’Yan Arewa a Majalisar Tarayya sun ba da gudummawar N395m

’Yan Arewa a Majalisar Wakilai sun ba da gudunmmawar kudi Naira miliyan 45 da kayan more rayuwa na miliyan 350 ga al’ummar kauyen Tudun Biri

’Yan Arewa a Majalisar Tarayya sun ba da gudummawar N395m

’Yan Arewa a Majalisar Wakilai sun ba da gudunmmawar Naira miliyan 45 da kayan bore rayuwa na miliyan 350 ga al’ummar kauyen Tudun Biri da jirgin soja ya kai wa harin a taron Mauludi a bisa kuskure.

Shugaban ’Yan Arewa a Majalisar, Alhassan Ado Doguwa ya sanar da alkawarinsu na samar da abubuwan more rayuwa da kudinsu ya kai Naira miliyan 350 a kauyen.

Doguwa ya ce abubuwan da za su samar sun hada da cibiyar lafiya, azuzuwan makaranta da rijiyar burtsatse da kuma dakin taro.

Ya kara da yin Allah-wadai da harin, tare da cewa sun yanke shawar kai ziyarar ta’aziyya Tudun Biri.

Ya sanar da gudummawar ne a sakon jajensu ga al’ummar kauyen a zauren majalisar a ranar Litinin.

Dan majalisar ya bayyana cewa ziyarar za ta ba su damar gane wa kansu don fahimtar ainihin abin da ya faru a harin da jirgin sojin ya kai.

Sun ba da gudunmmawar ne washegarin da sanatoci 109 gaba dayansu suka ba wa al’ummar da harin ya shafa gudunmmawar miliyan N109.

An ceto jaririyar da ’yar aikin gida ta sace a Edo

An ceto mutum 58 da aka sace a Kaduna

Sarkin Zazzau ya naɗa sabbin hakimai 7

Hajjin 2025: Maniyyata za su fara ajiye N8.4m a Kaduna