’Yan adawar Thailand sun jajirce sai Firayiminista ta yi murabus
Firayiministar kasar Thailand da ke fama da matsayin lambar ’yan adawa kan lallai ta sauka daga mukaminta, ta rusa majalisar kasar, ta kuma bukaci a gudanar da zabe. Su kuwa masu zanga-zanga a birnin Bangkok sun ce ba ta isa ta sanya wadanda ba zababbu ba, su mulke su.’Yan sanda sun kiyasta yawan masu zanga-zangar, […]
?????????????????????????????????????????????????????????

Firayiministar kasar Thailand da ke fama da matsayin lambar ’yan adawa kan lallai ta sauka daga mukaminta, ta rusa majalisar kasar, ta kuma bukaci a gudanar da zabe. Su kuwa masu zanga-zanga a birnin Bangkok sun ce ba ta isa ta sanya wadanda ba zababbu ba, su mulke su.
’Yan sanda sun kiyasta yawan masu zanga-zangar, cewa sun kai dubu 160, har ma sun yi cincirindo a gaban ofishin Firayiminista Yingluck. Babu tashin hankali, babu zubar da jini, haka aka gudanar da zanga-zangar.
Masu zanga-zangar na bukatar a kawar da Gwamnatin Yingluck, ta yadda za a share tasirin dan uwanta tsohon Firayiminista, Thaksin Shinawatra, wanda aka kawar da gwamnatinsa a shekarar 2006. Don haka ya tafi gudun hijira, ta yadda zai kauce wa zaman kurkuku, bisa tuhumar cin hanci da rashawa.
Shugaban ’yan adawar kasar, Suthep thaugsuban ya yi jawabi ga magoya bayansa, inda ya ce: “Daga wannan lokacin al’ummar Thailand za su karbi karfin iko mu mayar da shi ga al’umma.”
Ya ce Gwamnatin Yingluck ta nuna gazawa, kuma cin hanci da rashawa ya dabaibaye kasar, har ta kai ga an samu hauhawar farashi a shirin bunkasa noman shinkafa da samar da tsaftattacen rowan sha.
Tun a ranar Lahadin da ta gabata, ’yan Jam’iyyar adawa Democrat suka yi murabus daga mukamansu, inda suka yi nuni da cewa ba za su iya aiki tare da Yingluck ba.