Yaki na Ruhaniya (4)
A cikin makon da ya shige mun soma ganin kadan daga hanyoyin da Shaidan yakan bi domin ya ga cewa mutum bai gamsar da Allah cikin ayukansa na yau da kullum ba. Za mu ci gaba da duba irin wannan yaki na ruhaniyya, yadda ya kamata mu fuskanci irin kalubalen da muke samu daga Shaidan […]
A cikin makon da ya shige mun soma ganin kadan daga hanyoyin da Shaidan yakan bi domin ya ga cewa mutum bai gamsar da Allah cikin ayukansa na yau da kullum ba. Za mu ci gaba da duba irin wannan yaki na ruhaniyya, yadda ya kamata mu fuskanci irin kalubalen da muke samu daga Shaidan da magoya bayansa, mu kuma ci nasara a bisansu gaba daya.
Shirin da kowane mai bin Yesu Kiristi ya kamata ya yi:
Maganar Allah na koya mana a cikin Littafin Timothawus ta Biyu sura Biyu aya uku zuwa Biyar: (2Timothawus 2: 3 – 5) cewa: “Ka daure shan wuya tare da ni, kamar mayakkin kirki na Kiristi Yesu. Mayakin da ke a kan sha’anin yaki ba za ya nannade kansa da al’amarin wannan rai ba; gama yana so ya gami wanda ya rubuta shi mayaki. Idan kuma mutum yana kokawa cikin wasa, ba a yi masa rawanin ba, sai ya yi kokawa daidai.” Da zarar mutum ya karbi Yesu Kiristi ya zama mai cetonsa; daga lokacin sunansa ya shiga cikin sunayen mayakan Yesu Kiristi. Yesu Kiristi shi ne shugaban wadannan mayaka. Idan kuwa muna so mu zama masu nasara cikin wannan yaki; dole ne mu bi ka’idojin da shi shugabanmu ya tsara. Babu yadda za mu gamshi Allah ba tare da bin umarninsa ba. daya daga cikin abin da Ubangiji Allah Yake so da kowane mayakin da ke cikin rundunarsa shi ne ya kasance mutum wanda ya kimtsa hankalinsa wuri guda; ba mai rawar ido ba ko kadan. Maganar Allah tana koya mana cewa, idan har muna da niyyar cin nasara, to ba za mu iya nannade kanmu da al’amuran wannan rai ba, ma’ana, dole mu kafa ido a kan shi shugabanmu; Shaidan yana da hanyoyin kawo jarrabawa da yawa da yakan shirya domin ya dauke hankalin mutane daga ainihin bauta wa Allah cikin gaskiya. Wadannan sun kunshi kwadayin kayan duniya, abu guda wanda mutane da dama suna fama da shi, shi ne kayan duniya – dukan abin da ba zai taimaki mutum ya bauta wa Ubangiji Allah da zuciyarsu ba, tushen irin wannan abubuwa kuwa KUdI ne. A yau neman kudi ya shiga cikin zuciyar mutane da yawa; mutane sukan iya yin komai domin su samu kudi daga yin sihiri ko kuwa tsafi zuwa kisa; koda danginsu ne.
Samun wadata yana da kyau sosai, samun arziki na da kyau; albarka ne daga wurin Allah ga mutum domin kyautata rayuwar jama’a, amma idan hanyar samun wannan kudi ba bisa hanyar da ta dace ba ne; ko ma nawa ne kudin, ba shi da amfani a gaban Allah. Yesu Kiristi ya yi magana a kan bauta wa kudi da Ubangiji Allah tare a cikin Littafin Matta: 6: 24 ya ce “Ba wanda ke da iko ya bauta wa ubangiji biyu: gama ko yaki daya ya kaunaci dayan: ko kuwa ya lizimci dayan ya reaina dayan. Ba ku da iko ku bauta wa Allah da mammon ba.”
