’Yan Arewa mazauna Legas sun yi na’am da sabon Gwamna
Al’ummar Arewa mazauna Legas sun bayyana farin cikinsu da nasarar da dan takarar Gwamnan Legas na Jam’iyar APC Babajide Sanwo-Olu ya yi, inda ya lashe zaben Gwamna da ya gudana a ranar Asabar da ta gabata da ratar kuri’u sama da dubu 500 a tsakaninsa da mai biye masa na Jam’iyyar PDP, Jimi Agbaje. Jaridar […]
Al’ummar Arewa mazauna Legas sun bayyana farin cikinsu da nasarar da dan takarar Gwamnan Legas na Jam’iyar APC Babajide Sanwo-Olu ya yi, inda ya lashe zaben Gwamna da ya gudana a ranar Asabar da ta gabata da ratar kuri’u sama da dubu 500 a tsakaninsa da mai biye masa na Jam’iyyar PDP, Jimi Agbaje.
Jaridar Aminiya ta ji ta bakin wadansu daga cikin ’yan Arewa mazauna Legas, inda suka nuna farin cikinsu da sakamakon zaben, suka ce su a koyaushe suna tare da jam’iyya mai mulki ne a jihar kuma irin wannan salon siyasa Sardaunan Sakkwato Sa Ahmadu Bello ne ya koya musu.
A cewar Alhaji Sule Ahmad Gogori Sarkin Samarin Seme Boda, ’yan Arewa mazauna kan iyakar Najeriya da kasar Benin sun yi farin ciki da sakamakon zaben Jihar Legas. Ya ce ce sai dai hukumar zabe ta hargitsa sunayen ’yan Arewa wadanda ya kamata su yi zabensu a Unguwar Hausawa ta Zango da ke Seme Boda.
“Sai aka tura sunayen mafi yawan jama’armu can wasu yankunan na daban amma hakan bai sanya mun yi kasa a gwiwa ba, domin mun ajiye ababen hawa muka bai wa jama’armu hakuri cewa su daure su je su kada kuri’arsu, domin muhinmmancin zaben Gwamna gare mu. Wannan shi ne dalilin fitar jama’armu da dama wajen kada kuri’a amma a gaskiya an fi fita a lokacin zaben Shugaba Buhari. Fatanmu shi ne wannan sabon Gwamna ya tuna da mu domin akwai bukatar a dama da mu ’yan Arewa a wannan karon,” inji shi.
Hakazalika, a’lummar Kasuwar ’Yan Gwangwan da ke yankin Ojota a Gidan Kwali a Legas sun bayyana farin cikinsu da sakamakon zaben Gwamnan Legas, inda suka ce tunda sanyin safiyar ranar Asabar suka fita rumfunan zabensu da ke yankin, amma jami’an zaben ba su iso yankin nasu ba sai da misalin karfe daya da rabi na rana.
Alhaji Ibrahim Soja Sarkin ’Yan Gwangwan shi ne jagoransu, kuma ya shaida wa Aminiya cewa sun yi aikin wayar wa jama’arsu kai domin su fito su kada kuri’arsu a lokacin zaben Gwamna da na ’yan majalisar jiha. “Wannan ne ya sanya jama’armu suka amsa kira sai dai an samu tsaiko domin mun dauka ba za a ba mu damar zabe ba a wannan karo, domin jami’an zaben ba su zo wajenmu ba sai bayan Sallar Azahar, sun kuma alakanta rashin zuwansu da wuri da karancin kayayyakin ayyukan zaben, wadansu ko na ganin rashin biyan hakkokin ma’aikatan zaben na wucin gadi ne ya janyo jinkirin, wadanda suka yi bore kafin su fara gudanar da aikin zaben. Amma duk da haka mun yi hakuri mun fita kwanmu da kwarkwata, mun zabi abin da ranmu ke so bayan da jami’an zaben suka zo bayan mun yi Sallar Azahar kuma Allah Ya bai wa wanda muka zaba. Fatanmu shi ne ya kyautata al’amuran siyasar jihar nan ta yadda mu ma baki ’yan Arewa za mu amfana,” inji shi.
A Kasuwar Alaba Rago, inda a nan ma aka samu dandanzon ’yan Arewa mazauna yankin da suka fita suka yi zaben, Shugaban Kasuwar Alhaji Malami ya shaida wa Aminiya cewa duk da a wannan lokacin zaben suna cikin alhinin kamen ’yan kasuwarsu, su kimanin 30, wadanda ke hannun hukuma; bayan rigingimun murnar zaben da ya lakume ran mutum uku a yankin. Ya ce ba a Kasuwar Alaba Rago wannan rikicin ya samo asali ba, hasali ma da yawa daga cikin wadanda suka shirya abin ba ’yan Alaba Rago ba ne.
“Duk da wannan yanayi da muke ciki, mun fito mun yi zabe Allah Ya kuma bai wa wanda muka zaba. Don haka muna murna domin wannan gwamnati na da kyakkyawan tsarin gyara a kasuwar, kuma muna kokarin ganin an sako ’yan kasuwarmu da aka kame a lokacin wancan hatsaniyar da ta biyo bayan murnar zaben Shugaban Kasa,” inji shi.
Alhaji Muhammad Musa Maitakobi Shugaban Kungiyoyi Masu Motocin Sufuri na Jihar Legas ya bayyana cewa jama’ar Legas na bukatar abubuwan ci gaba da ake yi a Legas, a ci gaba da yin su don haka suka zabi dan takarar APC Babajide Sanwo-Olu.
“Ba don haka ba abin da ya faru a Jihar Kwara ne zai faru a Legas, don haka goyon bayan jama’a shi ya bai wa wannan sabon Gwamna dama, na kuma yi farin ciki da wannan yanayi na siyasar Legas, wanda ya isa ya zama aya ga jama’ar kasar nan, domin Gwamna mai ci an yi takara da shi ya fadi amma ya hakura da dadi ba dadi har ya tabbatar da Jam’iyyar APC ta ci zabe. Domin mazabarsa ma jam’iyyar ce ta yi nasara, ka ga wannan ya nuna ya hakura, ya rungumi kaddara cewa shi mulki na Allah ne. Wannan abu ne na koyi da ya kamata sauran jihohin kasar nan su yi koyi da Legas,” inji shi.
Zaben wanda Mista Babajide Sanwo-Olu ya lashe, ya gudana lafiya, sai dai an samu karancin masu kada kuri’a idan aka kwatanta shi da zaben Shugaban Kasa.