Yaki na ruhaniyya 12
Takobin Ruhu – Wato Maganar Allah: “Ku dauki kwalkwali na ceto kuma da Takobin Ruhu, wato Maganar Allah.” (Afisawa:6:17). Yau za mu ci gaba ne da nazarin da muke yi game da yaki na Ruhaniyya. daya daga cikin muhimman makamai da idan ba mu dauka ba, babu yadda za mu yi nasara cikin wannan yaki; wannan […]
Takobin Ruhu – Wato Maganar Allah:
“Ku dauki kwalkwali na ceto kuma da Takobin Ruhu, wato Maganar Allah.” (Afisawa:6:17).
Yau za mu ci gaba ne da nazarin da muke yi game da yaki na Ruhaniyya. daya daga cikin muhimman makamai da idan ba mu dauka ba, babu yadda za mu yi nasara cikin wannan yaki; wannan kuwa shi ne takobin Ruhu: ko kuwa Maganar Allah. A cikin dukan kayan yakin da muka riga muka yi bincike a kansu, mun gan cewa dukan wadancan makamai na kariya ne kawai, da takobi ne kawai za mu iya kai wa Shaidan farmaki. Idan har ka iya ka rataya dukan sauran makamai amma ba ka dauki takobin Ruhu ba, to a gaskiya cin nasara zai yi wuya sosai, domin ba ka da makamin da za ka iya fuskantar Shaidan da shi. Maganar Allah ne kawai muke iya kai wa Shaidan farmaki da ita. A cikin Littafin Ibraniyawa 4:12–13, maganar na cewa “Gama maganar Allah mai rai ce, mai aikatawa, ta fi kowane takobi mai kaifi biyu ci, tana kuwa hudawa har zuwa rarrabar rai da ruhu, da gababuwa da bargo kuma, tana kuwa da hanzari ga ganewar tunanin zuciya da nufe-nufenta. Babu wani abu mai rai kuma da ba a bayyane a gabansa ba: amma abubuwa duka a tsiraice suke, budaddu kuma gaban idanun wannan wanda muke gare shi.” Maganar Allah babbar makami ce ga kowane mai bin Yesu Kiristi, ta yaya ne mutum zai iya yin amfani da wannan takobi har ya kai ga cin nasara bisa Shaidan da kuma dukan ayyukansa?. Bari mu ga yadda Yesu Kiristi ya yi amfani da wannan takobi a cikin Littafin Matta 4:1–11, maganar Allah na koya mana cewa, “Sa’annan Ruhu ya tafi da Yesu cikin jeji domin Shaidan shi yi masa jarraba. Sa’anda ya yi azumi yini arba’in da kwana arba’in, daga baya ya ji yunwa. Sai mai jarraba ya zo ya ce masa: Idan kai dan Allah ne, ka umurci wadannan duwatsu su zama gurasa. Amma ya amsa ya ce, An rubuta, ba da abinci kadai ba mutum za ya rayu, amma da kowace magana da ke fitowa daga bakin Allah, Sa’annan Shaidan ya dauke shi zuwa cikin birni mai tsarki; ya tsayar da da shi a kan husumiya ta haikali, ya ce masa, idan kai dan Allah ne, fada da kanka: gama an rubuta, Za ya ba mala’ikunsa umurni a kanka, a bisa hannuwansu za su dauke ka kada alama ka buga kafarka bisa dutse. Yesu ya ce masa, An kuma rubuta, ba za ka gwada Ubangiji Allahnka ba. Kuma Shaidan ya tafi da shi cikin wani dutse mai tsawo kwarai, ya gwada masa dukan mulukokin duniya, da daukakarsu; ya ce masa, dukan wadannan na ba ka, idan ka fadi ka yi mani sujada. Sa’annan Yesu ya ce masa, rabu da nan, ya Shaidan: gama an rubuta, ka yi sujada ga Ubangiji Allahnka, Shi kadai ma za ka bauta maSa, Sa’annan Shaidan ya rabu da shi; ga mala’iku kuma suka zo, suka yi masa hidima.”
