Yaki na Ruhaniya (6)

Makamai na yakin masu bin Yesu Kiristi:A cikin binciken da muke yi makonin da suka gabata, mun ga yadda masu bin Yesu Kiristi suke fuskantar yaki mai tsanani sosai cikin ruhaniyya da a yawancin lokaci yakan bayyana a fili, ta wurin jarrabawa iri-iri da wahalhalu daban-daban, tsanani ta kowace fuska da sauransu. Abu guda da […]

Yaki na Ruhaniya (6)
Yaki na Ruhaniya (6)

Makamai na yakin masu bin Yesu Kiristi:
A cikin binciken da muke yi makonin da suka gabata, mun ga yadda masu bin Yesu Kiristi suke fuskantar yaki mai tsanani sosai cikin ruhaniyya da a yawancin lokaci yakan bayyana a fili, ta wurin jarrabawa iri-iri da wahalhalu daban-daban, tsanani ta kowace fuska da sauransu. Abu guda da kowane mai bin ubangijinmu Yesu Kiristi ya kamata ya yi ko ta yi shi ne; sanin wannan yaki da muke ciki, bayan haka kuma, mu san cewa irin makamin da kake da shi ne zai sa mu ci nasara ko magabci ya ci nasara a kanmu. Abu na biye shi ne, idan mun san makamanmu, dole ne mu iya yin amfani da su, domin idan soja yana da kayan yaki masu kyau amma bai san yadda ake amfani da su ba; to kayan yakin ba su da amfani ko kadan a gare shi. Magabcin zai iya kwace makamin daga wurinsa ya kuma yi amfani da shi ya ci nasara. Haka dukan masu bin Yesu Kiristi suna da makamai masu iko sosai da zamu duba mu kuma gane yadda ake amfani da kowane makamin domin kada Shaidan ya ci nasara a bisanmu. “Ku yafa dukan makamai na Allah, domin ku samu ikon da za ku yi tsayayya da dabarun Shaidan. Gama kokuwarmu ba da nama da jini take ba, amma da mulkoki da ikoki da mahukuntan wannan zamani mai duhu da rundunai masu ruhaniyya na mugunta cikin sammai. Domin wannan fa ku dauki dukan makamai na Allah da za ku iya tsayayya cikin mugunyar rana, kuma bayan da an gama duka a tsaya. Ku tsaya fa, kun rigaya kun daure gindinku da gaskiya, Kun yafa sulke na adalci, kun daure wa sawayenku shirin bishara ta salama, musamman kuma, ku dauki garkuwa ta ban-gaskiya da za ku iya bice dukan jefe-jefe masu wuta na mugun da ita. Ku dauki kwalkwali na ceto kuma da takobin ruhu, wato maganar Allah: kuna addu’a kowane loto cikin ruhu da kowace irin addu’a da roko, kuna tsare wannan da dukan naciya da roko saboda dukan tsarkaka.” (Afisawa:6:11–14) .
Ina son kowane mai bin Yesu Kiristi ya san cewa, Yesu Kiristi da kansa ne tushen ikonmu da kuma karfinmu. Ba mu da wata madogara kuma ban da sanin ubangijinmu Yesu Kiristi idan har mana so mu yi nasara bisa wannan runduna mai iko sosai na Shaidan da kansa; wadda ainihin nufinsu shi ne su ci nasara bisa Ekklesiyar Kiristi Yesu. Dole ne mu san cewa Shaidan yana kokari ne ya ga mun koma ga aikata zunubi, mu bar bin tafarkin Yesu Kiristi; amma cikin wannan abu duka; muna da tabbaci a cikin Littafi Mai tsarki na tsayuwar EkklesiyarAlmasihu, “Kuma ina ce maka, kai ne Bitrus, a kan wannan dutse kuma zan gina ekklesiyata; kyamaren Hades kuma ba za su rinjaye ta ba.” (Matta:16:18). Muna da alkawarin nasara tun kafin mu soma yakin! Mu kanmu ba za mu iya wannan yaki ba sai dai cikin ikon Allah da kanSa; shi ya sa muka karanta cewa ‘Ku yafa dukan makamai na Allah.’ Za mu soma binciken wadannan makamai dai-dai; mu kuma ga yadda suke aiki cikin wannan yaki da muke ciki.
GASKIYA: Makami na farko a ya kamata kowane mai bin Yesu Kiristi ya dauka, shi ne gaskiya. Maganar Allah na koya mana cewa ku daure gindinku da gaskiya. Mene ne gaskiya? Abin da babu karya a ciki, karya halin Shaidan ne, karya yaren Shaidan ne, a kullum idan zai yi magana, kamar yadda kowane mutum yake da harshensa; misali, Bature zai yi Turanci; Bahaushe zai yi Hausa; mutumin Kare-kare zai yi Kare-Kare, hakan nan Shaidan, shi nasa harshen a koyaushe karya ne kawai ya iya fadi. Shi ya sa kowane mutum makaryaci ba zai taba iya cin nasara bisa Shaidan ba, don yarensu daya ne, kowane makaryaci dangin Shaidan ne. A cikin Littafin Yohanna:14: 6; 17; maganar Allah na cewa, “Yesu ya ce masa, ni ne hanya, ni ne gaskiya, ni ne rai: ba mai zuwa wurin Uba sai ta wurina;…Shi ruhu na gaskiya: wanda duniya ba ta iya ta karbe shi ba; gama ba ta ganinsa, ba ta san shi ba: ku kun san shi, gama yana zaune tare da ku, za shi kuwa zauna a cikinku. A wannan wuri mun ga cewa Yesu Kiristi da kansa ne gaskiya, daya daga cikin asirin cin nasara cikin wannan yaki ga kowane mutum shi ne, samun Yesu Kiristi cikin zuciyarmu. Idan har muna dauke da ruhun Allah cikinmu babu yadda Shaidan zai iya cin nasara a bisanmu. Ruhun Allah ba ya karya, shi ya sa ba zai yi zumunci da Shaidan ba. haka nan idan muka bude cikin Littafin Yohanna, sura goma sha bakwai aya sha bakwai, maganar Allah na koya mana cewa ka tsarkake su cikin gaskiyar, maganarka ita ce gaskiya. Ashe maganar Allah ita ce gaskiya. Allah ba Ya karya kuma ba Ya canja maganarSa domin Shi ba Ya yin kuskure ko kadan, ba Ya kuma janye maganar da Ya rigaya Ya yi. Sanin maganar Allah na da muhimmanci sosai domin shi ne kawai zai sa mu san yadda Allah Yake tunani bisa kowane abin da ke tafe cikin rayuwarmu. “Kada jinkai da gaskiya ta yashe ka ka rataya su a wuyanka: ka rubuta su a kan allon zuciyarka: Da haka nan za ka samu tagomashi da kyakkyawan suna a gaban Allah da mutum kuma.” (Misalai:3:3–4).
Abin nufi a nan shi ne kada mu rabu da gaskiya koda wane irin matsi muke ciki, domin a karshe za mu ci amfanin tsayawa kan gaskiya. Alherin da mutum zai samu ba kadan ba ne, gaskiya ba rudu ba, kariya ne, ko makami ne da za mu iya yafawa domin mu iya cin nasara bisa babban magabci wato Shaidan. Maganar Allah a cikin Zabura:145:18, na koya mana cewa Ubangiji Yana kusa da duk wanda suke kira bisa gare Shi, ga duk wanda suke kira gare Shi da gaskiya. Wani abu guda ya kamata mu gane a matsayinmu na masu bin Yesu Kiristi shi ne; kada mu yarda wani abu ya rufe idanunmu har ya zamo ba za mu iya ganin ubangijinmu Yesu Kiristi ba. Misalai: 20 : 28. Tana cewa jinkai da gaskiya sukan kiyaye Sarki, kursiyyinsa kuma yana tokare da jinkai. Sai mu sani gaskiya tana da ikon kiyayewa ko tsare mutum daga kowane irin kalubalen da za mu fuskanta.
Idan Allah Ya bar mu cikin masu rai mako mai zuwa; za mu ci gaba da wannan bincike. Ubangiji Allah Ya taimake mu.