Yaki na Ruhaniya (9)
Garkuwa ta Ban-gaskiya: “Musamman kuma, ku dauki garkuwa ta ban-gaskiya, wadda za ku iya bice dukan jefe-jefe masu wuta na mugu da ita.”(Afisawa 6:16). Mine ne garkuwa? Garkuwa dai makami ne da kowane mayaki kan dauka domin kariyar kansa daga kowace kibiya da magabci ya harbo. Mu ga yadda kibiyar magabci take bisa ga maganar […]
Garkuwa ta Ban-gaskiya:
“Musamman kuma, ku dauki garkuwa ta ban-gaskiya, wadda za ku iya bice dukan jefe-jefe masu wuta na mugu da ita.”(Afisawa 6:16). Mine ne garkuwa? Garkuwa dai makami ne da kowane mayaki kan dauka domin kariyar kansa daga kowace kibiya da magabci ya harbo. Mu ga yadda kibiyar magabci take bisa ga maganar Allah; kiban wutar mugu, hari daga wurin Iblis ba abu mai sauki ba ne ko kadan, gaba da take tsakanin mai bin Yesu Kiristi da Shaidan tana da tsanani sosai. Amma komai tsananin wannan yaki; muna da tabbacin nasara bisa Shaidan ta wurin nasarar da Yesu Kiristi ya yi a kansa. Ta yaya wadannan kiban wuta suke bayyana? Sau da dama mukan fuskanci matsaloli a cikin rayuwarmu ta yau da kullum, wadannan kalubalen sun kunshi ciwo da rashin abin yi kamar aiki da rashin abin hannu na biyan bukatun yau da kullum, wani lokaci ma rashin abinci a gida, kuma ga shi kana da aure da yara da dai sauransu. Wani lokaci kuwa sun kunshi wahalhalun da ake sha cikin kasa, musamman ma wuraren da ake hargitsi, babu zaman lafiya; babu salama sai tashin hankali da fargaba a kullum; wadannan abubuwa ba su da sauki ko kadan. A cikin irin wannan yanayi ne idan mun tuna cewa Allah Yana nan tare da masu ba da gaskiya gare Shi, za mu iya ratsawa ta ciki har mu kai ga nasara. Wannan garkuwar da kowane mai bin Yesu Kiristi ya zama yana shirye domin ya dauke ta kuwa ita ce ban-gaskiya. Ban-gaskiya dai tana da fannoni daban-daban; da farko dai mun san cewa shigowarmu cikin ceton da Allah Ya shirya wa kowane mutum ta wurin ban-gaskiya ne kadai; wadda kuma ta zame mana adilci. Wannan ban-gaskiyar ce takan sa mu ga bayyanuwar ikon Allah a cikin rayuwarmu; musamman idan muna so mu ga wannan ikon domin aikin al’ajibai iri iri a cikin rayuwarmu. Maganar Allah na cewa cikin Littafin Yohanna ta Fari, Sura biyar aya hudu: “Gama kowane haifaffe daga wurin Allah yana yin nasara da duniya: nasara wadda ta ci duniya ke nan, Ban-gaskiyarmu.” Ashe ceton da masu bi ke da shi ta wurin mutuwar Yesu Kiristi da tashinsa daga matattu ya kawo mu wani matsayin na masu cin nasara bisa duniya da duk abin da ke cikinta. Ba samun ceto kadai muke da shi ba, amma har da samun nasara bisa shi Iblis da mataimakansa. Ina son mu lura cewa kowane abin da muka gani a bayyane da har za mu iya gani ko mu taba, ya riga ya faru cikin ruhu tuknuna. Rayuwa cikin ruhu ta fi rayuwa cikin wannan jiki tabbaci, shi ya sa idan muka ga mutum ko mutane suna yin wasu abubuwa da a ganinmu ba su dace ba, ko ba su da kyau, misali mugunta ko kisa ko cin amana ko danniya da makamantansu, mu sani ya riga ya faru cikin ruhu kafin ya bayyana a fili yadda kowa da kowa zai iya gani a sarari. Shi ya sa Allah Yake ce da mu: yakin da muke ciki, ba da nama da jini ba ne, amma da ruhohi ne, dalilin da ya sa ba za mu iya yin yakin nan da makamai na duniya ba idan har muna so mu ci nasara. Dole ne mu yi amfani da