Yan Acaba sun yi zanga-zagar lumana a Legas

Gamayyar kungiyoyin da suka kira kansu wadanda suke kare hakkin dan Adam da kawayensu sun gudanar da zanga-zangar lumana don jawo hankalin gwamnan Jihar Legas, Akinwunmi Ambode ya soke wa’adin kwanaki 21 da ya ba ’yan acaba su daina bin wasu hanyoyi a jihar. Da yake jawabi a madadin gamayyar kungiyoyin yayin zanga-zangar a makon […]

Yan Acaba sun yi zanga-zagar lumana a Legas
Yan Acaba sun yi zanga-zagar lumana a Legas

Gamayyar kungiyoyin da suka kira kansu wadanda suke kare hakkin dan Adam da kawayensu sun gudanar da zanga-zangar lumana don jawo hankalin gwamnan Jihar Legas, Akinwunmi Ambode ya soke wa’adin kwanaki 21 da ya ba ’yan acaba su daina bin wasu hanyoyi a jihar.

Da yake jawabi a madadin gamayyar kungiyoyin yayin zanga-zangar a makon nan, Kwamared Declan Ikekaire ya bayyana cewa abin da gwamnatin jihar ta yi bai dace ba.
“Gaskiya abin da gwamnati ta yi bai kamata ba. Mutanenmu da suke yin haya da babura mutane ne masu bin doka da oda saboda haka ba sa bin manyan hanyoyi. Ayyukansu sun takaita ne a hanyoyin cikin gari. Saboda haka ba mu ga dalilin da za a hana mu neman halaliyarmu ba bisa doka da oda.” Inji shi.
Ya ci gaba da cewa, “Babu shakka Jihar Legas saboda cunkoson abubuwan hawa da na mutane da take da su tana bukatar dokokin tuki masu inganci amma kuma yana da muhimmanci idan za a yi irin wadannan dokoki a rika sara ana duban bakin gatari ta yadda ba za a tauye wa wasu hakkinsu ba.”
Shugaban ya bayyana cewa korafe-korafen da suke da shi sun hada da yadda jami’an tsaro suke yin amfani da dokokin da gwamnatin ta kafa suke tatsar kudi daga ’yan Najeriya, musamman ma masu haya da babura a jihar.
Ya kara da cewa, ya kamata gwamnati ta san cewa a yanzu baburan haya ne kadai damar da ta rage wa ’yan Najeriya wajen samun sufurin da suke amfani da shi don gudanar da harkokinsu na yau da kullum.
“Ta irin wadannan hanyoyin da aka hana bi ne masu baburan suke bi su isa gidan mai don sayen man da za su sanya a baburansu. Daga bisani sai jami’an tsaro su kama su hakazalika jami’an hukumar LASMA ma suna yin amfani da damar wajen gallaza wa masu baburan ta hanyar tatsar kudi a hannunsu amma kuma sai ka ga masu motocin tanka suna cin karensu ba babbaka ba tare da an musguna musu ba.” Inji shi.
Daga bisani sai ya yi kira ga majalisar dokokin jihar ta sake nazarin dokar don yi mata gyare-gyaren da suka dace.
A kwanannan ne gwamanatin Jihar Legas ta jaddada dokar da tsohuwar gwamnatin jihar ta kafa na hana masu baburan hawa wasu hanyoyi a jihar.
Gwamnan jihar Akinwumi Ambode ya ba masu baburan nan da kwanaki 21 su daina hawa hanyoyin ko kuma doka ta yi aiki a kansu.