’Yan Arewa a Benin sun nuna alhini kan harin bom da aka kai Kano

Al’ummarn Arewa mazauna Jihar Edo sun nuna alhininsu kan harin bom da aka kai Babban Masallacin birnin Kano, inda suka bayyana ra’ayinsu dangane da kisan gilar da aka yi wa al’ummar Musulmi a Masallacin juma’a na Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi na II, a ranar juma’ar makon da ya gabata, inda mutane da […]

’Yan Arewa a Benin sun nuna alhini kan harin bom da aka kai Kano
’Yan Arewa a Benin sun nuna alhini kan harin bom da aka kai Kano

Al’ummarn Arewa mazauna Jihar Edo sun nuna alhininsu kan harin bom da aka kai Babban Masallacin birnin Kano, inda suka bayyana ra’ayinsu dangane da kisan gilar da aka yi wa al’ummar Musulmi a Masallacin juma’a na Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi na II, a ranar juma’ar makon da ya gabata, inda mutane da dama suka rasa ransu, kuma wasu da dama suka jikkata, tsakanin yara da manya. Kodayake babu wata kungiyar da ta fito ta dauki alhakin kai wannan harin.

Bisa la’akari da wannan mummunan hali da al’umma ta tsinci kanta a ciki, sai mazauna wannan yanki, ‘’yan asalin Arewa suka yi gangamin bayyana ra’ayoyinsu ga jaridar Aminiya, inda wasu daga cikin ‘yan Arewan mazauna garin Benin a Jihar Edo .
Ibrahim Muhammed Sumaila ya ce’’Hakika wannan abin da ya faru a Kano mun yi matukar bakin ciki, sai dai abin da zan iya ce wannan shi ne ‘yan uwa wadanda suka rasa rayukakansu Allah ya jikansu, Ya sa wannan ya zama tsira garesu ranar tashin alkiyama, ya bai wa iyalansu hakuri. Wadanda suka samu raunuka kuma Allah ya ba su lafiya sai ya ci gaba da cewa wannan aika-aikar babu mai imani da zai yi marhabin da shi Musulmi ko kirista kawai shawara ita ce, mutane su ji tsoron Allah, kuma mu tashi tsaye akan addu’ar Allah ya dawo mana da zaman lafiya a kasarmu.”
Malam Abdullahi Larau shi kuma Addu’a ya yi inda ya ce: ‘’Ni dai abin da zance shi ne Allah ya yi mana kariya, kuma ya kawo mana karshen wannan masifar. Wadanda suka mutu kuma Allah ya jikansu.
Shi kuwa Badamasi Muhammed ya ce: ‘’Na farko dai ina yi wa ‘yan Uwa Musulmi wadanda suka riga mu gidan gaskiya addu’ar Allah ya gafarta musu, kuma ina kira ga ’yan uwana Musulmi da sauran kada irin wadannan ayyukan ‘yan ta’adda su jefa musu fargaba azukatansu, domin mutuwa tana ko ‘ina; su kuma manyan Arewa su tashi su yi wata hobbasa, inda za su nuna matsayinsu na shugabanni.
Malam Shi’tu Abdul-Mumini cewa yayi, a ra’ayinsa kamar haka:’’Ni dai bayanina akan wannan harin shi ne, ina kira tare da rokon manyamu na Arewa su tashi tsaye, su yi wani abu na nuna suna da tausayi ga al’ummar Arewa, musamman wadanda a halin yanzu suke fuskantar hare-haren masu tada kayar baya a yankin kuma ina shawartar ’yan uwana akan dagewa da yawaitar addu’o’i, Allah ya warware mana wannan matsalar.
Malam Sabi’u Maigari ‘’Ra’ayina game da wan nan ta’addanci na ‘yan tada kayar baya a Arewa shi ne, mu ci gaba da yin addu’a Allah ya yi mana katanga tsakaninmu da irin wadannan mutane marasa imani, sannan ya dawo mana da zaman lafiya a yankunanmu.
Sai ra’ayin Alhaji Sani Musa Shugaban Fataken Shanu na Jihar Edo da yake cewa: ‘’Abin da zance shi ne, Allah ya jikan ’yan uwa wadanda wannan harin ya salwantar da rayukansu marasa lafiya da suke asibiti, ko suke kwance a gidajensu Allah ya ba su lafiya ya kuma kiyaye gaba sai ya roki gwamnati akan ta nuna da gaske take yi wajen murkushe wadannan marasa tsoron Allah. Ya ce ya zama wajibi ga jami’an tsaro a kasar nan su ci gaba da yin bincike na kwakwaf domin zakulo masu aikata miyagun laifukan a kasar nan, kuma ita gwamnatin ta yi odar kemarori masu nuna maboyar miyagu, ta sanya a biranen kasar nan, idan da so samu ne har da kauyuka, sannan su kuma wadanda suka rasa ‘yan uwa da iyaye da sauransu Allah ya ba su hakuri; Allah ya jikan wadanda suka rigamu gidan gaskiya, wadanda suke kwance a asibiti Allah ya ba su lafiya.
Alhaji Ishaku Abdullahi ya tofa albarkacin bakinsa kamar haka, inda ya ce:’’Ni dai abin da zan fara fada shi ne (Inna lillahi wa inna ilaihi rajiu’na), wadanda suka mutu Allah ya jikansu kuma duk mai hannu a cikin wannan aika-aikar Allah ya fallasa su duk da cewa gwamnati tana mai cewa tana yin wani abu akan wannan abin da yake ci gaba da faruwa, amma wajibi ne mu ci gaba da taimakawa da yawan addu’o’i.
Su kuma kungiyar dattawan Arewa ya kamata su tashi daga barci su hada kai da talakawa, domin samun maslaha akan abin da yake faruwa a Arewa.
Da yake bayyana ra’ayinsa, Malam Usman ‘’da farko bayanina shi ne Allah ya jikan ’yan uwanmu da suka mutu a wannan mummunan hari su kuma masu wannan aikata hakan Allah ya tona musu asiri aduk inda suke kuma tunda muna da jamian tsaro kama daga sojoji da ‘yan sanda amma gaba daya sai suka zura ido sun bar kome yana ta ci gaba da ta barbarewa abangaren tsaro akasannan sai dai muce Allah ya kyauta.