Yakubu Kumo ya kara mata ta biyu

A ranar Asabar da misalin karfe 11 na safe aka daura auren fitaccen marubucin fina-finan Hausa Yakubu Modibbo Kumo da amaryarsa Khadija Abdallah a Islamiyyar Darul Arkam da ke Titin PDP a garin Gombe a kan sadaki Naira dubu 30.Khadijah ita ce matar marubucin ta biyu bayan uwargidansa Ummuaimana.Bayan an daura auren ne sai aka […]

Yakubu Kumo ya kara mata ta biyu
Yakubu Kumo ya kara mata ta biyu

A ranar Asabar da misalin karfe 11 na safe aka daura auren fitaccen marubucin fina-finan Hausa Yakubu Modibbo Kumo da amaryarsa Khadija Abdallah a Islamiyyar Darul Arkam da ke Titin PDP a garin Gombe a kan sadaki Naira dubu 30.
Khadijah ita ce matar marubucin ta biyu bayan uwargidansa Ummuaimana.
Bayan an daura auren ne sai aka dunguma zuwa dakin taro na Doma Foundation, inda aka ci aka sha, sannan aka ba ango shawarwari.
Marubucin ya bukaci mutane su yi masa addu’ar zaman lafiya a gidansa da kuma addu’ar Allah Ya ba shi ikon yin adalci tsakaninsa matansa.
A cikin ’yan fim da suka halarci daurin auren akwai fitaccen dillalin fina-finan Hausa Alhaji Sani Abubakar Rambo da marubuci Ibrahim Birniwa da furodusoshi da suka hada da Abdul Amart da Usman Mu’azu da Yusuf dan kundalo da Mukhtari Young Boy da sauransu.
Marubucin yana da ’ya’ya uku da suka hada da Aiman da Mahmood da kuma Basma.