Haka nan a cikin Littafin Luka:16:13; Ubangijinmu Yesu Kiristi ya maimaita wannan magana kamar haka “Ba baran da zai iya bauta wa iyayengiji biyu, kodai ya ki daya, ya so daya, ko kuwa ya amince wa daya ya raina dayan, ba dama ku bauta wa Allah da dukiya gaba daya.” Ina so mu gane wani abu mai muhimmanci a nan: Allah Mahalicci Yana so mu bauta maSa; Shi kadai, amma sai muka ga wani abu da ke neman bauta daga wurin mutum –Kudi ko Dukiya. Kamar yadda Allah Yana so mu zama bayinSa muna yi masa hidima; haka kudi ko dukiya kan iya dauke hankalin mutum har ya yi kokarin nema daga wurin mutum, domin ya dauke hankulanmu daga wurin yin sujada ga Allah. Tunanin kudi kadai ya mamaye zuciyarka; barci da dare ma sai ta zama da wahala sosai domin neman kayan duniya, tunaninka ke nan, ko kana wurin ibada ma; yayin da sauran mutane suna ta addu’a suna godiya wa Allah domin alherinSa zuwa gare su, kai kana nan kana tunanin yadda za ka samu wancan kwangilar. Duk irin wannan tunani cikin zuciyar mutum jarrabawa ce daga wurin Shaidan. Wannan yaki ne sosai na cikin ruhu. Sauran jarrabawan ma, idan aka duba a hankali, zancen kudi ne tushensu. Sayen kayan duniya da kudi ake yin su, mene ne yakan kawo kishi tsakanin mutane? Yawancin lokaci idan ka ga wani yana da abu; misali mota mai kyau da ya saya, sai ka gan shi ba wai ya fi ka da komai ba ne, wani abu sai ya ce maka a cikin zuciyarka kai ma ka gwada masa cewa kai ma za ka iya sayen irin motar har ma fiye da wannan; irin wannan tunani ba daga wurin Allah ba ne, Shaidan ne yake kokarin sa gaba tsakaninka da wani.
Dalilin ke nan da maganar Allah a kullum tana koya mana cewa: “Kada ku kaunaci duniya, ko abin da ke cikinta. Kowa yake kaunar duniya baya kaunar Uba ke nan sam. Don kuwa duk abin da yake a duniya, kamar su sha’awa irin ta mutuntaka da sha’awar ido da kuma alfarmar banza, ba na Uba ba ne, na duniya ne. Duniyar kuwa tana shudewa da mugayen burinta, amma mai aikata nufin Allah zai dawwama har abada.” (1Yohanna 2:15–17). Allah ba Ya so mu yi rayuwarmu cikin rashin sanin dabarun Shaidan a wannan karshen zamani; shi ya sa ba za mu gaji da nanata wannan kalma ba kadan, domin Shaidan yana amfani da haka ne ya raba zumuncin da ke tsakanin Allah da mutanenSa, wannan shi ne niyyar Shaidan da sauran wadanda suke aiki tare da shi; ba ya so ya ga wani ya gamshi Allah cikin rayuwarsa.
Ta yaya ne za mu iya cin nasara? Abu na farko shi ne mu zama masu tsaro: A cikin Bitrus ta fari, sura biyar aya takwas (1Bitrus 5: 8), maganar Allah na koya mana cewa: “Ku yi hankali shimfide, ku yi zaman tsaro; magabcinku Shaidan, kamar zaki mai ruri ne yana yawo yana neman wanda za ya cinye.” Dole ne mu zama mutane natsattsu idan har za mu ci nasara bisa Shaidan, dole mu tsare zuciyarmu daga tunanin banza da takan kazantar da zuciya har ta kai ga rabuwa da jin umarnin Allah. Hanyoyin Shaidan a kullum kan kare da hallaka ne.
Idan Ubangiji Allah Ya bar mu cikin masu rai zuwa makon gaba, za mu soma binciken makaman da kowa ya kamata ya dauka domin mu samu cikakken nasara bisa Shaidan a cikin wannan yakin da muke ciki. Kada mu manta da yin addu’a domin jama’ar da suke Borno, Allah Ya kawo musu zaman lafiya da salama. Ubangiji Allah Ya taimake mu, amin.