’Yan adawar siyasa sun nemi halaka ni – Mawaki Ibrahim Auyba

Ibrahim Ayuba mawaki ne da ya shahara a kan wakar siyasa. Kwanakin baya, ana gab da zaben gwamnoni ya sha da kyar a hannun ’yan adawa, a lokacin da yake yawon tallar jam’iyyarsa, inda wasu da ya yi zargin ’yan adawar siyasa ne, suka sace shi da niyyar halaka shi, a lokacin da yake zagayawa […]

’Yan adawar siyasa sun nemi halaka ni – Mawaki Ibrahim Auyba
’Yan adawar siyasa sun nemi halaka ni – Mawaki Ibrahim Auyba

Ibrahim Ayuba mawaki ne da ya shahara a kan wakar siyasa. Kwanakin baya, ana gab da zaben gwamnoni ya sha da kyar a hannun ’yan adawa, a lokacin da yake yawon tallar jam’iyyarsa, inda wasu da ya yi zargin ’yan adawar siyasa ne, suka sace shi da niyyar halaka shi, a lokacin da yake zagayawa yana tallar jam’iyyarsa da ’yan takararsa. Ya yi wa Aminiya bayanin yadda ya kubuta:

Wane ne Ibrahim Ayuba?

Kamar yadda aka sani, suna na Ibrahim Ayuba, wanda aka fi sani na da lakanin ‘Na Goma Mai Waka.’Akalla yanzu na shekara 35 da haihuwa kuma akalla na shekara 16 ina waka. Na yi wakoki kala-kala kuma wakar da aka fi sani na da ita, ita ce wakar da na yi wa ‘Ummina’ wato wakar da na yi wa mahaifiyata.
Yaushe ka fara wakar siyasa?
A tun lokacin da Buhari ya fara tsayawa takarar Shugaban kasa Allah Ya sa mun sonsa kuma na fara yi masa waka, har aka zo yau da yawancinmu mawaka muka shiga wakar neman canji. To na yi wa jam’iyyar da Buhari ke ciki wakoki kala daban-daban kuma na yi masa shi kansa waka akalla kala biyar. To kullum da yamma nakan dauki babur dina roba-roba, in daura lasifika da janaretona a bayan babur din, na sa wakar nemen canji; ina zagawa layi-layi, unguwa-unguwa. Da aka sace mashin din, Allah Ya ba ni kudi na sayi mota, na dora mata lasifika gaba da baya, na kuma sa mata janareto. A kullun nakan zuba mai na Naira 2, 500 tsakanin mota da janareto na kuma babu mai ba ni kwabonsa. Ni dai sha’awata in zaga ina tallar jama’iyyata da kuma ’yan takarana. Ashe abun ba ya wa wasu dadi. Sai suka biyo ni har gida suka bude injin motar suka zuba gishiri.
Motar ta da daina aiki. Na kara sayen wannan ta uku, ita ma na sa mata lasifikoki kamar yadda na yi wa wancan motar; kusan kullum sai na zagaye cikin garin Zariya da wajenta, ina sa waka, ina bi layi-layi.
Me ya faru da kai daga baya?
To a ranar Laraba, misalin karfe tara na dare; ina cikin tafiya kawai sai na ga wata mota kirar Sharon ta sha gabana, wata kuma motar kirar Hilos ta matse ni ta baya. Da ganin haka sai na yi sauri na daga gilashin motata, sai ko mutanen suka fito da adduna da su gariyo, suka hau motata da sara. Kafin ka ce wani abu sun yi kaca-kaca da motar, ni kuma suka kamo ni suka daure min hannayena da kuma bakina, suka jefa ni a motarsu, suka tafi da ni wani daji da ke hanyar Galadimawa. Nan suka fara muhawarar a kasha ni, sai wani daga cikinsu ya ki yarda da a kashe ni. Su kuma sauran suka ce masa ai cewa aka yi mu kashe shi, don haka dole mu kashe shi. Da yake kwanana bai kare ba sai suka yanke shawarar cewa su daure ni har na mutu. Don haka suka yi mini mummunan dauri, na kwana a wurin da sassafe sai ga biyu daga cikinsu sun dawo. Suka ce har yanzu fa shegen bai mutu ba. Suka aje wayoyina a gabana kuma ana ta kiran wayoyin ina kallo amma ba zan iya dauka ba.
Bayan sun dauki wani lokaci, suka kwashe wayoyin suka kara tafiya, suka bar ni a nan na kara wuni a daure. Bayan magariba sai suka dawo suka kwance ni, suna kwance ni jiri ya kwashe ni, na fadi kuma a lokacin ba na gani saboda tsananin wahala. Suka dauko ni suka kawo ni bakin kwalta. Na farka ne kawai na gan ni a gadon asibiti.
Ko za ka iya sanin wadanda suka yi maka wannan aika-aika?
Wallahi ba zan iya sanin ko su waye ba sai dai a zatona ’yan adawa ne, saboda suna jin haushi na tuntuni saboda na ki yi musu waka kuma na gargadi yarana da kada su kuskura su yi wa wani wanda ba dan jam’iyyata ba waka a sutudiyo dina. Kuma ni Allah Ya cika min burina na farko tun da aka zabi Buhari a matsayin Shugaban kasa. Buri na biyu shi ne, Allah Ya tabbatar min da Nasiru el-Rufa’i a matsayin Gwamanan Jihar Kaduna.
Me kake buri daga wadannan da aka zaba?
Na Goma Mai Waka, ni ba na bukatar komai illa a kyautata wa al’umma kuma a cire mu daga cikin wannan kangi da muka shiga; domin idan ni aka yi mawa, ni kadai zan amfana ba tare da sauran al’umma ba. Burina a yau in ga an daina kashe al’umma, jama’a su zauna lafiya, mu fita da ga cikin wannan kangin bauta da aka sa mu.