’Yan Afirka ta Kudu sun je rumfunan zabe don zaben shugaban kasa
Dubbunnin jama’a ne suka fito don kada kuri’arsu a zaben da aka gudanar ranar Larabar da ta gabata a kasar Afirka ta Kudu, wanda shi ne karo na biyar tun bayan kawo karshen mulkin gwamnatin wariyar lauyin fata shekaru 20 da suka wuce.Jam’iyyu 29 ke fafatawa a zaben wanda ake kyautata zaton jam’iyya mai ci, […]

Dubbunnin jama’a ne suka fito don kada kuri’arsu a zaben da aka gudanar ranar Larabar da ta gabata a kasar Afirka ta Kudu, wanda shi ne karo na biyar tun bayan kawo karshen mulkin gwamnatin wariyar lauyin fata shekaru 20 da suka wuce.
Jam’iyyu 29 ke fafatawa a zaben wanda ake kyautata zaton jam’iyya mai ci, wato ANC za ta lashe duk zargin almundana da ake wa wasu ’ya’yanta ciki har da Shugaban kasar, Jacob Zuma.
Wani da ya kada kuri’arsa mai suna Sithembiso Ngcobo ya shaida wa tashar talabijin ta Aljazeera cewa dalilin da ya sa matasa ba su fito sosai ba, shi ne yadda galibinsu ba su karar da irin fadi tashin da aka sha ba kafin kawo karshen mulkin wariyar launin fata wanda gwamnatin wancan lokacin ba kowa ne ta ba ’yancin kada kuri’a ba.
Har-ila yau, wata kungiya da ta kunshi tsoffin ministoci da kuma wasu kungiyoyin kare hakkin jama’a wanda suke kira ga masu kada kuri’a da su guje wa zaben jam’iyya mai mulki. kungiyar ta ce ta na yin wannan ne saboda yadda gwamnatin jam’iyyar ANC ta kasa ceto jama’ar kasar.
Gwamnatin ANC dai karkashin jagorancin Shugaba Jacob Zuma na fuskantara tuhume-tuhume da suka hada da na almundana da kuma yadda tattalin arzikin kasar ke ci gaba da yin tafiyar hawainiya. Duk da wadannan kalubalen dai, kuri’ar jin ra’ayin jama’a da aka gudanar gabanin zaben, na nuni da cewa jam’iyyar ANC ce za ta samu galaba da akalla kashi sittin cikin dari wanda hakan zai baiwa Shugaba Zuma damar zarcewa zuwa zango na biyu na wa’adin shugabancinsa.