Yalwatacciyar wutar lantarki za ta farfado da masana’antu – Shugaban Matasa
Alhaji Zakari Tijjani Fagge, wanda aka fi sani da (shugaban matasa) shi ne shugaban kamfanin sayar da injunan sarrafa kayan amfanin gona da gyara su da ke Kano, ya ce idan aka samu wadatacciyar wutar lantarki masana’antun kasar nan za su koma aiki, kuma tattalin arzikin kasa zai inganta sannan za a samar da karin […]

Alhaji Zakari Tijjani Fagge, wanda aka fi sani da (shugaban matasa) shi ne shugaban kamfanin sayar da injunan sarrafa kayan amfanin gona da gyara su da ke Kano, ya ce idan aka samu wadatacciyar wutar lantarki masana’antun kasar nan za su koma aiki, kuma tattalin arzikin kasa zai inganta sannan za a samar da karin hanyoyin dogaro da kai, domin rage zaman rashin aikin yi. Ya yi wannan bayani ne cikin zantawar su da wakilin mu, ga kuma yadda hirar ta gudana:
Aminiya: A matsayin ka na daya daga cikin masu sayar da injunan sarrafa kayan amfanin gona, ta yaya kuke gudanar da kasuwancinku?
Shugaba: Muna wannan kasuwanci ne ta hanyoyi da yawa, kuma mun shafe shekaru fiye da ashirin cikin harkokin saye da sayar da injuna da kuma gyaran su. Sai dai gaskiya akwai babban kalubale da muke fuskanta kan wannan kasuwanci namu na rashin ingantacciyar wutar lantarki a wannan kasa tamu.
Idan aka wadata kasa da wutar lantarki mai karfi ko shakka babu harkokin kasuwanci za su bunkasa, domin za a sake bubbude masana’antu da kamfanoni, wadanda suka dade a rufe, sannan tattalin arzikin kasa zai inganta kana za a samu karin guraben ayyukan dogaro da kai a kowane sako da lungu na wannan kasa tamu.
Muna yin kira ga gwamnatin tarayya da ta kara samar da wutar lantarki mai karfi, domin yanzu zamani ya canza kusan komai sai an hada shi a wutar lantarki, domin gudanar da ayyukansa kamar dai yadda muke gani a sauran kasashen da suka ci gaba ta fuskar masana’antu da kamfanoni.
Aminiya: Wasu jihohin suna kokarin samar da karin wutar lantarki a jihohinsu, kana ganin wannan shirin zai gamsar da masana’antu da kamfanoni ke nan?
Shugaba: Babu shakka wannan kokari da jihohi ke yi yana da amfani kwarai da gaske, amma yana da kyau a tsaya a tabbatar shirin samar da wutar lantarkin yana tafiya cikin sauri, domin an sha cewa za a yi hakan sai daga bisani a ji shiru babu maganar. Zai yi kyau a yi wani tsari tsakanin masu zuba jari da gwamnatoci domin cimma nasarar wannan kuduri na samar da wutar lantarki mai yalwa a kasar nan, domin bunkasa tattalin arziki da farfado da masana’antu da kamfanoni kamar yadda na bayyana a baya.
Idan da wuta mai karfi kusan daikacin masana’antun da suka durkushe za su tashi kuma za a samu ci gaba ta fuskar kasuwanci da cinikayyar kayayyaki, wadanda ake sarrafawa da na’urori masu aiki da wutar lantarki. Yana da kyau a cire siyasa wajen samar da wutar lantarki mai karfi, sannan a tsaya a yi abin da gaske, domin ganin al’umma sun samu wadatuwa da ita, kamar yadda take a sauran kasashen duniya da muke zuwa.
Amniya: Ana korafin cewa masu amfani da wutar lantarki ba sa biyan kudin wuta. Me za ka ce dangane da wannan batu?
Shugaba: Gaskiya ne cewa ana samun tirjiya wajen biyan kudin wuta da na ruwa da sauran abubuwa na more rayuwa, amma akwai bambanci tsakanin masu amfani da wuta daidaiku da kamfanoni ko masana’antu. Kamfanoni za su iya biyan wutarsu a kan ka’ida domin sai da ita suke aikinsu a kowace rana.
Sannan ina ganin cewa idan har wutar za ta wadata kowa zai biya, ta yadda za a iya bullo da hanyar yin amfani da kati a gidaje, wanda idan kana da kati to za ka samu wuta idan babu sai ka sabunta katinka, kamar dai yadda ake amfani da wayar hannu wadda idan babu kudi a kan layi to babu kira. Amma babbar matsalar mu ita ce rashin wuta wadatacciya.
Aminiya: Wadanne irin injuna kuke sayarwa, kuma wane aiki suke yi na sarrafa kayan amfain gona?
Shugaba: Muna sayar da injunan gyaran shinkafa, wadanda idan muka gyara maka shinkafa za ka dauka daga waje take; da injin casar masara da dawa da gero, kana akwai na ban ruwa a fadamu da injunan shuka da feshi da dai sauran ayyuka, wadanda ake yi da injuna. Kuma injunan suna iya gyara shinkafa har fiye da buhu 200 a rana guda. Haka kuma muna da dangantakar kasuwanci da kamfanoni da gwamnatoci, kana muna sayar da kayanmu a kasashe kamar su Kamaru da Nijar da Mali da Chadi da Burkina Fasso da sauran kasashe makwata.
Sannan yanzu haka shiri ya yi nisa za mu kai manyan injunan gyaran shinkafa a jihohi bakwai , inda muke kokarin fara wani shiri da gwamnatin Kano domin fara ba da horo ga matasa fiye da dari 500, wadanda za ta bai wa tallafi kan bunkasa noma dadi da wasu muhimman ayyuka da suka shafi noma, wanda idan da a ce akwai wuta wadatacciya al’amura za su kara bunkasa.
Aminiya: Wane shiri kuke da shi domin ganin ta hanyar kamfaninku an cimma nasarar bunkasa sarrafa kayan amfanin gona a wanna kasa?
Shugaba: Akwai tsare-tsare da muke da su domin fadada amfani da injuna sosai wajen aikin gona da sarrafa kayan amfanin gonar da kuma ajiye shi ya dade bai lalace ba. Amma fa sai an hada hannu wajen gyara wutar lantarki, domin cimma wannan manufa kuma na tabbata suma masu masana’an tu suna son ganin wuta ta samu. Sannan muna ba da horo kan sarrafa injuna da gyaransu tun da muna da kwararrun injiniyoyi.