’Yan ƙwadago sun soke tafiya yajin aiki

Kungiyar Ƙwadago ta shirya shiga yajin aikin sai baba ta gani a gobe Talata.

’Yan ƙwadago sun soke tafiya yajin aiki

Kungiyar Ƙwadago ta Kasa NLC da takwararta ta TUC sun jingine batun tafiya yajin aikin sai baba ta gani.

Aminiya ta ruwaito cewa wani jami’in kungiyar wanda ya halarci zaman da NLC ta gudanar a Babban Ofishinta yau Litinin ne ya tabbatar da hakan.

A ranar Lahadin da ta gabata ce Gwamnatin Tarayya ta yi wani zama na musamman da shugabannin kungiyar kwadago na kasar NLC da TUC, kan matakan da za a dauka na magance takaddamar da ta biyo bayan cire tallafin man fetur da ake ta takaddama a kai.

Su dai ’yan kwadagon sun shirya tafiya yajin aikin sai baba ta gani a wannan makon yayin da ake tsaka da bikin cikar kasar shekara 63 da samun ’yancin kai.

Sai dai yayin wani zama da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa Femi Gbajabiamila ya jagoranta tare da shugabannin kwadagon, an tattauna muhimman batutuwa don lalubo mafita.

Batutuwan da aka tattauna sun hadar da amincewa da karin albashin wucin gadi na Naira 35,000 ga ma’aikata, da kuma gaggauta samar da motoci masu amfani da gas don saukaka matsalolin sufuri, da cire tallafin man ya haifar.

Wani alkawari kuma da gwamnatin ta yi shi ne na samar da kudade ga kananan masana’antu, da kuma cire harajin VAT daga iskar gas tsawon watanni shida, da rabawa gidaje miliyan 15 tallafin Naira dubu saba’in da biyar a wata uku, ma’ana Naira dubu ashirin da biyar a kowanne wata.