‘Yan Arewa za su samu albarka a Kasuwar Ogere — Sarkin Ogere

Duk dan Arewa mazaunin Kudu, ko mai zuwa ya yi kasuwanci ya koma, dole ya yaba wa gwamnatin Ogun.

‘Yan Arewa za su samu albarka a Kasuwar Ogere — Sarkin Ogere

A ranar Alhamis din makon jiya ne ’yan Arewa masu harka a kasuwar dabobbi da mayanka da gwamnatin Jihar Ogun ta gina a garin Ogere suka kai ziyarar girmamawa ga Sarkin garin, Ologere na Ogere, Oba Obafemi James Saliu.

Sarkin ya karbi bakuncinsu tare da shugabannin Kungiyar Ci-gaban Ogere da wakilan Shugaban Karamar Hukumar Remo inda kasuwar take.

’Yan Arewar da suka kai ziyarar sun hada da wakilin Sarkin Hausawan Ogere Alhaji Abdullahi Saminaka da Sarkin Fulanin Kasuwar Ogere Alhaji Muhammadu Bammi da daya daga cikin shugabannin kasuwar Mahmoud Zamfara da wakilin ’yan kasuwar kara ta Isheri da ta Abbatuwa ta Legas da sauransu.

Ziyarar na zuwa ne a yayin da Babbar Kasuwar Ogere ke dab da fara kankama bayan umarnin Gwamnatin Jihar Ogun na maido da kasuwar shanu ta Isheri da ke iyakar jihar da Legas zuwa cikin kasuwa da mayankar dabobbin ta Ogere.

A lokacin ziyarar, Oba James Obafeme Saliu, ya ce a daukacin Kudancin Nijeriya, garin Ogere na sahun gaba wajen maraba da ’yan kasuwar Arewa da sauran masu sana’o’i da leburori.

Ya ce haka ne ya sa duk wanda ya zo Kudu daga Arewa garin Ogere ne masaukinsa, kuma hakan ya sa garin ya yi suna.

Sarkin ya ce Kasuwar Ogere matattara ce ta albarka da gwamnati ta gina, don haka ya yi kira ga ’yan kasuwar Arewa su zo kasuwar don su amfana, kuma su tabbatar an samu zaman lafiya da kwanciyar hankali don hakan ne zai kawo ci gaba.

Sarkin ya gina rijiyar burtsatse, da sanya fitulun lantarki masu amfani da hasken rana da wajen zaman jami’an tsaro a kasuwar, ya bai wa ’yan Arewa tabbacin ci gaba da raya kasuwar ta hanyar zuba jari da samar da abubuwan more rayuwa.

Ya ce abin da yake bukata daga gare su shi ne su hada kai, su zauna lafiya a tsakaninsu da mutanen garin da kasuwar ke ciki.

Shugaban Karamar Hukumar Ikenne a Jihar Ogun wanda ya samu wakilcin jami’in mai sanya ido a yankin, Mista Amusu Ademola Kazeem, bayan kammala taron, ya shaida wa Aminiya cewa, akwai bukatar tsaro domin samun ci gaba, don haka mahukuntan yankin ke bai wa tsaro muhimmanci a daidai lokacin da kasuwar ke fararbukasa.

Ya ce suna yaba wa Gwamnan Jihar Ogun, Mista Dapo Abiodun a kokrinsa na habaka kasuwanci a jihar.

Ya ce “Dawo da Karar Isheri da Gwamnan ya yi zuwa garin Ogere wani yunkuri ne da zai bunkasa kasuwanci a daukacin jihar.”

Ya ce dama garin Ogere ya saba da karbar baki da zaman lafiya, wannan ya sa a tsawon shekaru ya shahara a fuskar ci gaba.

Shugaban ya ce kofar kasuwar a bude take ga kowa, duk mai neman arziki ya shigo, ya kawo hajarsa don ya amfana.

Otunba Lekon wanda ya wakilci Kungiyar Ci-gaban garin Ogere Remo ya shaida wa Aminiya cewa, babbar kasuwar dabobbin da gwamnatin jihar ta gina a daidai wannan lokaci gwamnatin jihar ta yi yunkurin bunkasata ta hanyar dawo da wasu kasuwannin da ke ci a jihar cikinta.

Ya ce sun dade da samun labarin cewa garin zai bunkasa ya yi fice ta hanyar kasuwanci, don haka suna yi wa Gwamna Dapo Abiodun godiya kan kokarinsa na tabbatar da haka.

Sarkin Fulani Kasuwar Dabobbi ta Ogere, Alhaji Bammi Ogere, ya shaida wa Aminiya cewa suna maraba da bakin ’yan kasuwa su zo kowa ya amfana.

“Kasuwa tana maraba da kowa, muddin za a zo a yi ladabi da biyayya, a bi ka’ida.

“Sarki shi ne uban kasuwa, zaman lafiya da bin doka da oda ne mafi a’ala, mun dade muna jiran wannan lokaci, muna jira ga jama’a baki daya, babu bambanci kowa ya zo ya amfana,” in ji shi.

Kwamared Mahmuda Alhassan Zamfara daya daga cikin shugabannin kasuwar, ya shaida wa Aminiya cewa sun shirya zama da ’yan kasuwan jihohin Legas da Ogun da dama, inda da dama suka nuna sha’awarsu ta zuwa kasuwar kasancewarta mai girma da gwamnati ta gina, inda kowa ke da kwanciyar hankali don gudanar da kasuwancinsa.

“Zuwan kasuwar a wannan lokaci zai taimaka wa ’yan kasuwarmu na Arewa da ke fuskantar matsalolin wuraren zama, in ka lura Jihar Legas ta cika, kamfanoni ma dawowa Ogun suke yi, don haka wannan dama ce da za mu zo mu gina wannan waje don amfaninmu da wadanda za su zo bayanmu.

“Duk dan Arewa mazaunin Kudu, ko mai zuwa ya yi kasuwanci ya koma, dole ya yaba wa gwamnatin Jihar Ogun, kuma ya gode wa Gwamnan Jihar Dapo Abiodun, domin ya aza harsashin share mana haayenmu,” in ji shi.

Kasuwar Dabobbi ta Ogere, a garin Okere, na kan babbar hanyar Legas daga Ibadan, kuma tana da mayanka ta zamani, da sashen sayar da shanu da kananan dabobbi da bangaren zaman fatake da gidajen ’yan kasuwa, kuma tuni ’yan kasuwa ’yan Arewa da ke kasuwanci a garuruwan Legas da Ogun suka fara zuwa don samun gurbin kasuwanci a kasuwar.

’Yan sanda sun ƙwace sakamakon zaɓe a Ribas

Yadda mutanen Jigawa suka ƙi fita zaɓen ƙananan hukumomi 

Za mu yi wa Kwankwaso ritaya a 2027 — Doguwa

’Yan daba sun ƙone ofishin hukumar zaɓen Akwa Ibom