YAMTARAWALA: Waken da ya ja hankali a taron Kungiyar Gizago na 2019

A ranar Asabar 17-04-1441 (Bayan Hijira), daidai da 14-12-2019 (Miladiyya) Gizagawan Najeriya suka hallara a zauren taro na Sultan Sa’ad Abubakar da ke Kwalejin Barewa, Zariya, Jihar Kaduna, inda suka gudanar da taronsu na shekara, wanda shi ne karo na 6 tun kafuwar kungiyar. Daya daga cikin harkokin da suka gabatar, har da karance-karancen wakokin […]

YAMTARAWALA: Waken da ya ja hankali a taron Kungiyar Gizago na 2019

Daga hagu, Dokta Bukar Usman ne yake musabaha da Alhaji Ahmadu Giyaxe, sai Dokta Abdullahi Shehu a tsakiya, yayin kaddamar da wani littafi a shekarun baya

A ranar Asabar 17-04-1441 (Bayan Hijira), daidai da 14-12-2019 (Miladiyya) Gizagawan Najeriya suka hallara a zauren taro na Sultan Sa’ad Abubakar da ke Kwalejin Barewa, Zariya, Jihar Kaduna, inda suka gudanar da taronsu na shekara, wanda shi ne karo na 6 tun kafuwar kungiyar. Daya daga cikin harkokin da suka gabatar, har da karance-karancen wakokin fasaha, inda GIZAGO, Bashir Yahuza Malumfashi (08065576011) ya karanto tare da rera wakoki uku daga littafin marigayi Mahmoon Baba Ahmad, masu taken: ‘Lokaci’ da ‘Rayuwa’ da ‘Mutuwa.’ Daga bisani kuma ya rera wake mai taken Yamtarawala, wanda ya rubuta musamman domin yabo da jinjina ga dan kishin kasa kuma daya daga cikin jigogin da ke tallafa wa Kungiyar Gizagon Najeriya, wato Dokta Bukar Usman. Ganin yadda waken ya dauki hankalin mahalarta taron ya sa za mu kawo shi a nan, kamar haka:  

Amshi:

Dan Najeriya,

Mai kishin kasa,

Bukar Yamtarawalar zamani.

Allahu Sarki, Shi ne Zamani,

Mai juya komai ba razani,

Mai jure wauta har yai lamuni.

 

Muhammadu Manzo jigon alheri,

Mijin su Khadija mahanin sharri,

Jagoran shiriya a kowane zamani.

 

Ya ku jama’a ku zo ku ji ni,

Za ni ziyara sai ku biyo ni,

Bagiren Yamtarawalar zamani.

 

Ba ka jin rugum sai da dalili,

In ka ji guda babu jidali,

Mu zamto nazari mu feke tunani.

 

Ranar 10 yaz zo gwanin ta’ajibi,

A watan sha biyu mai nasibi,

Nineteen Fourty Two shekarar zamani.

 

Kings’ Kwaleji batun ilimi ne,

Ya yi da gaske mai kwazo ne,

Dan Usmanu yai ilimin zamani.

 

Ya yi karatu ya kara karatu,

Tsangayar ABU ya gwagwatu,

Ya zama Dokta tun can zamani.

 

Yamta na dauri ya ciri tuta,

Ya sha da maza har sun kuta,

Ya ’yanta Biu ba mai razani.

 

Bukar Namiji ya dau gado,

Da alkalaminsa ya sauka gado,

Ya ’yanta kasa Yamtarawalar zamani.

 

Jure fari yau sai dai tofa,

Garnakaki ne murfin karfe,

Ya dasa rassa a dukkan zamani.

 

Ya bauci kasa ba gajiyawa,

Ya buga aiki ba amajawa,

Ya kare kasa zahiri-badini.

 

A fagen wallafa ba ya da wasa,

Tun da ya fara ba ya fasa,

Alkalaminsa ya fi gaban tamani.

 

A fagen adabinmu fanni-fanni,

Hausa-Ingilishi duk yai journey,

Har Ajaminmu yau ba badini.

 

Dole ne mu kira shi Gatan Adabi,

Ya tsare al’ada babu takobi,

Ko jiya ko yau da dukkan zamani.

 

Ga Hatching Hopes tarihinsa,

Ta Zo Mu Ji Ta daga taskarsa,

Tarihin Biu a dukkan zamani.

 

Aikin Ofis Bukar ya rattaba,

Littafinsa ciki ba tababa,

Ya tanada su don ’yan zamani.

 

Ina ’yan siyasa ku zo kui karatu,

Ga littaffai nan ya yo rututu,

Ku dau iliminku ba batun tsanani.

 

Ga Gidauniya mai albarka,

Tana baza aiki sai san barka,

Ga al’umma sun dau sansani.

 

Taimakon gajiyayyu Bukar ya saba,

Tallafi na karatu ya ba da sawaba,

Dan kwarai mai himma da zurfin tunani.

 

Duk wani jan wuya a Najeriya,

A fadin duniya har Saberiya,

An san da zaman jigon zamani.

 

Bukar ya sam girma komai haiba,

Lambar OON ba tababa,

Doktan A.B.U. shaharar zamani.

 

Jakadan Adabi a Burkina Faso,

Daukaka a Nijar duk ku hasaso

Ya sam lambar adabi fanni.

 

Hali a mutum shi ne jarinsa,

Goron tanka ya wuce tsutsa,

Hadarin safe ka fi uba mai tsanani.

 

Ina mai cin kasa kiyayi ta shuri,

Wandon karfe sa maza kuri,

Dokta mai Allah Yamtarawalar zamani.

 

Duk kaudin wuta karshenta toka,

Mu kauce assha mu bar taba doka,

Inji dan kishin kasa Doktan Zamani.

 

Addu’a daga tushe Allah jikan su,

Baba Usman Hajiya Falmata ga su,

Iyayen daraja ga Yamtar zamani.

 

Muna tuna baya Kemi mun kewarta,

Mun yaba Dupe Madam don kwazonta,

Matan girma ga Doktan zamani.

 

’Ya’ya mata Mero adon gari,

Allah jikansu Fatima yau ba su gari,

’Ya’ya na kwarai ba guni-guni.

 

Ga Halimatu ’ya mai nagarta,

Nana Hadiza ba ta karanta,

Kun dau gadon Yamtar zamani.

 

Hafsat kina nan ki karo himma,

Auta shalele Zahrah ba kya hadama,

Allahu Ya kare sharrin zamani.

 

Hanyar lafiya a bi ta da shekara,

Dokta kai aiki a dukkan lamurra,

Kawiyyu Ya fisshe ka a dukkan zamani.

 

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos