’Yan ƙwallon Nijeriya da suka koma kasuwanci bayan jingine wasa

Bayan wasannin ƙwallon ƙafa masu matuƙar ƙayatarwa da nuna hazaƙa da suka yi a filin wasa, ya zuwa sauya sheƙa zuwa bazama cikin harkokin kasuwanci, wasu ’yan wasan da suka taka leda wa ƙungiyar ƙwallon ƙafar Nijeriya sun nuna wa duniya cewa ba a fagen ƙwallon ƙafa kawai suke da ƙwarewa ba, a’a har ma […]

’Yan ƙwallon Nijeriya da suka koma kasuwanci bayan jingine wasa

Bayan wasannin ƙwallon ƙafa masu matuƙar ƙayatarwa da nuna hazaƙa da suka yi a filin wasa, ya zuwa sauya sheƙa zuwa bazama cikin harkokin kasuwanci, wasu ’yan wasan da suka taka leda wa ƙungiyar ƙwallon ƙafar Nijeriya sun nuna wa duniya cewa ba a fagen ƙwallon ƙafa kawai suke da ƙwarewa ba, a’a har ma a harkar kasuwancin sun yi fice tamkar dai yadda suka yi zarra a fagen tamaula.

Waɗannan ’yan wasan sun zama manyan misalai na yadda ƙwararrun ’yan ƙwallo za su yi amfani da ƙwarewarsu da shahararsu da ma gogewarsu domin samun nasara a fagen kasuwanci.

Za mu kawo muku jerin wasu ’yan ƙwallon da suka taka wa ƙungiyar ƙwallon ƙafar Nijeriya leda, da suka rikiɗa zuwa harkokin kasuwanci daban-daban bayan sun yi adabo da wasan ƙwallon ƙafan.

Nwankwo Kanu

Kanu ƙwararren ɗan wasan ƙwallon ƙafan Nijeriya da sunansa ya yi shuhura sannan hamshaƙin ɗan kasuwa ne a yanzu. Shi ne ya mallaki Hardley Apartments, otal mai daraja ta 4 da ke unguwar nan ta attajirai wato Ɓictoria Island, a birnin Legas, kuma shi ne shugaban ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Enyimba. Har wa yau, Kanu jakadan kamfanin Simba TƁS, ne, wajen tallata ababen hawa kamar su babur mai ƙafa uku na TƁS King Tricycle da kuma Apache Power Bike. An kuma naɗa shi jakadan Sportsbet na duniya a 2022.

Bugu da ƙari, Kanu yana amfani da ƙwarewarsa a fagen tamaula wajen yin sharhi wa kafofin wasanni a faɗin duniya a matsayin masani a harkar tamaula.

Obafemi Martins

Obafemi Martins ya mallaki harkoki kasuwanci daban-daban da ke bunƙasa. Kafanoninsa sun haɗa da Cosa Nostra Patron, wani sanannen gidan rawa na dare a Legas da wani katafaren wurin haɗa tufafi a Amurka mai ɗauke alamar acrobatic. Waɗannan su ne harkokin

kasuwanci biyu da tsohon ɗan ya mallaka. Sannan, Obafemi Martins ya mallaki gidaje sama da 20 a manyan unguwannin birnin Legas. Har wa yau shi ne yake da Gidauniyar Obafemi Martins.

Jay-Jay Okocha

Ɗaya ne daga cikin fitattun ’yan wasan ƙwallon ƙafa a Nijeriya. Jay-Jay Okocha shi ne mai kamfanin TGBG Global Inɓestment Ltd., kamfanin da yake gudanar harkokin canji (Bureau de Change) da gidan abinci da wata mashaya da shigo

da kayayyakin masarufi kamar su barasa, sannan jakadan talle ne na kamfanin Kwik Deliɓery kuma mai sharhin ƙwallon ƙafa na Supersports.

John Mikel Obi

Harkokin kasuwancin Mikel Obi suna da rassa da dama tamkar yadda gogewarsa a fagen ƙwallon ƙafa ta kasance mai faɗi. Ya mallaki kamfanin sufuri tsakanin jihohin Nijeriya sannan shi ne mai tallan kamfanin caca na BetWinner Africa. A harkar yaɗa labarai ma ba a bar shi a baya ba, domin kuwa Mikel ɗin

yakan gabatar da shirin The Obi One Podcast, (rediyon intanet) inda yake sharhin wasanni da kasuwanci.

Duk da na ɗan taƙaitaccen lokacin da ya yi a kamfanin ƁISIONPRO SPORTS EUROPE LLP a 2011, gudummawar da ya bayar a kamfanin ya yi tasiri sosai a kamfanin ba da shawarwari a fagen wasanni.

Cikin yardar mai duka a mako mai zuwa, za mu kawo sauran ’yan wasan da suka shiga kasuwanci bayan jingine tamaula.