’Yan Arewa 170 Da Muka Kama Ba ’Yan Ta’adda Ba Ne —Amotekun

Amotekun ta ce yunkurin tserewar da wasu daga cikin matafiyan suka yi ne ya sanya aka kama su

’Yan Arewa 170 Da Muka Kama Ba ’Yan Ta’adda Ba Ne —Amotekun

Amotekun

Rundunar tsaron yankin Kudu maso yammacin Najeriya (Amotekun) ta bayyayna cewa ’yan Arewa matafiya 170 da ta kama ba ’yan ta’adda ba ne kamar yadda ta zata a baya.

Rundunar ta ce ta gano matafiya ne da za su sauka a garin Ogere na Jihar Ogun, don haka za ta mika su ga yan Sandan jihar, domin ci gaba da bincike.

Shugaban Amotekun reshen Jihar Oyo, Kanar Olayinka Olayaju, ya bayyana wa Aminjya cewa bayan sun hango ayarin matifiyan ne, amma yunkurin tserewar da wasu daga cikin matafiyan suka yi ne ya sanya aka kama su.

“Mutanenmu sun sanar da ni yadda kusan mutum 20 daga cikinsu suka tsere da suka hango su, wannan ne ya sa suka yi zargin ko ’yan Boko Haram ne.

“Amma yanzu za mu mika su ga Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ogun, tunda sun ce can suka nufa,” in ji shi.