makamai na Allah da su ne makamai na ruhu. Allah Yana so mu kai dagar yakin nan cikin dandalin ruhu inda za mu gamu da Shaidan da mukarrabansa mu kuma ci nasara a wurin; da zarar mun ci nasara a fannin yaki cikin ruhaniya, to babu shakka za mu ga bayyanuwarsa a sarari kuma kowa zai san cewa wannan Allah ne da kanSa Ya ba mu nasara. daya daga cikin wadannan makamai da za su tabbatar da nasara bisa Shaidan idan har muna dauke da su, ita ce ban-gaskiya da muke bincike a kai. To mene ne ban-gaskiya? A takaice dai ban-gaskiya ita ce yarda da maganar Allah da kuma yin amfani da ita, ko kuwa dogara dungum ga Ubangiji Allah da kuma maganarSa. A cikin Littafin Ibraniyawa sura goma sha daya aya daya, maganar Allah tana cewa “Ban-gaskiya fa ainin abin da muke begensa ne, tabbatawar al’amuran da ba a gani ba.”Daga wannan aya mun ga cewa ban-gaskiya ainin abin da muke begensa. Masu iya magana kan ce ‘gani ya kori ji’ amma idan ya zo ga zancen ban-gaskiya, ba sai ka gani ba kafin ka yarda cewa abin gaskiya ne. Manzo Bulus ya ce ta wurin ikon Ruhu Mai tsarki a cikin 2Korinthiyawa 4: 16 – 18, “Saboda haka ba mu karai ba, kodayake jikinmu na mutuntaka yana ta lalacewa, duk da haka, ruhunmu a kowace rana sabunta shi ake yi. Don wannan ’yar wahalar tamu, mai saurin wucewa ita take tanadar mana madauwamiyar daukaka mai yawa, fiye da kwatancin. Domin ba abubuwan da ido yake gani muke dubawa ba, sai dai marasa ganuwa, gama abubuwan da ake gani masu saurin wucewa ne, marasa ganuwa kuwa, madauwama ne.” Haka nan a cikin Littafin Romawa sura biyar aya ta biyu, maganar Allah na koya mana cewa: “Ta wurinsa kuma muka samu shiga alherin nan da muke ciki, saboda ban-gaskiyarmu, muna kuma takama da sa zuciyarmu ga samun daukakar nan ta Allah.” Har ila yau a cikin Ibraniyawa 11: 6 maganar Allah tana koya mana cewa: “ba shi kuwa yiwuwa a gamshe shi ba sai tare da ban-gaskiya ba, gama mai zuwa wurin Allah sai shi ba da gaskiya akwai shi, kuma shi mai sakawa ne ga wadanda ke bidarsa.” Ban-gaskiya abu ne mai muhimmanci ga kowane mai bin Yesu Kiristi; domin babu wata hanya da rayuwarmu za ta gamshi Ubangiji Allah sai dai ta wannan hanya kadai. Ubangiji Allah a kullum Yana jin dadin kowane mutum wanda ya kafa begensa duk a kanSa, yana jin dadin kowane mutum wanda ya yarda da Shi game da kowane irin kalubalen rayuwa, wurin Allah ne kadai wurin zuwa a kowane lokacin bukata. Idan har mun yarda akwai Allah to dole ne mu sani cewa babu wani abin da zai fi karfinSa, Shi da kanSa zai iya yin yaki domin kanSa yadda Ya ga dama, kuma zai yi yaki domin wadanda suka dogara gare Shi. Yaya ban-gaskiya takan zama makami da idan mun dauka za mu ci nasara bisa Shaidan? Idan Shaidan ya kawo hari ta kowane fanni, sai mu duba mene ne maganar Allah game da wannan kalubalen, sai mu gaya wa Shaidan cewa maganar Allah ta ce haka, kuma muna kafa hujjarmu a kai. Babu yadda Shaidan zai iya gaba da maganar Allah; duk lokacin da mai bin Yesu Kiristi yake karkashin inuwar maganar Allah to babu shakka zai samu tsari daga wurin Allah, kuma duk yakin da ya kamata ya yi ta wurin ban-gaskiya za mu iya mika wannan yaki ga Allah. ’Yan uwana, bari mu zama masu ban-gaskiya.Ubangiji Allah Ya taimake mu mu iya rayuwa wadda za ta gamshi Allah a koyaushe.