’Yan Arewa ne tushen matsalar Arewacin Najeriya

Jama’a kar ku ga laifin Shugaba Johnathan bisa abubuwan da ke faruwa a yankin Arewacin kasa ko kasar baki daya. Yayin da idan kuka duba da kyau, za ku fahimci mukarrabai ke tafiyar da gwamnatin nan, wadanda da dama daga cikinsu ’yan Arewa ne! Balle kowa ya san Shugaba Jonathan ba ya da horon mulki, […]

’Yan Arewa ne tushen matsalar Arewacin Najeriya
’Yan Arewa ne tushen matsalar Arewacin Najeriya

Jama’a kar ku ga laifin Shugaba Johnathan bisa abubuwan da ke faruwa a yankin Arewacin kasa ko kasar baki daya. Yayin da idan kuka duba da kyau, za ku fahimci mukarrabai ke tafiyar da gwamnatin nan, wadanda da dama daga cikinsu ’yan Arewa ne! Balle kowa ya san Shugaba Jonathan ba ya da horon mulki, sa’a ta kai shi kujerar.
Da Arewa ke sama, Arewa ce kan gaba a komai, sai aka ce a zama daya, a raba! Yanzu su ne sama ta fuskokin kasuwanci, ilimi siyasa da shugabanci. Sun fi mu yawan makarantu, malamai, kai ko jami’o’i ne da yawan farfesoshi karara a jiha daya za ka sami wadanda idan ka hada Arewa ba su kai na jihar yawa ba. Sannan sun fi yawan likitoci, lauyoyi, injiniyoyi da ayyukan da suke bukatar kwararru.
’Yan Arewan su suka zabo Jonathan, koda ba kai tsaye ba, wa ya zabo Obasanjo? Wa ya dora Umaru? Kuma wa ya gaji Umaru? Bugu da kari da ’yan Arewa ake cin zabe a kasar nan kuma duk wanda yake bibiyar tarihi zai fahimci ’yan Arewa suka gina Kudu. Ko a kwanan nan wa ya tabbatar da zaman lafiya a Neja-Delta kuma wa ya tsokano ’yan Borno?
Tabbas manyan mutanen Arewa su ne matsalolin Arewa kuma makiyan yankin, domin da sun so da yankin ya ci gaba, ya bunkasa, ko a yau ba a yi jinkiri ba. Amma zuciyarsu ta mutu ko kudi ba su iya zubawa don yankin ya farfado. Har wa yau yana da wuya dan Arewa ya iya bambace tsakanin masu kudi da masu kishin Arewa!
Ga damar gina Arewa a bisa turbar masana’antu da habaka harkar noma da kiwo amma an yi watsi da wannan, ana koma kacokam sai abin da aka turo daga ribar man fetur. Da suka zama shugabanni, gwamnoni, Sufeto-Janar da kwamishinoni, mutane nawa suka dauka aiki? Ko har yanzu da suke da damar karfafa wa matasan, me suka yi? Sai iskar siyasa ta kada ka ji suna fitowa, suna magana madadin mutanen Arewa.
Abin takaici, a rayuwar wasu da suke kiran kansu da manyan Arewa ko dattijan Arewa ake kashe-kashe a Arewacin kasar nan, ba rana ba dare, gara ku yi fatan irin wannan bakin cikin bai afku ba a rayuwarku, wai Bafulatani ba ya iya kiwo a Arewa, idan ya je Kudu kuma daya yake da dabbobin da ake farauta.
Duk wanda ya sami damar wakilci, maimakon ya auna bukatun ’yan uwansa, makwabtansa sai ya mayar da komai abin da ya shafe shi kai tsaye shi ke nan! Idan aka ba da kudi su raba mana sai mutum daya ya cinye kuma a kasa yin komai! A haka yankin Arewa ya fi yawan jahilai da kauyawa.
Ko ’yan majalisar da ake tura da sanatoci ba su iya cewa komai a majalisar, sai ’yan Kudu suke kawo kudurori gwargwadon bukatunsu. A siysance sai cika baki, ba aiki. Shi ya sa sai ka iske har yanzu ana tura mutane daga nan yankin Majalisar Tarayya bayan ko Turancin ba su iya ba. A haka sai su zama ’yan kallo a majalisar! Ko a taron kasar da ake gudanarwa kuri’ar ’yan Arewa ba ta da karfi, don an fi su yawa!
Dadin dadawa ’yan Arewa ba a shirye suke ba, kusan ma ba su dauka suna da matsaloli ba, su dai a sallame su, su saurara!
Kar mu yaudari kanmu, ba Jonathan ya kawo almjirai ba, ta wata fuskar Gwamnatin Jonathan ta yi kokarin kawo karshen bara da mabarata. Wai me gwamnanku da gwamnonin da suka wuce suka yi wajen samo wa matasa ayyukan yi. Me attajiran garinku suka yi wajen ciyarwa duk da dimbin ladar da ke ciki?
Za ku iske kusan duk gwamnonin ’ya’yan talakawa ne amma da zarar sun sami damar hawa kan karagar mulki sai su zama su ne attajiran jihohinsu. Amma bakin ciki da kyashi ya yi yawa, musamman a nan Arewa bayan su ’yan Kudu ba haka suke yi ba. Idan ma ba za mu yi koyi da komai ba a Gwamnatin Jonathan, mu yi ko yi da yadda yake kishin addininsa, kabilarsa ko jiharsa!
Sannan manyan malamai suna da dabi’ar raba kan mabiya ta hanyar dariku, Izala, Shi’a, ba a magana da murya daya, bayan an lura ba ruwan makami da inda ka fito. Tasirin mukarrabai ya sa Johnathan na rabewa a kan wasu muhimman bayanai dangane da tsaron kasa, daukar ma’aikata, cin hanci da rashawa, kare gwamnatin tare hanyoyin tafiyar da kasafin kasa.
Har yanzu akwai damar farfado da Arewa daga halin da ta tsinci kanta, musamman idan aka yi la’akari da cewa yanzu lokaci ne na hadin kai, sai a kai labari, kar ku zama ’yan gulma, sai kun yi tsegumi za a yi maku hasafi. Tabbas samun shugaba mai gaskiya da mabiya masu da’a, sa’a ce a Najeriya.

Daure, mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, za a iya tuntubarsa ta +2347305986444

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno