’Yan adawa da matar Firayiministan Malesiya sun tsige gashinsu

Masu adawa da uwargidan Firayiministan Malesiya sun fara tsige gashin kansu, don nuna takaicinsu game da kalamanta na korafin tsadar gyaran gashi da dinkuna na kawa, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na AFP da jaridar Malaysian Insider suka ruwaito. Uwargigdan Shugaban kasar Malesiya na shan caccaka saboda korafin da ta yi game da yawan kiran […]

’Yan adawa da matar Firayiministan Malesiya sun tsige gashinsu
’Yan adawa da matar Firayiministan Malesiya sun tsige gashinsu

Masu adawa da uwargidan Firayiministan Malesiya sun fara tsige gashin kansu, don nuna takaicinsu game da kalamanta na korafin tsadar gyaran gashi da dinkuna na kawa, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na AFP da jaridar Malaysian Insider suka ruwaito.

Uwargigdan Shugaban kasar Malesiya na shan caccaka saboda korafin da ta yi game da yawan kiran wayar da take samu daga masu gyaran gashi da teloli. Uwargida Rosma Mansor, ’yar shekara 63, mace da ta saba haifar da rudani a kasar, kuma masu adawa da ita sun yi mata tabo da cewa ba ta yin wata hulda da talakawa, wadanda a kullum ke fafutikar neman abin biyan bukatun rayuwa.
Wannan mata ta Firayi minista Najib Razak ta nsai wa magabtanta wani babban makami a ranar Litinin din da ta gabata, inda ta koka kan cewa, tana kashe kudin ringgit dubu da 200 a wayar da take kiran masu zuwa gida su yi mata gyaran gashi; sannan tana kashe ringgit 500 don kiran telolinta. Wannan kudi da ta ke kashewa sun kai Naira Dubu 660 da kuma dubu 250, jimla dubu 910.
“Sai mun dinka kayan kawa don shiga taro, wadanda farashinsu ke da matukar tsada. Ga wadanda ke da hali ba wata matsala ba ce, amma me za a ce game da matan aure irin mu, wadanda ba su da hanyar samun kudin shiga?” a cewarta, kamar yadda jaridar Malaysian Insider ta ruwaito.
Mafi karancin albashi a Malesiya shi ne, Ringgit 900 a wata, kodayake ’yan adawa sun ce ba a cika tabbatar shi ba. Rosmah ta yi wannan Maganar ce a wajen tattaunawar al’umma game da sabon tsarin haraji, da ake sa ran fara amfani da shi cikin watan Afrilu.