Yakin Sudan: Karin ’yan Najeriya 130 sun dawo gida

Karin ’yan Najeriya 130 daga cikin wadanda suka makale baan barkewar yaki a kasar Sudan sun sauka a Abuja a yammacin ranar Juma’a.

Yakin Sudan: Karin ’yan Najeriya 130 sun dawo gida

Karin ’yan Najeriya 130 daga cikin wadanda suka makale bayan barkewar yaki a kasar Sudan sun sauka a Abuja a yammacin ranar Juma’a.

Sun dawo gida ne a daidai lokacin da kasar Masar ta tisa keyar wasa ’yan Najeriya kimanin 500 zuwa Sudan, bayan sun tsallaka zuwa cikin kasarta neman tsira.

Masar ta dauki matakin ne bayan da wasu daga cikin ’yan Najeriyar da aka kwashe daga Khartoum, babban kasar Sudan, zuwa kasar Masar suka lakada wa jami’an tsaronta duka.

’Yan Najeriyar da ake zargi sun yi wannan danyen aiki ne bayan takaddamar da ta barke tsakaninsu da jami’an tsaron Masar filin jirgi.

Najeriya dai na ya kokwarin kwaso ’yan kasar da suka makale a Sudan daga filin jirgi a kasar Masar da kuma Sudan din.

A safiyar Juma’a Aminiya ta ruwaito cewa wadanda suke Port Sudan ma shirin hawa jirgi domin dawowa gida, inda aka ba wa mata fifiko wajen shiga jirgin.

Aminiya ta ruwaito yadda hukumomin Masar suka hana ’yan Najeriya shiga kasar, bayan sun tsere daga kasar Sudan.

Sai da ’yan Najeriyan da suka hada da mata da kananan yara da kuma dalibai suka shafe kwana hudu a kan iyakar kasar Masar kafin ta ba su izinin shiga.