’Yan Arewa ina muka dosa?

Tushen ci gaban kowace al’umma a duniyar nan ya ta’allaka ne ga hadin kan al’ummar da tausayin juna, kowa kuwa ya san al’ummarmu ta taso da wadannan abubuwa za ta cimma nasara. A da can iyaye da kakanninmu suna da hadin kai da tausayin junansu ga yawan ziyartar juna fiye da yadda muke yi a […]

’Yan Arewa ina muka dosa?

Tushen ci gaban kowace al’umma a duniyar nan ya ta’allaka ne ga hadin kan al’ummar da tausayin juna, kowa kuwa ya san al’ummarmu ta taso da wadannan abubuwa za ta cimma nasara.

A da can iyaye da kakanninmu suna da hadin kai da tausayin junansu ga yawan ziyartar juna fiye da yadda muke yi a yanzu, duk da cewa a wancan lokacin ba su da wadatattun kayan sufuri, na sadarwa kuwa ba batunsa ake yi ba. Haka tarin dukiyar da ake da ita yanzu ta ninninka wadda kakanninmu suka mallaka. Sai dai kuma sun fi mu kyautatawa a cikin abin da suka mallaka, wanda hakan ne ya jawo musu ci gaban da mu muka kasa samu kuma ake yi musu kallon al’umma daya saboda ba su da muguwar dabi’ar nan ta nuna kabilanci ko bambancin addini

Haka suka yi ta tafiya tun kafin zuwanTurawan mallaka kuma har suka zo suka tafi kakanninmu na da kyakkyawar mu’amula kuma irin wannan rainon suka bai wa ’ya’yayensu suka kuma tashi a kan haka.

Cikin ikon Allah a irin ’ya’yan nasu ne muka samu hazikan shugabannin da suka gina Arewarmu da Najeriya baki daya suka kuma dora yankinmu a kan turbar da in aka bi ta za ta kai mu ga kyakkyawan matsayi wajen ci gaban rayuwa ta yadda za mu iya gogayya da Turawan Yamma. Wadannan iyaye namu da suka dora Arewa a tudun-mun-tsira su ne su Sa Ahmadu Bello Sardauna da Sa Abubakar Tafawa Balewa da Malam Aminu Kano da sauransu.

Ina da yakinin duk lokacin da aka ambaci wadannan bayin Allah sai an samu masu yi musu addu’a saboda kokarin da suka yi wa Arewa a lokacinsu, duniya ta shaida su suka dago da martabar Najeriya baki daya. To, a irin rainon da su ma suka yi ne aka samu su Janar Murtala Ramat Muhammad da dai sauransu.

Tabbas! Kowa ya san lokacin da wadancan hazikan mutane suke raye babu wanda ya isa ya nuna Arewar da yatsa, ba dan Kudancin Najeriya ba ko da Turawan Yamma ne, a haka kuma suka tafi suka bar Arewa da kimarta a idon duniya, sai dai kash! Ba da jimawa ba da tafiyar wadancan bayin Allah sai Arewa ta rasa kimarta, ta koma tamkar mujiya a cikin tsuntsaye. Ko me ya jawo haka?

A halin yanzu dan Arewa ba ya  iya zuwa Kudancin kasar nan ya sake ya yi harkokinsa kamar yadda dan can Kudu zai zo Arewa ya yi abin da yake so. Kai hatta karatu a jami’o’in tarayya da ke Kudu ’yan Arewa ba sa samun guraben karatu a cikinsu idan ma an samu to, tsangwama da kyara ba za su bar mutum ya iya zama ba. Ba sa ganin Arewa da ’yan Arewa da mutunci, ba sa ganinmu da wata kima a halin yanzu duk da yake yankinmu ne mafi yawan jama’a da girman kasa. Kullum suna ganinmu a matsayin ci-ma-zaune sun dauki karan-tsana sun aza mana. Wai ta yaya hakan ya samo asali ne ma?

Ni dai ina ganin hakan ya samo asali ne daga ba su kofa ta hanyar sauka daga kan waccan turbar da su Sardauna suka dora mu. Kadan daga cikin kofar da suka samu su ne; hadin kan da suka sanmu da shi a da yanzu babu shi, sun ga muna yawan fada da junanmu, suna yawan jin fadan da ke faruwa a Kaduna tsakanin Katafawa da Hausawa da Filato a tsakanin Berom da Hausa/Fulani da Taraba da Benuwai da sauransu. Ta haka ne suka samu damar aiwatar da abin da suke so a kanmu. Uwa-uba kuma sun samu wata dama ta yin haka ne yayin da batagarin ’yan siyasarmu suka sayar da mutuncin yankinmu ta hanyar amfani da ofisoshinsu, suna karbar kudi daga hannun ’yan Kudu su samar musu manyan mukamai saboda kawai kansu suka sani da ’ya’yansu, ba sa hangen baya balle su yi tunanin gaba.

To, wadannan kofofi biyu da suka samu ne ya sa suka raina mana yankinmu da ma mu kanmu wanda a da babu wani dan Kudu da yake da bakin magana a kan Arewa. Idan ma zai yi to, sai dai ya yabe ta. Kullum idan na ji wani mummunan labari game da Arewa sai wadansu tambayoyi suke fado min wadanda har yanzu na kasa samun amsarsu, sai in ji ina tambayar kaina; mu ’yan Arewa ina muka dosa ne? Shin a haka za mu yi ta tafiya cikin wannan kaskancin matsayi? In haka ne, a wane irin yanayi ’ya’yanmu za su taso in har ba mu tashi tsaye mun gyara ba? Sai yaushe za mu dawo da martabar yankinmu ne?

A karshe ina so duk wani dan Arewa ya sani har yanzu fa ’yan Kudu kudin goro suke yi mana, ba ruwansu da kasancewarka Bafulatani ko Bahause ko Berom ko Nupe ko Kanuri ko Tibi ko Angas.  Kawai in kai dan Arewa ne to kai dan Arewa ne hatta da bambancin addini ba sa dubawa balle na yare. Sannan ina kira mu kara sani kamar yadda muke da bambance-bambancen yare da addini haka su ma suke da shi, sai dai su ba sa nuna wa junansu. Don haka nake kira ga ’yan siyasa da sarakunan gargajiyarmu su yi kokarin dawo mana da martabarmu ko ma samu abin da muke nema.

Allah Ya datar da mu Ya ba mu ci gaba da zaman lafiya mai dorewa a Arewa da Najeriya baki daya.

  1. Bello Kiyawa (070-3252-8895)

[email protected]