Yakin Gaza: Tinubu ya bukaci a gaggauta tsagaita wuta

Tinubu ya yi kiran ne a birnin Riyadh na kasar Saudiyya

Yakin Gaza: Tinubu ya bukaci a gaggauta tsagaita wuta

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya yi kira da a gaggauta tsagaita wuta a yakin da Isra’ila take gwabzawa da Falasdinawa a Zirin Gaza.

Ya bayyana hakan ne ranar Juma’a yayin da yake magana a taron Saudiyya da kasashen Afirka a Riyadh, babban birnin kasar.

Da yake magana a kan taron kuma, Shugaba Tinubu ya ba masu sha’awar zuba jari da cewa Najeriya waje ne mai albarka da ba za su yi da-na-sanu ba muddin suka yi hakan.

Ya kuma bukaci a ruɓanya alaka da Saudiyya domin shawo kan matsalar Boko Haram da ISWAP da ma ta sauran kungiyoyi masu tsauraran ra’ayoyi da suka addabi yankin Tafkin Chadi da na Sahel.

Tinubu, kamar yadda wata sanarwar da Kakakinsa, Ajuri Ngelale ya fitar ranar Juma’a, ya ce, “Najeriya da Saudiyya sun jima suna hulda da juna a matakai daban-daban.

“A cikin shekaru 60 da suka gabata, alakarmu, wacce a baya ta tsaya a kan iya aikin Hajji, yanzu ta faɗaɗa ta kunshi bangarori masu yawa.

“Abin farin cikin yanzu shi ne ƙaruwar ’yan kasarmu a ɓangarorin lafiya da kwallon kafa da dai sauransu.

“Najeriya, kamar Saudiyya, tana aikin fadada tattalin arzikinta don ya tashi daga mai dogaro da man fetur zalla domin a samu ci gaba. Gwamnatina ta dauki wani mataki mai matukar wahala na cire kudaden ta ake tabargazarsu wajen biyan tallafin man fetur da kuma daidaita farashin canjin kudaden kasashen waje da sauran manufofin da za su dada saukaka kasuwanci a Najeriya,” in ji sanarwar.

Tinubu ya kuma gode wa gwamnatin Saudiyya saboda bayar da ayyukan jinkai a Najeriya ta hannun Gidauniyar Bayar da Tallafi ta Sarki Salman.

DSS ta gurfanar da Mahdi Shehu kan zargin ta’addanci

Sojoji sun kashe mataimakin Bello Turji

Harin ’Yan Fashi: Buni ya jajanta wa ’yan kasuwar Ngalda

An saki matar Ekweremadu daga gidan yari a Birtaniya, ta dawo Najeriya