’Yan Afirka miliyan 1 na fama da tarin fuka cikin rashin sani —WHO

Kashi 20 na sabbin kamuwa da cutar ta tarin fuka ko kuma TB na dauke da cutar HIV.

’Yan Afirka miliyan 1 na fama da tarin fuka cikin rashin sani —WHO

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce fiye da mutane miliyan guda a nahiyar Afirka na rayuwa da tarin fuka ko kuma TB ba tare da sani ba, lamarin da ke matsayin babban kalubale ga tsarin yaki da cutar.

 A jawabinta yayin bikin ranar yaki da cutar ta tarin fuka ko kuma TB, Shugabar WHO reshen Afirka, Dokta Matshidiso Moeti ta ce cutar na ci gaba da kisan mummuke ga miliyoyin al’ummar Afirka inda yanzu haka ake da jumullar mutanen da yawansu ya haura miliyan 1 da ke dauke da cutar amma ba tare da sani ba.

A cewar Moeti, duk da kokarin da hukumar ke yi da taimakon kungiyoyi masu zaman kansu da ke aikin yaki da cutar ta hanyar wayar da kai da kuma bayar da magunguna, har yanzu akwai wakeken gibi a kokarin kawar da cutar tsakanin al’ummar nahiyar.

Shugabar ta WHO ta ce lura da tazarar da ke tsakanin alkaluman wadanda suka yi rijistar cutar da kuma wadanda ke mutuwa sanadiyyar cutar, hakan na nuna yawan mutanen da ake da su wadanda basu san suna dauke da cutar ta TB ko kuma tarin fuka ba.

Dokta Matshidiso Moeti ta ce kashi 40 cikin 100 na masu dauke da cutar TB a Afirka ko dai basu san suna dauke da cutar ba ko kuma ba a kai ga tattara bayanansu a kunshin rahoton WHO na shekarar 2021 ba.

A cewar jami’ar, kashi 20 na sabbin kamuwa da cutar ta tarin fuka ko kuma TB na dauke da cutar HIV wanda ke matsayin babban tashin hankali lura da rashin kulawar da galibinsu ke fuskanta.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos