’Yan Arewa ne ke riƙe da muƙaman sha’anin tsaro — Fadar Shugaban Ƙasa

Hadimin ya ce sam raɗe-raɗin ba su da tushe.

’Yan Arewa ne ke riƙe da muƙaman sha’anin tsaro — Fadar Shugaban Ƙasa

Fadar Shugaban Ƙasa, ta musanta raɗe-raɗin cewar Shugaba Tinubu na fifita yankin Kudu Maso Yamma a kan sauran yankuna wajen rabon muƙaman da suka shafi sha’anin tsaro.

Wannan na zuwa ne, biyo bayan naɗa Manjo Janar Olufemi Oluyede, a matsayin Muƙaddashin Babban Hafsan Sojojin Ƙasan Najeriya, inda a kafafen sada zumunta aka zargi Tinubu da fifita ƙabilar Yarbawa.

An naɗa Oluyede ne, don ya maye gurbin Janar Tahoreed Lagbaja, Babban Hafsan Sojojin Kasa, wanda ya fita ƙasar waje domin neman lafiya.

Wasu ’yan Najeriya sun nuna cewar akwai manyan janar-janar masu ƙwarewa da za a iya bai wa wannan muƙami maimakon ɗauko wani daga yankin Kudu Maso Yamma.

Sai dai Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Harkokin Yaɗa Labarai, Sunday Dare, ya musanta raɗe-raɗin ta hanyar wallafa jerin sunayen shugabannin hukumomin tsaro da Tinubu ya naɗa.

Dare ya wallafa jerin yadda rabon muƙaman ya kasance

A cewarsa, ’yan Arewa Maso Yamma sun fi kowa samun gurbi a hukumomin tsaro (takwas), sai Kudu Maso Yamma (biyar), sannan Arewa Ta Tsakiya (huɗu).

Arewa Maso Gabas tana da mutum uku, yayin da Kudu Maso Kudu da Kudu Maso Gabas kowane ke da mutum ɗaya.

“Ba a ɓoye gaskiya. Ga gaskiyar abubuwan da ke nuna yadda Shugaba Tinubu ya naɗa shugabanni a hukumomin tsaro guda 20.

“Zargin cewa yana fifita Yarbawa a ɓangaren tsaro ba gaskiya ba ne. Muna tare da kai!” in ji Dare.