’Yan Arewa 151 da ake so a tuntube su saboda Jonathan

A kokarin da ake yi na ganin shugaba Jonathan ya samu goyon yankin arewacin kasar nan a zaben  shekarar 2015, wadansu na hannun damansa sun tsara sunayen wadansu fitattun ‘yan Arewa da za a tuntube su domin su goyi bayan Jonathan. Aminiya ta samu takardar da ke dauke da sunayen mutanen wanda aka ce wani […]

’Yan Arewa 151 da ake so a tuntube su saboda Jonathan

A kokarin da ake yi na ganin shugaba Jonathan ya samu goyon yankin arewacin kasar nan a zaben  shekarar 2015, wadansu na hannun damansa sun tsara sunayen wadansu fitattun ‘yan Arewa da za a tuntube su domin su goyi bayan Jonathan. Aminiya ta samu takardar da ke dauke da sunayen mutanen wanda aka ce wani dan siyasa mai zakin baki daga jihar Bauchi da yake kan gaba wajen goyon bayan Jonathan ne ya tsara sunayen.

Wadanda suka fara tonon sililin

Shugaban majalisar gwamnonin Arewa, gwamnan jihar Neja Mu’azu Babangida Aliyu ne a lokacin bikin cika shekara 25 na Sarkin Minna Alhaji Umaru Bahago, ya fara bayyana cewa akwai wadansu fitattun ‘yan Arewa 400 da aka tsara sunayensu domin su goyi bayan Jonathan.
Bayan Babangida Aliyu ya yi wannan fallasar sai kuma shugaban kungiyar kare muradun Arewa (ACF) Alhaji Aliko Muhammad, wanda shi ma sunansa ke cikin jerin sunayen da aka tsara, ya tabbatar da cewa ya samu wannan takardar.
Ya bayyana haka ne a wata sanarwa da shi da kansa ya sanya wa hannu, inda ya nuna cewa, ‘’ wadanda suke ba shugaban kasa shawarar ya yi amfani da kudi wajen neman goyon bayan mutane, sun nuna karara cewa wani abu daban za a yi la’akari da shi wajen sake zaben shugaban amma ba ayyukan da ya yi ba., idan kuwa haka ne, to kada su sanya dattawan Arewa a cikin wannan harkar, domin a cikin sunayen da muka gani mun ga akwai sunayen mutanen da ake matukar girmamawa a yankin Arewa.’’
Shugaban na ACF ya ci gaba da cewa, ‘’sai dai kuma da muka yi bincike a tsakanin jami’an gwamnati kuma muka yi magana da mafi yawan wadanda aka sanya sunayensu, sun tabbatar mana da cewa ba su san komai ba a game da haka.’’
Kodayake gwamnan Neja Babangida Aliyu ya ce mutane 400 ne aka tsara, amma a takardar da Aminiya ta samu mutane 151 ne kawai a ciki. Kuma duk majiyoyinmu da suka ga jerin sunayen sun tabbatar da cewa mutane 151 ne.
Akwai nakasu a jerin sunayen
Babu wanda ya sanya a hannu a takardar da ke dauke da sunayen, wanda ya nuna cewa akwai shakku game da ingancinsa. Sannan kuma an sanya sunayen mutanen da suka rasu, kamar dan siyasan nan a janhoriya ta biyu kuma tsohon ministan kwadago a karkashin gwamnatin Sani Abacha, marigayi Sanata Uba Ahmad, wanda ya rasu bara. Kuma sunansa ya fito a karkashin jihar Bauchi ne, alhali shi dan jihar Gombe ne.
Nakasun da aka samu wajen tsara sunayen ya nuna cewa wadanda suka shirya sunayen sun tsara su a cikin gaggawa ne domin samun wata alfarma daga ofishin shugaban kasa, kuma ga alama an shirya sunayen ne da dadewa, lokacin da wadansu daga cikin mutanen da aka tsara suke da rai.
