’Yan Arewa mu hankalta

Mutanen mu a Arewa a kullum idan ana magana kan raba Najeriya tsakanin Kudanci da Arewacinta, sai ka ji suna cewa “Ku bar su a rabu, ai idan an rabu (kudanci) za su sha wahala, saboda Yarabawa da Ibo basa ga maciji da juna, rikici ne zai kaure a tsakaninsu kamar yadda ya faru a […]

’Yan Arewa mu hankalta

Mutanen mu a Arewa a kullum idan ana magana kan raba Najeriya tsakanin Kudanci da Arewacinta, sai ka ji suna cewa “Ku bar su a rabu, ai idan an rabu (kudanci) za su sha wahala, saboda Yarabawa da Ibo basa ga maciji da juna, rikici ne zai kaure a tsakaninsu kamar yadda ya faru a Sudan ta kudu bayan ta fice daga Sudan.”

Mai yiwuwa wannan hasashe ya iya zama gaskiya, to amma ita Arewar fa? Wai a tunanin mu Arewar na iya zama a turbar son juna, kaunar juna, ’yan-uwantaka, dattaku da sanin yakamata a irin halin na-ciki-na-cikin da muke rayuwa, inda ake kallon-kallo ga juna?

Duk da yake cewa munfi ’yan kudanci rashin nuna bambance-bamcance a tsakanin juna, amma yana da kyau mu duba wasu bangarorin domin gyara, musamman batun da ya jibanci siyasa.

Alal misali mu duba cece-kuce da tatabarzar da take faruwa kwana biyun-nan tsakanin ’yan jihar Bauchi da Kano, bayan da Gwamnan Jihar Bauchi ya bai wa wani dan Jihar Kano mukamin mai magana da yawunsa. Na ga kalamai marasa dadi daga wasu ’yan Bauchi na nuna rashin amincewarsu da matakin saboda ba a bai wa dan jiharsu ba, shin a haka za mu cigaba da tafiya da sunan hadin kai? Hatta a tsakaninmu muna hassada ga juna a kan matsayin da bai taka kara ya karya ba?

Ka da mu yadda wannan abu ya ci gaba da faruwa idan ba so muke a kasa bambancemu da wadanda muke cewa kansu a rabe yake ba. Misali na biyu da zan baku shi ne, lokacin da ake rikicin Shugabancin jam’iyar PDP tsakanin Ali Modu Sherrif da Ahmed Makarfi, a bayyana.

Take cewa kowa na samun goyon baya ne na mafi akasarin mutane da gwamnonin da ke yankinsa a fahimta ta.

Inda ’yan yammacin Arewa ke rufa wa Makarfi baya, yayin da a bangarensu ’yan gabashin Arewa ke cewa Sheriff ba ja da baya. Shin wannan shi ne hadin kan Arewar? Wallahi ya zama wajibi mu kyautata ’yan-uwanta ka a tsakaninmu domin tsira daga barazanar rabuwar kai da ’yan-uwantaka gami da dogon zumuncin al’adda da addinin da ke tsakaninmu, mu yi siyasa ta cigaba mai tsafta a garemu.

 

Comr Usman Bin-affan Damaturu. Jakadan Matasa! 08038001563 Uthman Ibn Affan Muhammad Ibn Adam <[email protected]