’Yan Arewa ba su da wani dalilin kin zabar Tinubu — Ganduje

Ya ce bai taba ganin masoyin ’yan Arewa ba irin Tinubu

’Yan Arewa ba su da wani dalilin kin zabar Tinubu — Ganduje

Ganduje da Tinubu

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce ’yan Arewa ba su da wani dalili ko kadan da zai hana su zabar dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu.

Ya ce dan takarar tasu ya yi sadaukarwa mai tarin yawa wajen bunkasa Dimokuradiyya a Najeriya, musamman wajen kokarinsa na cicciba dan Arewa ya zama Shugaban Kasa.

Saboda haka, Ganduje ya ce yanzu ne daidai lokacin da ya dace a rama wa kura aniyarta.

Ganduje ya bayyana haka ne yayin wani taro da wata kungiya mai suna Volunteers for Democracy, karkashin Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Usman Alhaji ta shirya a Kano ranar Asabar.

A cewar Gwamnan, “Babu wani hanzari da ’yan Arewa suke da shi na kin zabar APC da dan takararta, Bola Tinubu.

“A baya, ya taka muhimmiyar rawa wajen nasarar ’yan Arewa, don haka ya kamata mu ma mu nuna halacci.

“Tinubu ya goyi bayan Buhari a gwagwarmayarsa har ya zama Shugaban Kasa. Bai nemi a biya shi da kowanne irin matsayi ba a gwamnati, kuma ya ci gaba da goyon bayan gwamnatin.

“Ni ban ma taba ganin masoyin ’yan Arewa ba kamar shi,” inji Ganduje.