’Yan Asalin Abuja na kalubalantar tsarin Abuja Land Swap

Shirin Land Swap wanda ma’aikatar kula da birnin tarayya ta kirkiro , inda za’a bada daukacin gunduma ga kamfanonin da ke gina mahalli da sayarwa, a maimakon tsarin bada fegi/fuloti, da a ke bi a baya, na fuskantar gagarumar tirjiya daga ’yan asalin yankin Abuja, wadanda ke zargin ma’aikatar da shirin saida daukacin filayensu ba […]

’Yan Asalin Abuja na kalubalantar tsarin Abuja Land Swap

Sanata Bala Mohammed Ministan Babban Birnin Tarayya, AbujaShirin Land Swap wanda ma’aikatar kula da birnin tarayya ta kirkiro , inda za’a bada daukacin gunduma ga kamfanonin da ke gina mahalli da sayarwa, a maimakon tsarin bada fegi/fuloti, da a ke bi a baya, na fuskantar gagarumar tirjiya daga ’yan asalin yankin Abuja, wadanda ke zargin ma’aikatar da shirin saida daukacin filayensu ba tare da sun ba su diyya ko tsugunar da su a wani waje ba. ’yan asalin Abujan, karkashin inuwar kungiyarsu mai su na “Original Inhabitant Debeloptment Association” (OIDA) ta gudanar da gangamin Allah wadai da tsarin a lokuta da dama, na baya-bayan nan shi ne wanda ta yi a majalisar kasa, inda a yayin zanga zangar jami’an tsaro suka tarwatsasu bayan jefa mu su barkonon tsohuwa.
Aminiya ta nemi sanin yadda tsarin na Land Swap ya ke, inda babban jami’i da ke kula da cibiyar zuba jari a bangaren ababan raya waje, wato “Abuja Infrastructure Inbestment Centre” Umar Faruk Sani ya bayyana dalilin kirkiro da tsarin na Land Swap da ma cibiyar gaba daya. Ya ce “ kamar yadda yawanci a ka sani, birnin tarayya ya kasu kashi biyu ne, a kwai bangare da a ke kira Federal Captal City F.C.C (kwaryar birni) wanda ke da gundumomi sama da 70 a waje mai girman skuare kilo meter 250, da ya kunshi sassa 4, (phase 1,2,3,4).
 “sai kuma bangaren kewayansa da a ke kira “Federal Capital Territory” F.C.T,  mai  girman skuare kilo meter 7,700.  “a tsarin da wadanda suka kirkiri birnin suka bayar, shi ne, daukacin gundumomin yankin na kwaryar birni da kewaye shi ne a samar ma su da ababan raya waje cikin shekara 25 (daga 1980 lokacin da a ka fara aikin birnin).
“wadannan ababan sun hada da tituna, da magudanan ruwa, da na bahaya, da ruwan famfo, da wutar lantarki, da layukan sadarwa, da Asibitoci, da Kasuwanni da dai sauransu, sai dai a sakamakon karancin kudi, har zancen nan da mu ke yi a yanzu, ayyukan da a ka yi ba su wuce kashi 25 cikin 100 ba. wannan shi ya sa Ministan Abuja Dakta Bala Muhammad ya ga ba makawa, sai an hada hannu da ’yan kasuwa masu sha’awar zuba jari don bude sababbin gundumomi da ma raya gundumomin da jama’a suka gina mahalli, amma babu ababen raya kasa, ya sa ba a iya zama a cikinsu.
Faruk Sani ya ce, hakan na kara jawo cunkushewar cikinh birnin da ma garuruwan da ke kewayensa, alhali ga filaye da dama wadanda idan a ka bunkasa su za a samu karin  saukin farashin muhalli a birnin tarayyar da kuma saukin zirga zirga. Ya ce sabon shirin Land Swap, wato ba ni gishiri-in ba ka manda, hadin gwiwa ce a tsakanin gwamnatin birnin da kuma manyan ’yan Kasuwa masu zuba hannun jari, inda za a bada gunduma guda mai girman hekta 300 zuwa 500 ga kamfanoni biyu, don su samar da ababen more rayuwa, hakan inji shi zai ba su damar mallakar kashi 60 ko 80 na wajen na tsawon shekara 100, a yayin da ragowar kuma, hukumar birnin ne za ta ci gaba da mallakarsa.
