’Yan Arewa mu kiyayi tashin hankalin bayan zabe
Daukacin ‘yan Nijeria da ma duniya baki daya hankali ya koma kan manyan zabukan kasa da za a gudanar a shekarar 2015 a wannan kasa. Wata babbar barazana da ke daukar hankula ita ce yadda alamu suka bayyana na irin siyasar nan ta ko a mutu, ko ayi rai, musamman idan aka yi la’akari da […]
Daukacin ‘yan Nijeria da ma duniya baki daya hankali ya koma kan manyan zabukan kasa da za a gudanar a shekarar 2015 a wannan kasa. Wata babbar barazana da ke daukar hankula ita ce yadda alamu suka bayyana na irin siyasar nan ta ko a mutu, ko ayi rai, musamman idan aka yi la’akari da irin kalaman da suke fitowa daga bakunan wasu manyan ’yan siyasar kasar nan. Sanin kowa ne cewar tashin –tashinar zabe kan faru ne sakamakon zafafan kalamai da ingiza mai kantu ruwa daga wadanda ya kamata su yi wa bakunansu linzami a lokacin da ake bukatar tunda ’yan magana kan ce ‘idan rai ya baci bai kamata hankali ya gushe ba.’
A bayyane take cewar tarihin rikice-rikicen siyasar wannan kasa na baya-bayan nan sun fi yin tasiri ne a Arewacin Najeriya. Saboda haka mutanen wanna yanki sun fi kowa damuwa da abin da ka iya biyo bayan wadanan zabubbuka na 2015. A sakamakon wannan tsoro ne ma wasu muhimman ’yan Najeriya ke kira da babbar murya wajen jawo hankulan mutane kan a guji dukkan wani abu da zai iya kawo tashin hankali a tsakanin al’umma, kuma ya kara jefa wannan yanki cikin rudani, musamman idan aka yi la’akari da irin halin da yankin yake ciki sakamakon matsalar rashin tsaro da ake fama da shi. Daga cikin wadanda suka yi kira, sun hada da tsohon Jakadan Najeria a kasar Biritaniya, Farfesa Bolaji Akinyemi, wanda ya yi kira ga manyan ’yan takarar shugban kasa na jam’iyyar PDP, Shugaba Goodluck Jonathan da kuma na APC, wanda tsohon shugaban mulkin soja ne, Janar Muhammadu Buhari da cewar su rubuta takardar tabbacin zaman lafiya bayan zaben 2015. Shi ma shahararren Malamin addinin Musuluncin nan da ke Kaduna, wato Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ya ja hankulan jama’a da cewar babu wanda ya cancanci a salwantar da rai saboda shi tsakanin Jonathan da Buhari.
Hakika wadannan shugabanni sun cika ’yan kishin kasa domin kuwa duk wani mai yunkurin tayar da jijiyar wuya ba zai wuce bangaren daya daga cikin wadannan ’yan takara ba. A saboda haka idan aka samu hadin kansu wajen kushewa da nesanta kai daga tashin hankali lallai magoya baya ma za su mayar da wukar.
Tarihi ya nuna cewa, yankin Arewacin ya kasance wata nahiya mai aminci da arziki iri daban-daban, sai dai abin takaici ne a ce yau wannan yanki da aka san shi a matsayin madubin siyasar Najeria da ma Afirka baki daya ya kasance wani dandamalin tashin-tashinar bayan zabe, duba da yadda aka tafka asarar rayuka da ta dukiyoyi a sakamakon rigingimun da suka biyo bayan zaben 2011. Lallai idan muka yi waiwaye za mu ga cewar al’amarin bai haifarwa da wannan yanki da mai ido ba, hasali ma dai ya kara zama wani mummunan koma baya a fannonin rayuwa daban-daban wadanda suka hada tattalin arziki da zamantakewa da sauransu.
Bayanai sun nuna, babbar kanwa uwar gami wajen hura wutar rikici a tsakanin al’umma su ne jagororin siyasa, musamman ’yan takarar in ba mu ba a mutu. Ashe ke nan al’umma ba ta da babban makiyi kamar dan siyasar da yake iza wutar rikici, ko dai ta kalamansa ko ayyukansa ko kuma nuna halin ko in kula a lokacin da ake rura wutar rikici, ba tare da ya tsawatarwa ko ya yi Allah wadai da masu wannan mummunar dabi’a ba, kawai domin wani kato ya kasa samun biyan bukatarsa. Babban abin takaici shi ne yadda wadannan ’yan siyasa kan boye lokacin wadannan rikice-rikice, ba za ka kara jin duriyarsu ba, har sai kura ta lafa bayan talakawa sun jikkata, sai su fito suna ta’aziyyar wadanda suka rasa rayukan su da jajen dukiyar da aka rasa. Inama dai ‘yan uwana talakawa za su dinga matsawa cewar irin wadannnan masu zuga su su ma su fito da matansu da ‘yayansu domin jagorantar kowane irin bore, ka ga idan har suka ki fitowa to mu sani cewar ba su da gaskiya kuma makiyan al’umma ne, amma idan suka fito sai a saka su a gaba duk inda za’a je suyi jagoranci.
Idan muka yi waiwaye dangane da irn rigingimun da suka biyo bayan zaben 2011, za mu ga cewar har a wasu watanni nan baya kadan akwai ragowar mutanen da ba su koma gidajensu ba, musamman a Jihar Kaduna sakamakon rasa matsugunansu da suka yi, inda suka samu mafaka a sansanin alhazai da ke Mando, kuma suka shafe kusan shekaru uku a cikin wannan yanayi. Wasu kuma sun rasa iyayensu da ‘yan uwansu bayan asarar dukiyoyi masu tarin yawa. A bangare guda kuma, su wadanda aka yi rikicin domin su tuni suka ci gaba da more rayuwarsu a yayin da wasu suka kasance cikin bakin ciki da asara iri daban-daban. Kuma akasarin wadanda suka shiga yanayin kuncin rayuwa sun kasance masu karamin karfi.
A nan ya zama wajibi mutanen Arewa mu shiga taitayin mu, bisa la’akari da irin guguwar rikicin da take neman baibaye kakar zaben shekarar 2015. Wannan jan hankali ya zama dole, musamman ga matasan mu wadanda sukan zamo abin amfanin ’yan siyasa ta hanyar ba su kayan maye alhalin ‘yayansu na kasashen waje suna karatu da nufin kyakyawara rayuwa, a waje guda kuma ‘ya’yan talakawa ko oho. A zuga su, su hallaka ‘yan uwansu, su barnata dukiyoin jama’a kuma wadansunsu su kare a kurku ko ma su rasa rayukansu a hanyar da ba ta dace ba.
Bisaa wannan babban kalubale, tabbatar da zaman lafiyar yankin Arewa ya rataya ne a wuyan shugabannin al’umma da suka hada da na siyasa da addini da masu sarautun gargajiya da ’yan kasuwa da shugabannin jama’a masu fada aji da mata da matasa da sauransu. Wajibi ne mu bai wa mara da kunya ta wajen jan hankulan al’umma akan irin fitinar da ke tattare da tashin hankali, musamman in an yi la’akari irin halin rashin tsaron da muke fama da shi.
Muhamma Auwal, Hotoro kuaters, Kano