’Yan acaba a Kaduna sun koka

Shekaranjiya Laraba dokar haramta sana’ar acaba ta soma aiki a Jihar Kaduna, bayan sanya wa dokar hannu da Gwamna Mukhtar Ramalan Yero ya yi makonni biyu da suka wuce.Aminiya ta lura cewa yanzu titunan garin Kaduna da Zariya sun kasance babu cinkoson ababen hawa saboda komawa garuruwansu da ’yan acaban suka yi domin kauce wa […]

’Yan acaba a Kaduna sun koka
’Yan acaba a Kaduna sun koka

Sakatare Musa Muhammed LitiShekaranjiya Laraba dokar haramta sana’ar acaba ta soma aiki a Jihar Kaduna, bayan sanya wa dokar hannu da Gwamna Mukhtar Ramalan Yero ya yi makonni biyu da suka wuce.
Aminiya ta lura cewa yanzu titunan garin Kaduna da Zariya sun kasance babu cinkoson ababen hawa saboda komawa garuruwansu da ’yan acaban suka yi domin kauce wa fushin gwamnati.
Wasu ’yan acaban da suka rage, wadanda Aminiya ta zanta da su, sun bayyana alhininsu ga dokar, amma sun sha alwashin bin ta sau-da-kafa.
A Kaduna, sakataren kungiyar ’yan acaba na Hayin Bello a Rigasa, Malam Musa Muhammed Liti ya bayyana cewa dokar ba  ta yi musu dadi ba, sai dai ita gwamnati abin da ta hango, “Mu talakawa ba mu hango ba, saboda haka babu abin da za mu ce sai dai mu yi fatan Allah Ya sada mu da abin da zai zame mana alheri.
“Kusan shekaru goma sha daya ke nan nake sana’ar acaba, amma tunda gwamnati ta saka dokar haramta shi, dole ne mu hakura, mu ga kuma abin da Allah zai yi, domin samu don ciyar da iyalanmu.
“Kiran da zan yi shi ne ga ’yan uwana ’yan acaba da ya kamata mu yi biyayya ga doka, Insha Allahu, muna sa ran alheri ya biyo baya. A yi hakuri a bi duk abin da gwamnati ta ce, domin kare mutunci,” inji shi.
Malam Abdullahi Sabon Gini Tela, shi cewa ya yi ita rayuwa duk yadda mutum ya tsinci kansa cikinta, sai ya yi hakuri, ya cije, domin babu abin da zai iya yi illah ya mika al’amuransa ga Allah. “Za mu bi wannan doka yadda ya kamata, amma abin da ya yi min dan tsauri a kai shi ne bai wuce kwanaki ashirin ba da sayen babur dina domin in rika kai yarana makaranta, tunda ba ni da kudin biyan mota, saboda yau da gobe, sai Allah.
“Hukuma za mu yi mata biyayya, amma ta dubi girman Allah ta dan sausauta a bari mu rika kai yara makaranta, sannan idan iyalanmu ba su da lafiya, su yarda a rika daukarsu a babur”, inji shi.
Shi kuma Malam Salisu Kano cewa ya yi haramta sana’ar ya shafi dukkan al’amuransa na rayuwa, domin kafin ya hau mota sau daya, ya hau babur sau goma, saboda yanayin aikinsa. “Hakika a yanzu ban san yaya zan yi ba, saboda akwai lungunan da Keke Napep ba za su iya shiga ba. Dole babur ne zai shiga kowane lungu ba tare da matsala ba, domin biya maka bukatarka. A halin da ake ciki a yanzu, ba ma ni kadai ba, jama’a za su shiga wani hali na damuwa.
“Kasantuwar Keke NAPEP din bai wadata yadda har zai isa mutane ba, gwamnatin ta yi gaggawan saka hannu a dokar, domin kamata ya yi kafin a haramta acabar sai KEKE NAPEP din sun wadata a cikin jihar,” inji shi.
A Zariya, wakilinmu ya tattauna da wanda yake mataimakin shugaban ’yan acaba a Kofar Doka, mai suna Malam Auwal Musa, wanda ya nuna alhininsa kan hana su gudanar da sana’arsu.
Ya ce, “Yau a kalla shekarata ishirin da biyu ina gudanar da wannan sana’ar.  Da kasuwanci nake, sai jarina ya karye, bashi ya fara hawa kaina, sai na fara wannan sana’a. Tsawon shekarun nan matana biyu, yarana goma sha shida hade da marayu kuma ba ni da wata sana’ar da ta wuce min acaba. Duk da na san cewar wasu baki sun shigo sun bata mana yanayin harkar, amma mu ita muka dogara da ita, muna samun rufin asiri, don haka bai kamata a ce, rana tsaka, a hana mu  gudanar da wannan sana’ar, ba tare da an musanya mana da wata ba”.
Malam Ali Mai maganin kwari, wanda ke zaune a kasuwar Sabon-Gari Zariya, bai ji dadin dokar ba. Ya ce, “’Yan acaba sun kasu kashi uku; akwai masu neman abinci tsakani da Allah; sannan akwai ’yan acaban; sannan  kuma akwai batagari, don haka maimakon a soke shi, sai a inganta shi, a tace su. Ka duba yau kadai da fara dokar an shiga matsala. Don haka ina kira ga gwamanati ta duba wannan lamarin ta gyara.