Yaki na Ruhaniya (3)

Makon da ya shige, mun soma bincike ne a kan sanin magabcinmu, mun ga cewa yakin da muke ciki ba da nama da jini ba ne, amma da Shaidan da kansa ne wanda shi ne shugaban mulkin duhu. Da yake Shaidan ya rasa gurbinsa da Allah, kuma ba ya da wata tagomashi a gaban Allah […]

Yaki na Ruhaniya (3)
Yaki na Ruhaniya (3)

Makon da ya shige, mun soma bincike ne a kan sanin magabcinmu, mun ga cewa yakin da muke ciki ba da nama da jini ba ne, amma da Shaidan da kansa ne wanda shi ne shugaban mulkin duhu. Da yake Shaidan ya rasa gurbinsa da Allah, kuma ba ya da wata tagomashi a gaban Allah sai ya kudurta ya yi gaba da Allah da kuma dukan mutanen da suke jin maganar Allah. A kullum Shaidan yana aiki tare da sauran mala’ikun da suka bi shi cikin yin tawaye ga Allah. A cikinsu akwai bambanci; domin wasu masu matsayi ne, mai yiwuwa mukamin wasu a cikinsu ya fi na wani, kuma suna da hadin kai sosai domin su iya cimma burinsu. Sukan kuma iya yin amfani da kowane irin abu har ma da mutane shi ya sa akwai mutanen da sun riga sun sayar da zuciyarsu ga Shaidan; sun kuma zama kayan aiki a hannunsa, irin wadannan mutane ba su da tausayi a cikin zuciyarsu ko kadan, sukan iya kashe wani ba tare da dalili ba, kuma ba zai dame su ba ko kadan; sukan iya cutar jama’a kuma ko a jikinsu ba za su ji ba. Irin wadannan mutane suna karkashin iko da kuma mulkin Shaidan ne. Ba su da ’yanci ko kadan su yi abin da suke so. Idan mun lura; sai mu ga cewa sau da dama wani yana son ya rabu da wani irin halin rayuwa; mu dauka misali shan giya, ko yin zina, mutane da yawa masu aikata irin wadannan halaye, sun san cewa Allah ba Ya so, amma sai su ga cewa komai yin kudirinsu, sai su sake iske kansu cikin wannan hali, wani lokaci ma har da kuka da hawaye, za su gaya wa kansu cewa daga yau na daina yin zina ko na bar shan giya, watakila bayan mako daya ko biyu sai ka ga sun koma ga aika abin da ba sa son aikatawa; dalilin daya ne kawai; Shaidan ya riga ya mallaki zuciyarsu. Shi kadai ke da iko bisa zuciyarsu kuma shi kadai ke da ikon ba su umarni ko suna so ko ba sa so. Irin wadannan mutane dole ne sai Allah da kanSa Ya cece su ko Ya ’yantar da su ta wurin ikon Ruhu Mai tsarki da kuma jinin Yesu Kiristi, idan ba haka ba za su yi ta rayuwa ne karkashin bautar Iblis.
Yadda Shaidan yakan yaki mutum:
 Mun sani ta wurin maganar Allah cewa yakin da Shaidan ba na jiki ba ne; yakin nan cikin ruhaniya ake yin sa, ya zama dole mu gane asirin hanyoyin da Shaidan yake bi domin ya yaki Kirista musamman, idan kana bakin daga, kuna kuma kallon juna fuska da fuska da magabcinka, to wannan yaki zai zama da sauki, amma ka tambayi sojoji musamman a yau a JiharBorno yadda suke fuskautar ‘magabta’ da ba sa ganinsu ba, yakin kan zama da wuya sosai. Wani lokaci ma maakiyin naka yana nan kusa da kai amma ba ka sani ba.
