’Yan Arewa masu fatauci na shan matsi daga masu karɓar haraji a Kuros Riba
Ban taɓa ganin yadda aka samu ƙaruwar masu karɓar haraji ba sai a wannan karo.
Tun bayan da aka ware Jihar Kuros Riba daga daga cikin jihohin da ke samun kaso 13 na jihohin da ake haƙo man fetur sai jihar ta koma wajen dora haraji mai yawa ga jama’a.
Jihar Kuros Riba mai rijiyoyin man fetur 18 an ƙwace su a hukumance aka mallaka su ga Jihar Akwa Ibom a zamanin mulkin tsohon Shugaban Ƙasa Cif Olusegun Obasanjo a shekarar 2002 .
- Shugaban Hukumar Tattara Bayanan Sirri ya yi murabus
- An soma biyan ma’aikata sabon albashi mafi ƙaranci a Adamawa
Tun daga wancan lokaci kuma jihar ta fada a cikin wani yanayi na rashin samun wadatattun kudi daga kason tarayya da jihohi masu man fetur ke samu.
Kasancewar jihar ba ta cikin jihohi masu man fetur, Gwamnan Jihar a yanzu Sanata Bassey Edet Otu ya yi ƙoƙarin ganin an lalubo wasu rijiyoyin man, don jihar ta koma cikin sahun jihohin da ke amfana daga kason da ake bai wa jihohi masu albarkatun man fetur.
Dukkan gwamnonin da jihar ta yi sun yi ta ƙoƙarin ganin jihar ta samu kudin shiga, don gudanar da ayyukan ci gaban al’umma.
Wannan ƙarancin kudin shiga da jihar take fuskanta ya sa gwamnati ta juya kan ’yan kasuwa da masu safarar kaya zuwa jihar, lamarin da ya jefa ’yan kasuwa da fataken kaya ’yan Arewa a cikin damuwa saboda yadda ake tatsarsu ta hanyar karɓar kudade ba gaira ba dalili da sunan kudin shiga.
Karɓar kudaden na haifar da kafa ƙungiyoyi da cibiyoyin karɓar haraji da jangali da sunan gwamnatin jihar ko ƙaramar hukuma, ciki har da na bogi, wanda hakan ya sa kudin da masu kaya ko direbobi ke biya ke yim yawa.
Binciken da Aminiya ta gudanar ta gano matsalar karɓar na goro daga hannu direbobi da ake zargin masu karɓar haraji na yi, walau na gwamnati ko na jabu da kuma jami’an tsaro da su ma ba a bar su a baya ba, ke sa farashin kayayyaki ƙara hauhawa.
Duk wani nau’in kaya da ake kai wa daga Arewa irin su albasa da tumatur da wake da dankali da gero da sauran kayan abinci da ake amfani da su da ake kawowa daga Arewa mai kayan kan biya kudade masu yawa a matsayin haraji.
Bincike ya kuma gano yadda ake karɓar haraji mai yawa daga masu shigo da shanu da awaki, zuwa jihar.
Malam Auwalu Sani wani mai kawo shanu da awaki daga Arewa, ya ce aƙalla suna kashe da sama da Naira miliyan daya a matsayin kudin da suke raba wa ma’aikata da masu karɓar kudin haraji da jangali na ƙarya da gaskiya, a kan kowace tirela.
Ya ce, “Idan muka dauko dabbobi daga Jihar Taraba zuwa Binuwai zuwa Kuros Riba duk shingen da muka zo, su za su yanka abin da za ka ba su, kuma dole ka biya muddin kana son kai kayan naka inda kake buƙata.
“Domin idan ba haka ba za su ce direba ya ajiye motar a gefen hanya su ɓata muku lokaci. Kuma ka san yadda dabbobi suke dama sun galabaita, dole don gudun asara ka biya ka wuce.”
Ta ɓangaren masu kayan lambu kuma wani mai kai kayan lambu Malam Magaji Zarewa ya ce da zarar ka shige Makurdi ka fada matsalar hanya ke nan.
“Tsakanin Jihar Binuwai da Kuros Riba sai ka samu shigaye masu yawa, wasu na karɓar Naira dubu biyar-biyar, wasu dubu goma-goma ga kuma masu karɓar kudi na gwamnatin jiha da ƙaramar hukuma, har ka isa Kalaba.
Shugaban Ƙungiyar Masu Manja ta Jihar Kuros Riba, Alhaji Ɗanlami Saleh Rishi, ya ce tunda yake bai taɓa ganin yadda aka samu ƙaruwar masu karɓar haraji da jangali ba sai a wannan karo.
Ya ce, “Ka ga tun daga Ogoja idan ka shigo Jihar Kuros Riba zuwa Ugep a Ƙaramar Hukumar Yakur shingayen duba ababen hawa da masu karɓar kudin rshiga sun ƙara yawaita.
“Idan suka tare direba a wannan shinge sai su ce kudin na shugaban ƙaramar hukuma ne, domin ƙaramar hukuma na da nata shingen kuma gwamnatin jiha ma da nata.
“Haka yara ɓata-gari sukan iya rufe hanya haka kawai su fadi abin da direba zai ba su, kuma dole sai ya bayar kafin su bari ya wuce.”
Ya ce wata babbar matsala ita ce muddin direba ya ƙi ya biya cewa suke a faka mota gefen hanya, inda wasu daga cikin yaran suke farke tamfal din mota sun saci kaya kai direba ba ka sani ba, sai ka je sauke kaya a ga ba su cika ba.
Alhaji Saleh Rishi ya nuna wa Aminiya wasu rasitai iri iri na masu karɓar kudin rabano na ƙarya da na gaskiya.
Sai dai binciken da aka gudanar ya nuna yara ne kurum zauna gari banza da ake zargi ’yan siyasa ne suka rufa musu baya, suke aikata hakan.
Duk ƙoƙarin da wakilinmu ya yi domin jin ta bakin hukumomin da abin ya shafa a jihar ya ci tura.