Tuni dai a ka ware gundumoni 8 daga yankin rukuni na hudu na birnin (Abuja phase 4) don harkar na hadin gwiwa ta Land Swap. Kodinetan na Land Swap ya ce, a cikin daukacin gundumomi sama da 70 da ke cikin birnin, gundumomi 11 ne kawai a ka bunkasa su 100 bisa 100, a yayin da ragowar kuma an taba aikin ne kawai sai kuma tarin wadanda ba a yi musu komai ba. Ya ce tuni kamfanoni da dama su ka nuna sha’awar zuba jari a harkar, wanda ba zai gaza cin Naira biliyan 20 zuwa da biyar ba ga ko wane gunduma.
Ya soki tsarin bada fulotai kusan kyauta da ma’aikatar kula da birninn tarayya ta rika yi ga kamfanonin gina gidaje a baya, in banda dan harajin “royalty” da ta ke amsa, inda Kamfanonin ke gina gidaje, su saida, su bar hukuma da alhakin samar da tarin kayan raya muhalli, wanda ya ce samar da su a halin yanzu ke neman ya buwayi hukumar Abuja. haka nan in ji shi a kwai daidaikun fulotai da a ka yi ta baiwa jama’a, amma sai su saida shi ga wani, sannan su sake neman wani, “wannan ya sa kusan kowane waje da ka gani a gundumomi sama da saba’in dinnan da ke kwaryar birni, mallakin wani ne, ba na hukuma ba.
Sai dai matsalar rashin samar da ababan raya kasa, ba ita ce matsala kadai da hukumar Abuja ke fama da ita ba. Tsarin bunkasa birnin ya bayyana cewa, a daidai lokacin da hukumar ke bunkasa shi, za ta kuma rika samar da sababbin matsugunai ga ’yan asalin yankin, a gundumomi da ke wajen kwariyar birnin, ko kuma biyansu diyya na kudi. Wannan in ji Pastor J.G danladi, shugaban kugiyar ’yan asalin Abuja wato “Original Inhabitants Debelopment Association” (OIDA) shi ne tushen asalin rigimarsu da hukumar, kuma muddin idan ba su dauki mataki a kai ba, suna ji, suna gani, za su rasa muhalli a yankin na su na Abuja.
Ya ce “ tsarin da Gwamnatin Murtala ta rattaba wa hannu bayan kwamitin Agudata bada shawarar yadda sabon birnin tarayya zai kasance ya mika sakamakonsa, shi ne, ’yan asalin yankin wadanda a lokacin ba su wuce mutane  dubu dari uku da hamsin (350, 000) ba, shi ne: za a tsugunar da su a wajen birnin, a gidaje da gwamnati za ta gina, wanda a ka kiyasta zai ci Naira Miliyan dubu 2 da miliyan dari takwas.
“Sai dai bayan rattaba hannun, sai Dimka ya kashe Murtala, da Obasanjo ya hau mulki sai ya yi fatali da tsarin bisa dalilin da ya bayar na kudin ya yi yawa a wancan lokacin, saboda daukacin kasafin kudin kasa na shekara a lokacin bai wuce Naira Miliyan dari hudu ba, Obasanjon ya karfafa cewa a bar  jama’armu su zauna a wuraren da su ke, sai dai zuwan Shugaban kasa Shehu Shagari, sai a ka sake jaddada tsarin na baya, tare da kaddamar da aikin gina wa jama’armu gidaje.
Ya ce sabanin abin da a ka fi sani, kabilun asalin Abuja, wadanda ke karkashin kungiyarsu ta OIDA, ba kabilar  Gbagyi ba ce kawai, akwai wa su karin kabilu takwas da su ka hada da ta: Bari, da Gade, da Gana-gana, da Gwandara, da Basa, da Ibira, da Koro, da kuma Amoma. ya ce ka da gwamnati ta jahilci fahimtar saukin kan jama’arsu, a matsayin wawaye ko wadanda ba su san hakkinsu ba. “gwamnati na da zabin aiwatar da abin da ya dace, ko kuma ta fuskanci turjiya.
Sauran matsalolinsu inji shi, shi ne sauya tsarin Mulkin yankin d aga gudanarwar Minista zuwa tsarin Zababben Magajin Gari, kamar sauran manyan biranen duniya, don mazaunanta su zaba wa kansu wanda suke so da kuma ki, idan bai yin aiki ba. Sai kuma karawa yankin karin kananan hukumomi, da Wakilai a majalisun Dattawa da na Wakilai.