‘Yan ɗarikar Tijjaniya sun yi wa Sarki Sanusi II mubaya’a
Kimanin mambobin ƙungiyar 200 ne suka je fada domin nuna mubaya’arsu ga Sarkin.
Duk da cewar ana turka turkar kujerar Sarautar Kano al’umma daga ciki da wajen jihar na ci gaba da kai wa Mai martaba Sarki Muhammadu Sanusi II ziyara domin yi masa mubaya’a da nuna goyon bayansu gare shi.
Ƙungiyar Ɗarikar Tijjaniya ta Ƙasa reshen Jihar Kano, wato Majalisisshura na Ɗarikar Tijjaniya ƙarƙashin jagorancin Khalifa Sani Shehu Maihula ta kai makamanciyar wannan ziyarar ga Sarkin wanda shi ne shugabanta na ƙasa.
- An soma jigilar maniyyata 3,888 daga Sakkwato
- Daliban jami’a sun kashe abokinsu saboda wayar salula a Oyo
A jawabinsa, Sarki Muhammadu Sanusi II ya yaba wa shugabannin Ɗarikar Tijjaniya bisa yadda suka duƙufa wajen yin addu’o’in samun zaman lafiya a Jihar Kano da ma ƙasa baki ɗaya
Da yake jawabi a madadin shugaban Ɗarikar ta Tjjaniyya, mataimakin shugaban Sayyadi Bashir Tijjani Zangon Barebari ya ce sun zo fada ne domin gabatar da gaisuwa ta ban girma da kuma yi wa Sarki mubaya’a.
A cewarsa “mun zo fada ne domin mu yi wa Sarki murna tare da addu’ar Allah Ya riƙa masa.”
Ya yi fatan samun zanan lafiya a Jihar Kano da ƙasa gaba ɗaya.
“Zaman lafiya shi ne abu mafi muhimmanci. Domin duk wani abu ba zai samu ba idan ba zaman lafiya.”
Da yake bayani game da muhimmanci karɓar ƙaddara, Shehin Malamin ya bayyana cewa “Komai na duniya Allah ne ke yinsa.
“Ya kamata Bawa ya karɓi duk wani abu da Allah Ya hukunta domin duk hukuncin Allah kyakkyawa ne.”
Ya kuma yi kira ga al’ummar da su guji tayar da tarzoma inda ya ce, “idan aka sami tashin hankali to za a samu rashin zaman lafiya.
Ya ce, “shi kuma rashin zaman lafiya abu ne da zai shafi kowa domin ba zai sami wani ya ƙyale wani ba. Shi ya sa mu a kullum muke wa’azi akan zaman lafiya
Aminiya ta ruwaito cewa kimanin mambobin ƙungiyar 200 ne suka je fadar Sarkin domin nuna mubaya’arsu a gare shi.