Yakin Rasha da Ukraine ba namu ba ne —NATO

Stoltenberg ya yi kashedin cewa al’amura na iya rincabewa fiye da yadda ake gani.

Yakin Rasha da Ukraine ba namu ba ne —NATO

Babban Sakataren NATO, Jens Stoltenberg

Babban Sakataren Kungiyar  Kawancen Tsaro ta NATO, Jens Stoltenberg ya ce kungiyar ba za ta kakaba dokar hana zirga zirgar jiragen sama a sararin samaniyar Ukraine ba.

NATO ta bayyana hakan ne biyo bayan kiraye kirayen da mahukuntar kasar ke yi na taimakawa wajen taka wa Rasha birki a kan luguden wuta da take yi a kan kasar.

A yayin wani  taron gaggawa na ministocin harkokin waje na kasashen NATO, Stoltenberg ya ce  hanya daya tilo da za  a bi wajen aiwatar da dokar hana zirga zirgar jiragen sama a Ukraine ita ce ta harbo jiragen saman Rasha, kuma yin haka zai kai ga babban yaki a Turai, wanda zai shafi kasashe da dama.

Stoltenberg ya yi kashedin cewa al’amura na iya rincabewa fiye da yadda ake gani a yanzu a  kwanaki masu zuwa, inda za a samu karin asarar rai da wahalhalu da barnace barnace, duba da yadda Rasha ke shigowa da manyan makamai tare da ci gaba da hare hare a fadin kasar.

NATO, wadda ta ce wannan yaki ba nata bane, ta dau wannan mataki ne duk da magiyar da  shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ke yi ta a taimaka masa wajen dakatar da luguden wutar da Rasha ke yi a biranen  kasarsa.

Gidan Rediyon Faransa ya ruwaito Ministan Harkokin Wajen Ukraine Dmytro Kuleba yana gabatar da jawabi ga taron ta kafar bidiyo, inda ya mika bukatar daukar mataki kafin a makara, yana mai cewa a shirye suke su kare kansu, amma suna neman taimako.