiyarka, kai da kawowa, a tsakiyar duwatsun wuta. Tun ran da aka halice ka kamiltacce ne kai a cikin dukan al’amuranka, har ranar da aka iske rashin gaskiya a cikinka. Ta wurin yawon shagalinka, an cika ka da aikin dazilama, ka kuwa yi zunubi: shi ya sa na ture ka, tozartacce ne, daga dutsen Allah na kuwa halaka ka, ya cerub mai rufewa na raba ka da duwatsun wuta. Zuciyarka ta daukaka saboda jamalinka; hasken ranka ya bata hikimarka: domin wannan na fyade ka na mike ka a gaban sarakuna, su zuba maka ido. Ta wurin yawan sabe-sabenka, cikin cikin wuraren zamanka masu tsarki; domin wannan na sa wuta ta fito daga cikinka, ta cinye ka, na maishe ka toka a kasa ga ganin duk masu kalonka. Dukan masu saninka a cikin al’ummai za su razana dominka; ka zama abin ban tsoro, ba ka da sauran zama ba dadai.” Wannan Shaidan din ba a halice shi a matsayin Shaidan ba ko kadan; dama shi shugaba ne a tsakanin mala’ikun Allah, shi ne shugaban masu hidima a gaban Allah. Rana daya kawai girman kai ya shige shi, sai ya ce, shi ma yana son matsayin Allah, yana so ya zama kamar Allah; har ya samu goyon bayan kashi daya daga cikin uku na mala’ikun Allah wadanda suka yarda da shi, suka yi tawaye cikin Sama, sun manta cewa dukansu halittarsu aka yi. Babu wanda ya isa ya yi gaba da wanda ya yi shi; ko ya halice shi, wannan shi ne sanadin faduwarsa daga daraja zuwa kaskanci da kuma la’ana, wannan kuwa ya faru ne tun kafin Allah Ya halicci mutum, sauran mala’ikun da suka yarda da shi cikin wannan rashin hankali, su ne aljanu a yau, kuma tun lokacin ne Shaidan da wadannan aljanu suka soma gaba da duk shirin Allah. A yau, abu daya da Shaidan ya sa hanlinsa a kai ya aikata shi ne, ya lalatar da duk shiri mai kyau na Allah. Ubangijinmu Yesu Kiristi ya koya mana a cikin Littafin Yohanna sura 10 aya ta 10 cewa: “barawo ba yakan zo ba sai domin sata ko kisa da halaka, amma na zo domin su samu rai, su same shi a yalwace kuma.” Abin da Shaidan magabci yake yi ke nan a koyaushe – sata da kisa da kuma halakarwa. Yana nan tun kafin Allah Ya yi mutum a cikin gonar Adnin; shi ya sa da Shaidan ya ga irin kyakyawan shirin da Allah Ya yi wa mutum, ya yi shiri ya ga cewa mutum bai ci nasara a gaban Allah ba. Yana yin amfani da hanyar rudi domin ya rudi mutane su ki yin biyayya ga umarnin Allah. Sai mu tuna da cewa Shaidan ya fi ka sanin hanyoyin da zai bi domin ya juya maka dukan tunani, shi ne ya sa kodayake mutum ya san dokokin Allah, amma har wa yau yana ketare su, yana aikata abin da Allah ba Ya so; ba domin bai sani ba ne amma domin Shaidan ya rigaya ya mamaye zuciyarsa da duk tunaninsa. Shaidan shi ne babban magabcin kowane mai bin Yesu Kiristi, shi ya sa Allah Yake ce mana a cikin Littafin Bitrus na Fari, Sura biyar aya Takwas: “Ku natsu, ku kuma zama a fadake. Magabcinku Iblis yana zazzagawa kamar zaki mai ruri, yana neman wanda zai lankwame. Ku yi tsayayya da shi kuna dagewa a kan ban-gaskiyarku; da yake kun san ’yan uwanku a duniya duk an dora musu irin wannan shan wuya.”
A kullum Shaidan yana yawan kai da kawowa yana cikin neman wanda zai kashe ya kuma lankwame. Idan har Ubangiji Allah Ya bar mu a cikin masu rai zuwa mako na gaba, za mu yi yi bincike a kan irin tsarin da Shaidan ke da shi cikin nasa mulkin. Mu kuma duba irin hanyoyin da yake bi domin ya cuci mutane. Sanin wannan ne zai sa mu ci nasara bisa Iblis. Mu ci gaba da yi wa kasarmu addu’a domin mu samu zaman lafiya, musamman ma da shekarar siyasa ta gabato. Ubangiji Allah Ya ci gaba da tsare mutanenSa, amin.