Abu na farko da dole mu gane a matsayinmu na masu ba da gaskiya ga Yesu Kiristi shi ne, idan har Ubangijinmu Yesu Kiristi ya fuskanci irin wannan kalubale daga wurin Shaidan magabci, to babu shakka dukan mabiyansa za su fuskanci irin wadannan jarrabobin, sai mu zama a shirye a koyaushe domin mu iya cin nasara bisa dabarun Shaidan. Shi magabcin, ya zo wurin Yesu da jarrabawa ko mu ce hari; a daidai lokacin da yake da bukata, Yesu Kiristi ya gama azumi ke nan na kwanaki arba’in, domin wannan yana jin yunwa. Shaidan da ya gane haka sai ya zo wurinsa da wannan gwajin, na cewa idan shi Yesu Kiristi dan Allah ne, bai kamata ya yi ta jin yunwa ba, ai yana da iko ya maida duwatsu su zama gurasa ya ci, wannan hila ce ta mugunta daga wurin Shaidan; Yesu ya gane abin da yake nufi sai ya yi amfani da Takobin da ke hannunsa – ya ce wa Shaidan An Rubuta. Abu guda da ya kamata mu sani, shi ne abin da maganar Allah ta ce game da kowane bukata ko damuwa, ko jarrabawa ko lalurin da muka samu kanmu a ciki. Sanin maganar Allah cikin zuciyarmu ne tushen cin nasarar kowane mai bin Yesu Kiristi. Yesu ya ce wa Shaidan, ba da abinci kadai mutum ke rayuwa ba; amma da kowace magana da ta fito daga bakin Allah. Cin nasararmu bisa Shaidan zai danganta ne da yadda muka iya furta Maganar Allah a daidai lokacin da ya kawo mana hari. A cikin dukan jarabobin da Shaidan ya kawo wa Yesu, kalma guda da muka ji ya yi ta maimaitawa ita ce An Rubuta, An Rubuta…. Haka idan muna so mu iya kada Shaidan, ya zama dole mu zama masu nazari a cikin Littafi Mai tsarki, mu gane ko mene ne maganar Allah ke fadi, mu kuma yi mata biyayya.
A inda muka yi karatu dazu cikin wannan koyarwa, a Littafin Ibraniyawa 4: 12; maganar Allah na koya mana cewa – ‘gama maganar Allah mai rai ce, mai aikatawa, ta fi kowane takobi mai kaifi biyu ci; tana kuwa hudawa har zuwa rarraban rai da ruhu da gababuwa da bargo kuma, tana kuwa da hanzari ga ganewar tunanin zuciya da nufe-nufenta.’
To ashe babu inda maganar Allah ba za ta iya shiga ba, Maganar Allah tana iya hudawa tsakanin rai da ruhu, tsakanin gababuwa da bargo; tana iya gane ko mene ne ke tafe cikin zuciyar mutum da dukan nufin da ke ciki. Wannan ne ya sa idan Shaidan ya kawo mana farmaki, sai mu yi amfani da maganar Allah a lokacin, ba zai iya yin gaba da maganar Allah ba ko kadan. Akwai abu guda mai muhimmanci da dole kowane mai bin Yesu Kiristi ya kamata ya gane: sanin Maganar Allah a cikin zuciyarmu daban yake da haddace Maganar Allah a kanmu. Dukan Maganar Allah da mutum ya hadace ne kawai amma bai yi mata biyayya ba, ba shi da amfani ko kadan, ba za ka iya yin yaki da ita ba lokacin da kake bukata, domin ba rai ba ne a cikinka. Amma dukan Maganar Allah da ka haddace, ka kuma yi nazari a kai, ka yi mata biyayya, za ta zauna cikin zuciyarka, kuma ita ce za ta zama sanadin cin nasararka bisa Shaidan; domin ka bar wannan Maganar Allah ta zama Rai a cikinka kamar yadda Littafi Mai tsarki ya fadi.
Sai mu tuna cewa wannan yaki ya soma farawa daga cikin zuciyarmu ne “Gama koda muna tafiya cikin jiki, ba mu yi yaki bisa ga jiki ba, gama makaman yakinmu ba na jini ba ne, amma masu iko ne gaban Allah da za su rushe wurare masu karfi; muna rushe zace-zace da kowane madaukakin abu wanda ya daukaka gaba da sanin Allah, muna komo da kowane tunani cikin bauta ga biyayyar Kiristi.” (2Korin.10:3-5). Hanya guda da Shaidan yakan yi amfani da ita sosai ita ce shiga cikin tunanin mutum, ya ba shi shawarar da zai yi gaba da umarnin Allah.
Mu ci gaba da yin addu’a domin wannan kasa Allah Ubangijinmu Ya kawo mana zaman lafiya a tsakaninmu. Allah Ya taimake mu, amin.