Haka kuma suna Sarkin Katagum mai hedkwata a Azare sunansa ya fito sau biyu a matsayin sarkin Katagum da sarkin Azare. Haka nan kuma akwai sunan Solomon Lar wanda ya rasu kwanan nan a cikinsu.
Sunayen mutanen
Daga jihar Adamawa akwai mutane 15, sune: tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da tsohon jakada Alhaji Hassan Adamu da Dokta Mahmud Tukur da Farfesa Jibiril Aminu da Cif Joel Madaki da Sanata Jonathan Zwingina da Sanata Paul Wampana da Dan Suleiman da Alhaji Gambo Jimeta da Alhaji Adamu Bello da Alhaji Dauda Birma da Lamidon Adamawa da Sarkin Mubi da Sarkin Bachama Sarkin Ganye.
A jihar Bauchi kuma akwai mutane 8, sune: Alhaji Bello Kirfi da Alhaji Aliko Muhammad da Alhaji Aminu Saleh da marigayi Uba Ahmad da Sarkin Azare da Sarkin Katagum (duk daya ne da Azare) da Sarkin Dass da Sarkin Bauchi.
A jihar Binuwai an tsara sunayen mutane 9, sune: Mista Paul Unongo da Cif Isaac Shaahu da Benjamin Chaha da Sanata Ameh Ebute da Janar Geofrey Ejiga mai ritaya da Iyorchia Ayu da Janar Lawrence Onoja mai ritaya da Tor Tib da Ochi na Idoma.
Daga jihar Borno kuma akwai sunayen mutane 10, sune: Shettima Ali Munguno da Alhaji Muhammadu Goni da Alhaji Ashekh Jarma da Janar IBM Haruna da Farfesa Nura Alkali da Ali Modu Shariff da Sanata Maina Ma’aji Lawan da Alhaji Kashim Imam da Shehun Dikkwa da kuma Shehun Borno.
A Gombe akwai mutane biyar, sune: Sarkin Gombe da Sarkin Dukku da Sarkin Akko da Sanata Adamu Waziri da kuma Alhaji Sa’idu Kumo.
A Jigawa kuma akwai mutane 10, sune: Saminu Turaki da AbM Mukhtar Muhammad da Alhaji Bashir dalhatu da Alhaji Ibrahim Babankowa da Alhaji Saleh Hassan Hadeja da Bello Maitama Yusuf da sarakunan Dutse da Hadeja da Ringim da Gwaram.
Daga Kano kuma akwai mutane 11, sune: Alhaji Tanko Yakasai da Dokta Junaidu Muhammad da Alhaji Yusuf Maitama Sule da Alhaji Muhammad Abacha da Alhaji Aminu dantata da Ghali Umar Na’abba da Galadiman Kano Alhaji Tijjani Hashim da Farfesa dandatti Abdulkadir da Babban limamin Kano Farfesa Sani Zaharaddeen da Alhaji Sama’ila Gwarzo da kuma Hajiya Naja’atu Bala Muhammad.
A jihar Katsina kuma akwai mutane 14, sune: Alhaji Ahmadu Kurfi da Alhaji M.D.Yusuf da Alhaji Ibrahim Coomasie da Alhaji Lawal Kaita da Alhaji Musa Musawa da Alhaji Lema Jibirilu da Alhaji Sama’ila Isa Funtuwa da Dokta Usman Bugaje da Alhaji Sani Zangon Daura da Alhaji Abba Musa Rimi da Sanata Mamman Abubakar danmusa da Alhaji Umaru Mutallab da sarakunan Katsina da Daura.
Daga jihar Kebbi kuma akwai mutane 14, sune; Abubakar dangiwa Umar da Muhammad Bello Khaliel da tsohon Sarkin Gwandu Al-Mustapha Haruna Jakolo da Alhaji Abubakar Musa da Ishaya Bamaiyi da Muhammad Magoro da sarakunan Argungu da Yauri da Zuru.
