Yaki na Ruhaniya (7)

Makamai na yakin masu bin Yesu Kiristi:A makonnin da suka gabata, mun ga yadda mai bin Yesu Kiristi zai yi amfani da makamai na ruhaniyya domin cin nasara wajen yaki da jarrabawa daban-daban da dabarun Shaidan a cikin rayuwarmu ta yau da kullum.A wannan makon za mu yi bincike ne a kan yadda mai bin […]

Yaki na Ruhaniya (7)
Yaki na Ruhaniya (7)

Makamai na yakin masu bin Yesu Kiristi:
A makonnin da suka gabata, mun ga yadda mai bin Yesu Kiristi zai yi amfani da makamai na ruhaniyya domin cin nasara wajen yaki da jarrabawa daban-daban da dabarun Shaidan a cikin rayuwarmu ta yau da kullum.
A wannan makon za mu yi bincike ne a kan yadda mai bin Yesu Kiristi zai yi amfani da makami na uku, wato Takalmin Bisharar Salama.
A cikin Littafin Afisawa, sura shida aya goma sha biyar, maganar Allah na cewa “Bisharar Salama ya zama kamar takalmi a kafafunku.”
Mayaki dai a da har ma a zamaninmu na yanzu, ba ya taba zuwa fagen yaki ba tare da ya sa takalmi a kafafunsa ba, dalili kuwa shi ne mun san dai takalmi na kare kafafunmu daga sukar kaya da kusa da zafin rana da tuntube da dutse da dai sauransu. Na biyu, takalmi musamman a fagen yaki na da amfani sosai wajen kare kaffafu, domin  idan ka ji rauni a kafarka a fagen yaki, magabcinka sai ya samu nasara a kanka, domin ba za ka iya korarsa ba ko ka guje masa domin raunin da ka ji.
Da wannan shirin ne mai bin Yesu Kiristi ya kamata ya shirya kansa ta wurin yada bisharar salama don ya fuskanci wadannan kalubale kamar yadda mayaka kan fuskanta a fagen yaki don kariya da kuma cin nasara. Wannan shiri kuwa na tafe da niyya da kuzari da doki wajen shelar bisharar salama. Wannan shiri ne na ratsawa cikin miyagun magabta da kuzari ba da fargaba ba don makaman ruhaniyya da muke yafe da su.

Bisharar Salama:
Bisharar Salama kuwa ita ce bisharar Yesu kiristi wadda takan kawo salama ga masu bacin zuciya, takan kuma nuna hanyar samun madauwamin rai. Abu ne mai kyau a zamanka na mai bin Yesu Kiristi ka samu wannan takalmi na bisharar salama.  A cikin Littafin Ishaya, sura hamsin da biyu aya bakwai, maganar Allah na cewa; “Me ya fi wannan kyau? A ga manzo yana zuwa ta kan duwatsu, dauke da albishir mai dadi labarin salama.Ya yi shelar nasara, ya ce wa Sihiyona,“Allahnki sarki ne!”
    Kolosiyawa, sura uku aya goma sha hudu na cewa: “Salamar Almasihu kuma ta mallaki zuciyarku, domin lallai ga haka aka kira ku in kuna jiki guda, ku kuma kasance masu gode wa Allah. Maganar Almasihu ta kafu a cikin zuciyarku a yalwace, kuna koya wa juna, kuna yi wa juna gargaɗi da matukar hikima ta wurin rerar wakokin Zabura da na yabon Allah, kuna kuma rera waka ga Allah, kuna gode maSa tun daga zuci.”
Misali, lokacin Idin ketarewa, a cikin Littafin Fitowa, sura goma sha biyu aya goma sha daya Ubangiji Allah Ya umurci Annabi Musa kan shirin Idin ketarewa; “Ga yadda za ku ci shi, da damara a gindinku da takalma a kafafunku… Idin ketarewa ne ga Ubangiji.
A nan dai mun ga muhimmancin sa takalmi a yi damara don ya nuna cewa ’ya’yan Isra’ila na shirye don zuwa kasar alkawari. Idan har muna son mu ci moriyar alkawarin Ubangiji Allah, lallai ne mu yi shiri mu kuma dauki kayayyakin da Ubangiji Allah Ya shirya mana don yaki na ruhaniyya. Yin haka kuwa zai karfafa mu cikin tafiyarmu ta ruhaniyya ya kuma ba mu kuzari cikin yaki na ruhaniyya. Kayan yakin ruhaniyya kuwa kaya ne da ake yafawa har sai mun ci nasara kan yakin nan na ruhaniyya.
Yakin nan ba na nama da jini ba ne, ba kuwa yaki da munanan halayenmu kadai ba ne, amma da duk miyagun hanyoyin da Shaidan ke amfani da su ne don ya mallaki rayuwar jama’a.
Shaidan yakan jarabce mu ta wurin abubuwan da muke shiryawa cikin zukatanmu, yakan yi kokarin juya kyawawan halayenmu da munanan nasa nufin domin ya samu galaba bisa rayuwarmu a kullum. Don haka sai mu yake shi da dukan kayan yaki na ruhaniyya da muka yafa, kada mu ba shi dama cikin rayuwarmu, mu kuma dauki takalman bisharar salama na Yesu Kiristi, Shaidan kuwa zai guje mu.
Mu dogara ga Ubangiji Allah don Shi ne karfinmu kamar yadda yake a cikin Littafin Habbaku, sura uku aya goma sha tara: “Ubangiji Allah Shi ne karfina,Ya sa kafafuna su zama kamar na bareyi, Ya kuma sa ni in yi tafiya a cikin madaukakan wurare.” Lallai ne in muna sanye da kayan yakin nan, Ubangiji zai tafiyar da mu cikin madaukakan wurare a rayuwarmu ta yau da kullum.
Domin haka kada mu ba wa Shaidan zarafi ta wurin rashin fadin gaskiya, ko rashin yin adalci da shelar bisharar salamar Yesu Kiristi da sauran kayan yaki da ya kamata mu yafa. Sai mu tsaya da karfi cikin yada biharar salama, bari kowane tafiyar da za mu yi ya zamana muna dauke da takalmanmu na shelar bishara.
Shi ya sa Littafi Mai tsarki na cewa, mu yafa duk makamai na ruhaniyya don cin nasara bisa Shaidan: “Shirin kai bisharar salama ya zama kamar takalmi a kafafunku”.
Ubagiji Allah Ya ba mu nasara cikin yakin nan na ruhaniyya.
Mu ci gaba kuma da yin adu’a don Gaskiya, Adalci da Salamar Ubangiji Allah su mallaki rayuwarmu a kasar nan, amin.