Yaudara: Tun daga farkon farawa hanya daya da Shaidan ya yi amfani sosai ita ce yaudara. Yaudara dai rudin wani ne, idan ka iya yin karya, babu shakka za ka iya rudin mutane musamman masu kwadayin kayan duniya. Ainihin nufin Shaidan shi ne; ya ga cewa ya raba tsakanin mutum da Allah. A cikin Littafin Farawa:3:1–7, maganar Allah na cewa “Amma maciji ya fi kowane dabba da Ubangiji Allah Ya yi, hila. Ya ce wa macen, ashe, ko Allah Ya ce, Ba za ku ci daga dukan itatuwa na gona ba? Sai macen ta ce wa macijin, daga ’ya’ya na itatuwan gona an yarda mana mu ci, amma daga ’ya’yan itace wanda ke cikin tsakiyar gona, Allah Ya ce ba za ku ci ba, ba kuwa za ku taba ba, domin kada ku mutu. Sai macijin ya ce wa macen, ba lallai za ku mutu ba: gama Allah Ya sani ran da kuka ci daga ciki, ran nan idanunku za su bude, za ku zama kamar Allah, kuna sane da nagarta da mugunta. Sa’anda macen ta lura itacen yana da kyau domin ci, abin sha’awa ne kuma ga idanu, itacen kuma abin marmari ne domin ba da hikima, sai ta dibi ’ya’yansa, ta ci ta kuma ba mijinta tare da ita, shi kuwa ya ci. Dukan su biyu kuwa idanunsu suka bude, suka waye kuma tsirara ne su; suka dundunke ganyayen baure, suka yi wa kansu mukuru.”  
Idan muka dubi wannan labarin abin da ya faru a gonar Adnin, za mu ga yadda ya shigo har ya rudi ita Hauwa’u da mijinta Adamu, sai ka yi mamaki yadda wani zai zo ya sa ra’ayinsa ga miji da matarsa, wadanda Allah Ya riga Ya ba su komai a yalwace, suka ki bin umarnin Allah; suka gwammace su bi shawarar Shaidan, maimakon bin umarnin Ubangiji Allah. Haka Shaidan yake yi a koyaushe, ya ga cewa ya kawo gaba tsakaninka da Allah. Abin da ya sa mutane da yawa suke fadawa jikin jarrabawa daban-daban shi ne rashin lura da koyarwar Allah. Abin da Shaidan yake yi shi ne; ya kawar da idanun mutane daga gaskiyar maganar Allah na dan lokaci. Ainihin makaminsa shi ne yaudara.
Kwadayin kayan duniya:  “Ku mazinata, ba ku sani ba abutar duniya magabtaka ce da Allah? Duk wanda yake so ya zama abokin duniya fa yana maida kansa magabcin Allah.” (Yakub:4: 4). “Kada ku yi kaunar duniya, ko abubuwan da ke cikin duniya. Idan kowa ya yi kaunar duniya, kaunar Uba ba ta cikinsa ba. Gama dukan abin da ke cikin duniya da kwadayin jiki da sha’awar idanu da darajar rai ta wofi, ba na Uba ba ne, amma na duniya ne. Duniya ma tana wucewa, duk da sha’awatata: amma wanda ya aikata nufin Allah ya zauna har abada.” (1Yohanna 2: 15–17).  Mu sani cewa wannan yaki a cikin zuciyarmu ne ya soma, Iblis zai kawo mana tunani cikin zuciyar mutum cikin yaudara; kuma duk abin da zai yi kokari ya yi shi ne, ya kawo abubuwan da ke cikin wannan duniya da nufin rudin mutane, wadannan abubuwa sun kunshi kudi da dukiya da mata da neman matsayi ko mulki da sauransu. Ina so mu gane cewa dukan wadannan ababe ba wai akwai wani abu mara kyau game da su ba ne, amma idan kwadayinsu ya fi kaunar da muke da ita zuwa ga Allah, to ya zama kamar gunki ne a rayuwar kowane mutum. Yakin da muke ciki shi ne, yadda za mu iya rike Allah cikin zuciyarmu fiye da wadannan abubuwa. Jarabobin duniya su ne sukan raba mutum da Allah, sai mu yi hankali.
 Za mu ci gaba mako mai zuwa mu ga yadda za mu fahimci hanyoyin Shaidan mu kuma yi yaki har mu ci nasara. Allah Ya taimake mu, Ya kuma ba mu sa’a irin tasa cikin wannan mako. Allah Ya tsare mu duka daga kowace irin jarrabawar Shaidan, Ya kuma ba mu zuciya wadda ta dogara gare Shi, Shi kadai, amin.