Yaki na ruhaniyya (10)
Kwalkwali na ceto:“Ku dauki kwalkwali na ceto kuma……” yakin da muke ciki; ba wasa ba ne ko kadan, domin haka dole mu gane ko mene ne cikakken kayan yakin da ya kamata a kullum muna dauke da shi. Kwalkwali dai yana kare kai ne ko mu ce wurin tunaninmu, idan har da gaske mun samu […]
Kwalkwali na ceto:
“Ku dauki kwalkwali na ceto kuma……” yakin da muke ciki; ba wasa ba ne ko kadan, domin haka dole mu gane ko mene ne cikakken kayan yakin da ya kamata a kullum muna dauke da shi. Kwalkwali dai yana kare kai ne ko mu ce wurin tunaninmu, idan har da gaske mun samu ceto; kuma wannan ceton yana aiki cikin rayuwarmu ta yau da kullum, babu shakka tunanin zai canja, zai samu sabontuwa. Ma’ana ita ce ba za mu yi tunani irin na da wanda muka saba yi ba, ba za mu yi tunani kamar yadda mutanen duniya suke yi ba. Gaskiyar ita ce idan har babu bambamci tsakanin yadda muke tunani da yadda wadanda ba su san Yesu Kiristi ba suke yi, zai zamana cewa akwai abin da muka kasa ganewa game da zancen cetonmu. Dole ne mu sake duba rayuwar, mun ga cewa bisa ga maganar Allah; dukan wanda ke cikin Kiristi Yesu, sabon halitta ne shi, tsofaffin al’amura sun shude, ga shi kuwa sun zama sababbbi. Haka nan dole ne tunanin ya zama daban da na da.
Duk da cewa mun rigaya mun samu sauyi cikin tunani, muna da bukata ta kariyar wannan tunanin domin mu zama cikakkun shaida ga dukan sauran mutane. Ceto kuwa shi ne kwalkwalin nan na kariya. Shi ne yake kare lamirinmu da kuma dukan tunanin da muke yi.
A gaskiya ceto yakan kawo sakewa nan da nan cikin rayuwar mutum wanda ya rigaya ya karbi Yesu Kiristi a matsayin mai cetonsa. Za ka iya gane cewa akwai abin da ya faru da wannan domin kowa zai lura cewa halin da aka sanka da shi wadanda ba su da kyau sun bambamta da wanda suke gani yanzu. Har yadda muke tunani ma zai sauya domin sabuwar rayuwa wadda muke da ita cikin Kiristi Yesu.
Gicciyen Yesu Kiristi shi ne ya sa muka san ko wane irin tunani ne ya kamata mu bari ya shigo cikin lamirinmu. Mutane da dama sun dauka cewa idan har sun samu ceto, babu abin da ya rage kuma, suna ganin kamar za su iya rayuwa yadda suka ga dama, su bar kowane irin tunani ya shigo masu zuciya; amma idan har mun gane tsayuwarmu cikin Fansar da muka samu ta wurin Mutuwar Yesu Almasihu bisa giciye, dole ne mu yi tsaye cikin adilcin da Allah Ya ba mu ta wurin wannan hadaya da shi da kansa ya yi. Haka nan kuma za mu iya kare lamirinmu daga banzan tunani mara riba. Maganar Allah ta koya mana a cikin Littafin Misalai 23: 7, cewa “Gama kamar yadda yake tunani a cikinsa, haka yake…..” wannan abu yana da muhimmanci sosai, domin idan yadda muke tunani haka muke, tambaya ta farko ita ce, wani irin tunani muke bari ya kama ranmu, ga wadansu; tunanin mugunta ne kawai; yadda za su cuci wani, wadansu kuwa tunanin zina ne kawai ko fasikanci, wadansu kuwa kishi ne, haka nan wadansu kuwa kisa ne da dai ayyukan duhu.
