‘Yan adawan Guinea sun bukaci a soke zaben kasar

A shekaranjiya Laraba ne ’Yan adawan kasar Guinea suka yi kira da a sake gudanar da zaben shugaban kasar da aka yi ranar Lahadin makon jiya, suna zargin an tabka magudi a wurare da dama a fadin kasar.Babban abokin hamayyar Shugaban kasar Alpha Conde, Cellou Dalein Diallo, ya ce mutane na da ikon yin zanga-zanga.Yana […]

‘Yan adawan Guinea sun bukaci a soke zaben kasar
‘Yan adawan Guinea sun bukaci a soke zaben kasar

A shekaranjiya Laraba ne ’Yan adawan kasar Guinea suka yi kira da a sake gudanar da zaben shugaban kasar da aka yi ranar Lahadin makon jiya, suna zargin an tabka magudi a wurare da dama a fadin kasar.
Babban abokin hamayyar Shugaban kasar Alpha Conde, Cellou Dalein Diallo, ya ce mutane na da ikon yin zanga-zanga.
Yana magana ne a madadin baki dayan ‘yan takarar shugaban kasar bakwai da suka fafata da shugaban mai ci. Kodayake, jam’iyyar da ke mulkin ta yi watsi da zargin magudin.
Hukumar zaben kasar Guinea ta ce sai karshen wannan mako za ta bayyana sakamakon zaben.
An kashe mutane da dama a rikicin da ya barke tsakanin magoya bayan gwamnati da na ‘yan adawa lokacin yakin neman zaban.
Bana shi ne karo na biyu da aka yi zaben da ya kunshi jam’iyyu da dama tun bayan da kasar ta samu ’yancin kai a shekarar 1958.