Yakin Rasha da Ukraine zai haifar da yunwa a duniya –MDD
Majalisar ta yi hasashen samun karancin abinci a wasu kasashen duniya
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya yi gargadin cewa yakin da Rasha ke yi a Ukraine na iya haifar da mummunar yunwa da kuma karancin abinci a fadin duniya.
Ya ce, yawancin kasashen Afirka da kuma kasashe matalauta sun dogara kacokam a kan alkamar da Rasha da Ukraine ke samarwa.
- NAJERIYA A YAU: Gaskiyar Inda Mai Mala Buni Yake A Yanzu
- Coronavirus: An janye dokar sanya takunkumi a Faransa
Ya ce, “Abinci da man fetur da kuma takin zamani duk farashinsu ya yi tashin gwauron zabo, sannan karancin kudade da kuma jinkiri wajen shigar da kaya ko fitar da su duk matsala ce.”
Ya ce duk wadannan ka iya jefa kasashe marasa karfi cikin garari.
Kasashen, a cewarsa sun hada da Burkina Faso da Somaliya da Yemen, wadanda tuni suke fadi-tashin yadda za su ciyar da al’ummarsu.
Mista Guterres, ya yi kiran da a gaggauta tsagaita wuta domin guje wa fadawa matsalar karancin abinci a duniya.
Tuni masana suka yi hasashen samun karacin kayan abinci da kuma tsadar kayan masarufi, wanda tuni a wasu kasashen kayan suka yi tashin gwauron-zabi.