Akwai wadansu wadanda suka gane dalilin cetonsu daga zunubi, Allah cikin alherinSa Ya ratsa rayuwar gaba daya, tunaninsu na alheri ne a kullum, suna son aika nagarta ba mugunta ba. Dole ne mu kare tunaninmu domin kada Shaidan ya kazantar da shi. Ta yaya muke ciyar da tunaninmu? Sau da dama ba mu sanin cewa akwai kafofi da yawa da Shaidan kan yi amfani da su domin ya cika zuciyarmu da tunanin wofi, tunanin banza. Hanya ta farko ita ce kallon munanan shirye-shirye a tashar talabijin ko karanta mujallu marasa amfani, wadansu irin kidin zamani na shashanci, mutane da dama ba su sanin cewa abin da muke gani, abin da muke karantawa, abin da muke ji sukan tasiri a kan tunaninmu ba. Dole mu tambayi kanmu ko wadanne shirye-shirye ne muke kallo a tashoshin talabijin na wannan zamani? Wace irin mujalla ne muke karantawa, a yau da yawa wadanda suke dauke da hotunan mata tsirara. Sai mu tuna cewa maganar Allah na koya mana a cikin Littafin Galatiyawa:6:7 – 8: “Kada ku bata; ba a yi ma Allah ba’a ba: gama iyakar abin da mutum ya shibka, shi za ya girbe. Gama wanda ya shibka ga jikin nasa, daga wurin jiki za ya girbe ruba; amma wanda ya shibka ga Ruhu, daga wurin Ruhu za ya girbi rai na har abada” Mene ne muke shukawa cikin zuciyarmu a yau? daya daga cikin dalilan da suka sa Manzo Bulus ta wurin ikon Ruhu Mai tsarki ya ba mu asirin abin da ya dace mu yi tunani a kai a cikin Littafin Filibiyawa: 4: 8 wanda ke cewa: “ A kare wa ’yan’uwa, iyakar abin da ke mai gaskiya, iyakar abin da ya isa ban girma, iyakar abin da ke mai adilci, iyakar abin da ke mai tsabta, iyakar abin da ke jawo kauna, iyakar abin da ke da kyakkyawan ambato, idan akwai kirki, idan akwai yabo, ku maida hankali ga wadannan.” Sai mu tambayi kanmu ko a kan mene ne muke mai da hankalinmu? Kwalkwalin ceto, makami ne mai muhimmanci sosai. Yawancin lokaci yakin da muke ciki na Ruhaniya, dagar yakin a cikin tunaninmu ne kamar yadda muka gani a cikin Littafin 2Korinthiyawa 10:3 – 5. Wadda yake cewa “Gama koda muna tafiya cikin jiki, ba mu yi yaki bisa ga jiki ba. (Gama makaman yakinmu ba na jiki ba ne, amma masu iko ne gaban Allah da za su rushe wurare masu karfi) muna rushe zace-zace da kowane madaukakin abu wanda aka daukaka domin gaba da sanin Allah, muna komo da kowane tunani cikin bauta ga biyayyar Kiristi.” Kowane yakin Ruhaniya yana somawa ne da tunani game da abin da muka sa cikin zuciyarmu.
Muddin zuciyarmu ba ta da kariya, to lallai Shaidan zai ci nasara a kanmu. Mu lura, kafin mutum ya aikata kowane irin zunubi, abu na farko da zai auku shi ne; Shaidan zai kawo shawara cikin tunanin mutum, idan ba mu da kariyar kwalkwalin ceto; to babu shakka Shaidan zai rinjayi mutum ya aikata zunubi. Mu yi kokarin shuka abubuwan kirki domin mu yi rayuwar da za ta gamshi Allah. Kada mu gaji da addu’a domin kasarmu da duk shugabanni domin Allah Ya kawo mana sauki cikin kalubalen da muke fuskanta. Sai mako mai zuwa idan Allah Ya bar mu cikin masu rai.