“ ’Yan Arewa za su ci gaba da zama bayi idan suka dogara da mai”

dan rajin kare ’yancin dan Adam din nan Kwamared Shehu Sani ya ce talakawan za su ci gaba da zama cikin “kuncin bauta” matukar ba su kaurace wa siyasar kudi suka zabi shugabannin da suka dace ba.  Ya ce Arewa za ta fuskanci bala’i idan ta ci gaba da dogaro da “kudin man fetur na […]

“ ’Yan Arewa za su ci gaba da zama bayi idan suka dogara da mai”
“ ’Yan Arewa za su ci gaba da zama bayi idan suka dogara da mai”

dan rajin kare ’yancin dan Adam din nan Kwamared Shehu Sani ya ce talakawan za su ci gaba da zama cikin “kuncin bauta” matukar ba su kaurace wa siyasar kudi suka zabi shugabannin da suka dace ba. 

Ya ce Arewa za ta fuskanci bala’i idan ta ci gaba da dogaro da “kudin man fetur na yankin Neja-Delta da ake rabawa wata-wata da sunan Kason tarayya ga jihohi.”
Kwamared Shehu Sani, wanda yake neman tsayawa takarar Sanatan Kaduna ta Tsakiya a karkashin Jam’iyyar APC, ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi ga ’yan fansho da ma’aikatan Hukumar Jiragen kasa a hedkwatar Hukumar Jiragen kasa da ke Kaduna.
Ya ce, “Jihohin Arewa ba za su kai gaci ba idan suka ci gaba da dogaro da kudin man fetur da ke yankin Neja-Delta. Jihohinmu sun gaza fito da dabarun yadda za su rika samar da kudaden da za su tafiyar da harkokinmu. Babu wata jiha a Arewa da za ta iya biyan albashin wata daya ba tare da kason tarayya ba, kuma kason tarayya yana fitowa ne daga kudin man fetur da ake samu a yankin Neja-Delta. Wannan hadari ne kuma yana iya haifar da bala’i a nan gaba. Shin zai yiwu mutum ya rika ciyar da kai ba tare da ya rika juya k aba? Shugabanninmu masu hangen nesa irin su marigayi Sa Ahmadu Bello sun hango wannan hadari, amma shugabanninmu na baya sun kauce wa abin da zai zame alheri. Idan Najeriya ta dare a yau, Arewa za ta shiga hadari.”
Kwamared Shehu Sani ya ci gaba da cewa, “Wajibi ne mu guje wa siyasar kudi mu rika zabar shugabannin da suka dace. Wajibi ne mu kare kuri’unmu. Mu ne kan gaba a yawan jama’a. Muna da sanatoci da gwamnonin da shugabannin kananan hukumomi da kansilolin da suka fi yawa, amma duk da haka mu ne muka fi yawan mabarata da wadanda ake zalunta.”
Jagoran ’yan fanshon Mohammed Aliyu ya ce ana biyansu fansho din Naira dubu biyar ne kowannensu. Kuma ya yi alakarin za su yo aiki domin yakar siyasar kudi. An kammala taron da yi addu’ar zaman lafiya da hadin kan kasa.