A jihar Kaduna kuma akwai mutane 7, sune: Janar Zamani Lekwot mai ritaya da Farfesa Ango Abdullahi da  Dokta dalhatu Sarki Tafida da Alhaji Rilwanu Lukman da Alhaji Gidado Idris da Alhaji Umaru Dikko da kuma Sarkin Zazzau.
A jihar Kogi akwai mutane 7, sune: Alhaji Sule Yaji da Alhaji Jibiril Isah Echocho da Air Commodore I. Alfa mai ritaya da Alhaji Abdullahi Ibrahim SAN da Attah na Igala da kuma Attah na Ibira.
Daga jihar Kwara akwai mutane 6, sune; Cornerlius Adebayo da Alhaji Shaba Lafiyagi da Sunday Adewusi da Farfesa Ibrahim Gambari da Sarkin Ilorin da Etsu na Pategi.
A jihar Nasarawa akwai mutane 4, sune: Alhaji Isiyaka Ibrahim da Sarkunan Lafiya da Keffi da kuma Nasarawa.
A jihar Neja akwai mutane 5, sune: Janar Inuwa Wushishi da Kanar Sani Bello da Sarkin Suleija da Etsu Nupe da kuma Etsu Lapai.
Sai jihar Filato mai mutane 9, sune; Sanata John Wash Pam da Misis Helen Gomwalk da marigayi Solomon Lar da Alhaji Yahaya Kwande da Alhaji Saleh Hassan da Janar Jerry Useni da Air Commordore Benard Banfa da Janar Damkat Bali da Gbong Gwong Jos Cif Jacob Buba Gyang.
A jihar Sakkwato akwai mutane 6, sune: Tsohon shugaban kasa Shehu Shagari da Alhaji Abubakar Alhaji da tsohon Sarkin Musulmi Ibrahim Dasuki da Alhaji Muhammad Arzika da Alhaji Yusuf Yabo da Alhaji Attahiru Bafarawa.
A jihar Taraba kuma akwai mutane 6, sune: T.Y.danjuma da Jolly Nyame da Sarkin Muri da Aku Uka na Wukari da Idris Waziri da kuma Mista Baba Adi.
Daga jihar Yobe akwai mutane 5, sune: Alhaji Adamu Fika da Adamu Ciroma da sarakunan Fika da Damaturu da Potiskun.
Sai kuma jihar Zamfara da ke da mutane 6, sune: Alhaji Umaru Shinkafi da Yahaya Abdulkarim da sarakunan Anka da Gusau da Tsafe da kuma kauran Namoda.
Bayanin da wadansu daga cikin mutanen suka yi
Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku ya bayyana ta bakin kakakinsa Garba Shehu cewa, yana sane da jerin sunayen amma ba shi da kwafin takardar kuma babu wanda ya tuntube shi a kan batun. Shi ma Alhaji Isyaku Ibrahim ya ce ya san da maganar sunayen amma babu wanda ya tuntube shi.
Shi kuwa Benjamin Chaha da Aminiya ta tuntube cewa ya yi bai san cewa an rubuta sunansa a cikin jerin sunayen wadansu mutane ba. Shi ma Alhaji Adamu Bello da aka tuntube shi ya ce bai san da maganar ba kuma babu wanda ya tuntube shi. Amma Abubakar dangiwa Umar da aka tuntube shi cewa ya yi babu wanda ya tuntube shi, amma kuma bai ga wani abun damuwa ba idan mutanen shugaban kasa suka tuntubi wadansu mutane, ‘’ da zarar hukumar zabe ta dage takunkumin yakin neman zabe duk masu neman zaman shugaban kasa za su fara tuntubar mutane.’’
Dokta Paul Unongo ya ce bai san da maganar ba, shi ma T.Y.danjuma ya ce bai san da sunayen ba kuma babu wanda ya tuntube shi. Haka shi ma Dokta Junaidu Muhammad ya ce bai san komi game da batun ba.
Shi kuwa Tanko Yakasai cewa ya yi ba a tuntube shi ba, ‘’duk al’amarin na makarkashiya ce, babu wata makarkashiya da za a shirya mini da za ta sanyi ni in goyi bayan wani dan takara da ba na so.’’