Yakin cacar-baki tsakanin APC da PDP ya dauki sabon salo
A ci gaba da sukar juna ta hanyar yin kalamai masu zafi tsakanin jam’iyyar PDP mai mulki da jam’iyyar adawa ta APC, a cikin makon da muke ciki yakin cacar bakin da jam’iyyun suke yi ya sauya salo. Aminiya ta gano cewa a farkon makon nan jam’iyyar PDP ta zargi ’yan adawa da shirya manakisar […]
A ci gaba da sukar juna ta hanyar yin kalamai masu zafi tsakanin jam’iyyar PDP mai mulki da jam’iyyar adawa ta APC, a cikin makon da muke ciki yakin cacar bakin da jam’iyyun suke yi ya sauya salo.
Aminiya ta gano cewa a farkon makon nan jam’iyyar PDP ta zargi ’yan adawa da shirya manakisar matsalar mai a Najeriya ta hanyar hada baki da wasu manyan ’yan kasuwar mai su dakatar da aika mai gidajen man kasar.
Shugaban jam’iyyar PDP Adamu Mu’azu da daraktan yada labarai na kungiyar kamfe din shugaban kasa Fani Kayode sun fito karara sun ce ’yan adawa na da hannu dumu-dumu a karancin man da ake fama da shi a sassa da dama na kasar.
Sai dai ’yan adawar ba su yi wata-wata ba wajen mayar da martani inda suka dora alhakin a kan gwamnatin PDP mai mulki.
Sun bayyana cewar matsalar man na nuna kasawar gwamnatin PDP mai mulkin kasar.
Ana cikin haka kwatsam sai shugaban Jonathan ya ce ba zai taba bai wa ’yan adawa dama su mulki kasar nan ba.
Shugaba Jonathan ya yi furucin ne yayin da ya yi taro da shugabanni da ’yan takarar jam’iyyar a fadarsa da ke Abuja a ranar Litinin din da ta gaba.
Ya ce ya fadi haka ne saboda irin bakar adawar da ’yan adawa suke yi das hi ta hanyar nuna masa kiyayya mai zafi saboda haushin da suke ji na kasa samun ragamar mulkin kasar nan.
Shi ma jigo a cikin jam’iyyar APC Bola Tunubu ya mayar da martani kan zargin da jam’iyyar PDP ta yi masa na neman zama shugaban kasa ta bayan gida.
Bola Tinubu ya bayyana a wata sanarwa da ya sanyawa hannu cewa idan yana son zama shugaban kasa ba sai ya bi ta bayan gida ba.
‘Idan ina son zama shugaban kasa zan bi ta kofar gida ne ba ta bayan gida ba. Shi ya sa na goyawa wasu baya suka shiga ta kofar gida kuma zancen da kuke yi a kan Osingbajo har yanzu shi ne mataimakin dan takararmu Janar Buhari. Ina da tabbacin cewa jam’iyyar mu za ta kayar da jam’iyyar PDP a zabe mai zuwa’. Inji shi.