Yaki na Ruhaniya (6) Makaman yaki na masu bin Yesu Kiristi:
Makon da ya shige mun soma bincike a kan makaman yaki da suka zama dole mu dauka, idan har muna so mu ci nasara bisa Shaidan. Mun gani cewa GASKIYA ita ce makami na farko da kowane mai bi ya kamata ya dauka ko ya yi damara da shi, babu yadda mutum zai iya shiga […]
Makon da ya shige mun soma bincike a kan makaman yaki da suka zama dole mu dauka, idan har muna so mu ci nasara bisa Shaidan. Mun gani cewa GASKIYA ita ce makami na farko da kowane mai bi ya kamata ya dauka ko ya yi damara da shi, babu yadda mutum zai iya shiga cikin fagen yaki idan bai yi damara ba. Gaskiya kuwa ita ce kadai abin da mutum zai iya yin damara da shi. A koyaushe idan Littafi Mai tsarki ya yi magana kan TSATSO yana nufin ba da ’ya’ya ne.
Tun farkon halitta; Allah Ya ba mutum umarnin ya hayayyafa ya mamaye duniya “Allah kuwa Ya sa musu albarka, Ya ce musu, ku hayayyafa ku ribanya, ku cika duniya, ku yi iko da ita ku mallaki kifayen teku da tsuntsayen sararin sama da kuma dukkan abin da yake da rai da yake kai da kawowa cikin duniya.” (Farawa:1: 28).Tun daga farko; Allah bai yi niyya kowane mutum ya kasa haihuwa ba, cikin shirinSa Ya sa a jikin kowane mutum ikon haihuwa. Tambayar ita ce, wane iri ne muke shukawa? A cikin Littafin Misalai, sura goma sha takwas aya ashirin da daya; maganar Allah tana cewa, “Mutuwa da rai suna cikin ikon harshe; Masu kaunarsa kuma za su ci amfaninsa.” Dole ne idan mun gane cewa kalmominmu kan iya zama rai ko mutuwa dole ne mu lura da yadda muke fitar da su. A koyaushe bari kalmominmu su zama da gaskiya domin duk abin da za mu haifa ya zama abin da zai kawo rai ba mutuwa ba. Wannan gaskiyar dai kada mu manta cewa maganar Allah ce. Gaskiyar nan kuwa Yesu Kiristi ne. Abu na biye shi ne:
SULKE NA ADALCI:
Sulke dai kayan yaki ne da kowane mayaki yakan sa domin ya kare kirjinsa daga kowane harbin da magabci zai yi da kibiya ko mashi. Da shi ke mutanen da suka saba yaki da takobi da su kibiya da mashi, dole ne su kare kirjinsu domin a wurin ne Allah lokacin da Yake halittar mutum Ya dasa abubuwa masu muhimmanci cikin jikin mutum, kamar zuciya da take bugawa ta sa jinin jikin mutum ya zaga dukan jikinsa, haka nan kuma huhun mutum da take sa shi yin numfashi, iskar da jikin mutum ke bukata don ci gaba da rayuwa takan shiga daga hanyar numfashi; shi ya sa idan mutum ba ya da zuciya ko huhu, to ka tabbata wannan mutum ba zai rayu ba. Wannan sulke kuwa adalci ne. Mene ne adalci? Adalci dai yin abin da ke daidai a gaban Allah; wannan ba abin da za mu yi lokaci-lokaci ba ne, a’a, abu ne da a kullum za mu dauke shi kamar jikinmu. Shi ne a kullum za mu sa kamar sulke domin ya kare zuciyarmu daga kowane harbin Shaidan. A kowane lokaci Shaidan kan so ya kazantar da tunanin mutum ta hanyoyi daban-daban, yana so kada mu kawo tunaninmu ga bin umurnin Allah, karfin wannan makamin ya danganta ga yadda muka dukufa ga yin abin kirki ko abin da ke daidai a gaban Allah. Adalci na gaske daga wurin Allah yake: “Gama Ubangiji Mai adalci ne; Yana kaunar adalci; mai zuciya sosai za shi ga fuskarSa.” (Zabura:11: 7). “Dare ya tsala, gari ya kusa wayewa:bari mu tube ayyukan duffai, mu yafa sulke na haske. Bari mu yi tafiya da halin kirki, kamar da rana, ba da rigima da maye ba, ba da bin sha’awa da lalata ba, ba da husuma da kishi ba. Amma ku yafa Ubangiji Yesu Kiristi, kada kuwa a shirya wa jiki kafa da za a bi sha’awoyinsa.” (Romawa:13:12–14). Yin abu da tsoron Allah cikin rayuwarmu ta yau da kullum makami ne da yana iya tsare mutum daga kowace hari da Iblis zai kawo masa. A koyaushe Shaidan yakan yi amfani da jarrabawa iri-iri domin ya kawar da hankulan mutane daga bauta wa Allah cikin gaskiya. Sai mu yi hankali domin hanyoyin ke nan – lalata da maye da husuma da kishi da rigima da sauransu; akwai kafofi da yawa da Shaidan kan yi amfani da su domin ya shuka irin wannan kazanta cikin zukatan mutane. Hanya ta farko ita ce abin da muke gani da idanunmu, kamar kallon abubuwa marasa amfani cikin talabijin, akwai wasu tallace-tallace cikin talabijin da muke kallo da dama an shirya su ne domin a tada sha’awar mutane har a kai su ga aikin lalata. Dole mu san wannan. Abu na biye kuma shi ne abin da muke karantawa, akwai wasu mujallu da an rubuta su ainihi domin su kazantar da tunanin mutane, za ku ga cewa wasu ma hoton mata ne tsirara, wasu kuwa labarai ne marasa kyau. Abu na uku da ke kazantar da zuciya shi ne abin da muke ji. Kalmomin wasu wakokin zamani da ake ji ba sa taimako ko kadan. To ashe hanyoyin ciyar da zuciya su ne; idanunmu da kunnuwanmu. Me kake gani ko kallo? Me kake ji? Mutane da dama sun rigaya sun sa kafa cikin zukatansu, Shaidan ya rigaya ya shiga, babu yadda za su iya cin nasara bisa Iblis. Idan kuwa kana kamar haka; to, dole ne sai ka yafe Ubangiji Yesu Kiristi domin kada ka shirya wa jiki kafa da zai sa ka bauta wa Shaidan. A cikin Littafin Misalai, sura goma sha biyu, aya ashirin da takwas ta ce “A cikin hanyar adalci akwai rai, a cikin turbarsa fa babu mutuwa.” Shaidan ba zai iya yin abin kirki ba; shi ya sa kowane mai bin Yesu Kiristi ta wurin aikin kirki zai ci nasara bisansa. Mu yi kokari mu kare zukatanmu daga kazantuwa da ayyukan duhu. Domin ta haka ne kadai za mu iya cin nasara cikin wannan yaki da muka riga muka shiga. Mu ci gaba da yin addu’a domin wannan kasa tamu cewa Ubangiji Allah Ya ba mu zaman lafiya. Ubangiji Allah Ya ci gaba da tsare mu, amin.