Yakin aiki: Ba gudu ba ja da baya —Kungiyoyin Kwadago

Mambobin gamayyar kungiyoyin Ƙwadago ta Najeriya sun sake jaddada cewa ba za su ci gaba da lamuntar jan kafa wurin tabbatar da mafi ƙarancin albashi ba nan da ranar 31 ga watan Mayu. Sun bayyana wannan matsaya ne a karshen taron Majalisar Zartaswan kungiyoyin na Kasa (NEC). Wannan itace matsayar  kungiyar kwadago ta Najeriya NLC […]

Yakin aiki: Ba gudu ba ja da baya —Kungiyoyin Kwadago

ƙungiyoyin ƙwadago

Mambobin gamayyar kungiyoyin Ƙwadago ta Najeriya sun sake jaddada cewa ba za su ci gaba da lamuntar jan kafa wurin tabbatar da mafi ƙarancin albashi ba nan da ranar 31 ga watan Mayu.

Sun bayyana wannan matsaya ne a karshen taron Majalisar Zartaswan kungiyoyin na Kasa (NEC).

Wannan itace matsayar  kungiyar kwadago ta Najeriya NLC da kuma kungiyar sana’o’i (TUC) a ranar Litinin.

Shugaban NLC Joe Ajaero da takwaranasa TUC, Festus Osifo, sun bayyana hakan ne a lokacin da suke karanta matsayar da suka cimma a taron ga manema labarai a Abuja.

Sun ce, sun  yi nazari sosai kan lamarin tare da yin la’akari kan hakikanin abin da ke faruwa a halin yanzu da kuma yadda ya shafi ma’aikata da talakawan Najeriya.

Sun bayyana cewa  “Muna bukatar albashin da zai iya rike ma’aikatan Najeriya lura da gudummawar da suke bayarwa ga cigaban kasar.

“Kungiyar kwadagon ta umurci dukkan shugabanninta na jihohin da har yanzu gwamnatocin jahohinsu ba su  aiwatar da mafi karancin albashi na N30,000 da kuma gyare-gyaren da suka biyo baya ba da su ba da wa’adin mako biyu ga gwamnatocin jihohin.

“Idan ba haka ba, a janye ayyuka a ma’aikatu da masana’antu.

Kungiyar kwadago ta baiwa Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Kasa (NERC) da Gwamnatin Tarayya wa’adin ranar 31 ga Mayu ta janye karin kuɗin wutar lantarki da ta yi.

Kungiyar kwadagon ta bukaci gwamnati da ta ba da fifiko wajen warware matsalolin domin samun zaman lafiya a ma’aikatu.

Ta yi kira ga dukkan kungiyoyi masu alaka, da kungiyoyin fararen hula a fadin Najeriya da su kasance cikin hadin kai da tsayin daka a cikin wannan mawuyacin hali da ƙasar ke ciki.

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta